Man Utd na son Tonali, Chiesa zai bar Liverpool

Sandro Tonali

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Ɗanwasan tsakiya na Newcastle da Italiya Sandro Tonali, mai shekara 25, na kan gaba cikin waɗanda Manchester United ke farauta domin maye gurbin ɗanwasan tsakiya na Brazil Casemiro, mai shekara 33 a wannan bazara. (Telegraph - subscription required)

Liverpool za ta ba ɗanwasan gaba na Italiya Federico Chiesa damar tafiya kuma tana son tsakanin fam miliyan 21.7 zuwa miliyan 26 yayin da Juventus da Napoli da Roma ke buƙatarsa. (Caughtoffside)

Tottenham ba ta buƙatar mallakar ɗanwasan gaba na Faransa Randal Kolo Muani da ta karɓo aro daga Paris St-Germain. (Teamtalk)

Liverpool na shirin sake ɗauko ɗanwasan Ingila Jarell Quansah daga Bayer Leverkusen a baɗi. (Football Insider)

Alex Jimenez na shirin kammala yarjejeniyar shekara biyar zuwa Bournemouth daga AC Milan kan fam miliyan. (Fabrizio Romano)

Manchester City na son ɗauko ɗanwasan tsakiya na Everton da Ingila Kiernan Dewsbury-Hall kan fam miliyan 40. (Fichajes - in Spanish)