Liverpool ta bai wa Arsenal tazarar maki 16 a teburin Premier

Mohamed Salah

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Mohamed Salah ya ci ƙwallo biyu a bugun fenariti da ta kai Liverpool ta doke Southampton 3-1 ranar Asabar a Premier League a Anfield.

Tun kan hutu Southampton ta zura ƙwallo a raga ta hannun Will Smallbone, haka suka je hutu ana cin Liverpool 1-0.

Bayan da suka sha ruwa suka koma zagaye na biyu ne, Liverpool ta farke ta hannun Darwin Nunez, sannan Salah ya kara biyu a bugun fenariti.

Kenan Liverpool na daf da lashe kofin Premier na kakar nan, ta bai wa Arsenal tazarar maki 11, sannan Southampton ta ci gab da zama ta karshen teburi.

Sai a ranar Lahadi Arsenal za ta je Manchester United, domin buga wasan mako na 28 a Old Trafford.