Abun da ya kamata ku sani kan yarjejeniyar Isra'ila da Masar wadda ke fuskantar barazana

Daga Attia Nabil

BBC Arabic, Cairo

Wani mutum yana taimakon wata Bafalasdiniya a keken guragu, a kan iyakar Rafah tsakanin Masar da Zirin Gaza, a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin Isra'ila da kungiyar Islama ta Falasdinu Hamas, ranar 1 ga Fabrairu, 2024

Asalin hoton, Reuters

Ministan harkokin wajen ƙasar Masar Sameh Shoukry ya sake jaddada aniyar ƙasarsa kan yarjejeniyar zaman lafiya da ta ƙulla da Isra'ila a shekarar 1979.

Hakan ya biyo bayan rahotannin kafafen yaɗa labaran Isra'ila da na Amurka cewa Masar na barazanar dakatar da yarjejeniyar idan har Isra'ila ta ƙaddamar da farmaki kan birnin Rafah na Falasɗinawa a kudancin Zirin Gaza.

Irin wannan farmakin na iya tura dubban Falasɗinawa tsallakawa kan iyaka zuwa yankin Sinai na Masar, tare da tilasta musu ficewa daga ƙasarsu ta haihuwa.

Mista Shoukry ya nemi yin watsi da waɗannan rahotanni ta hanyar bayyana cewa "duk wani tsokaci da mutane suka yi za a iya karkatar da su".

Sai dai wata majiya mai ƙarfi ta Masar ta shaida wa tashar Al-Qahera (Alkahira) cewa, Masar na bin diddigin halin da ake ciki a Rafah, kuma a shirye take ta tunkari dukkan al'amura, ba tare da yin ƙarin bayani ba.

Mene ne manyan sharuɗɗan yarjejeniyar?

Masar da Isra'ila sun gwabza yaƙi da juna, a shekarar 1973.

Amurka ta shiga tsakani kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ƙasashen biyu a ƙarshen shekarun 1970 wadda ta daidaita dangantaka da taƙaita girke sojoji a ɓangarorin biyu na kan iyaka.

Yarjejeniyar da aka ƙulla a shekarar 1979 ta shata iyakokin ƙasashen biyu tare da raba su zuwa manyan yankuna huɗu.

Yankuna uku suna cikin yankin Sinai na Masar. Na huɗu yana cikin Isra'ila kuma ana kiran sa da 'Zone D' a turance.

...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Masar Anwar Sadat (L) da firaministan Isra'ila Menachem Begin (R) tare da Shugaban Amurka Jimmy Carter a shekarar 1978

Yankin 'Zone D'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yarjejeniyar ta bayar da damar kasancewar wata ƙwarya-ƙwaryar rundunar sojan Isra'ila a yankin da ake kira 'Zone D'.

Ta ƙunshi bataliyoyin sojoji huɗu, masu ƙunshe da jami'an sojoji 4,000 tare da takaita musu yankin da kuma masu sa ido na Majalisar Dinkin Duniya.

A bisa yarjejeniyar, bai kamata sojojin Isra'ila da ke yankin su hada da tankokin yaki ko masu linzami ko masu linzami na kakkabo jiragen sama ba, sai dai makaman da mutum zai iya harbawa shi kaɗai,

Yankin Zone D yana da girman kilomita 2.5 (mil 1.5) a kan iyakar Isra'ila da Masar. Ya kuma haɗa da kan iyakar Zirin Gaza da Masar, in ji shugaban wata gidauniyar Larabawa, Samir Ragheb, wadda ke da cibiya a birnin Alkahira.

Sojojin Isra'ila sun kasance suna iko da kan iyaka da Masar a cikin Gaza, ciki har da yanki mai nisan kilomita 14 kusa da kan iyakar Masar da aka fi sani da kwarkwaɗon Philadelphi (wanda aka fi sani da axis Salah El-Din), har sai da ta fice daga yankin a shekara ta 2005.

Daga nan ne Isra'ila ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da Masar mai suna Philadelphi Protocol wadda suka danganta da yarjejeniyar zaman lafiya.

Hakan ya bai wa Masar damar tura sojoji 750 a yankin da ake kira Zone C a kan iyakarta da Gaza da kuma wajen shiyyar Zone D.

Ba rundunar soji ba ce, amma rundunar ƴansanda ce kuma aikinta shi ne yaƙi da ta’addanci da kutsawa kan iyaka.

Yarjejeniyar ta asali a shekarar 1979 ta hana tura sojojin Masar zuwa yankin Zone C kuma ta taƙaita kasancewar jami'an tsaro a wurin ga dakarun kasashen duniya masu sa ido, da kuma ƴansandan farar hula na Masar ɗauke da ƙananan makamai.

Amma Shafi na ɗaya na yarjejeniyar zaman lafiyar ya ba da damar yin kwaskwarima ga yarjejeniyar tsaro bisa buƙatar daya daga cikin bangarorin, tare da amincewar su.

A shekara ta 2021, Masar da Isra'ila sun ba da sanarwar karfafa rundunar sojojin Masar a yankin Zone C tare da tura tankokin yaki, da motoci masu sulke da kuma dakaru don yaki da ta'addanci da kuma tunkarar barazanar mayakan IS a arewacin Sinai.

'Matakin soji a Rafah na iya zama keta yarjejeniya'

Dr Ayman Salameh, farfesa a fannin dokokin kasashen duniya, kuma mamba a majalisar kula da harkokin wajen Masar, ya ce Isra'ila ba ta da damar tura ƙarin sojoji a yankin Zone D ba tare da izini daga Masar ba, hatta da manufar kare tsaron kasa na kasashen biyu.

Dr Salameh ya kara da cewa, duk wani matakin da Isra'ila za ta ɗauka na jibge sojojinta a kan iyakar kasa da kasa da Masar, ko da ba tare da wata niyyar rikici ko aikin soji ba, ya kamata a dauki matakin a matsayin ya saɓa wa ka'idojin yarjejeniyar zaman lafiya da tsaro wanda zai yi barazana ga tsaron kasa na Masar.

"Masar na da haƙƙi, a cikin kowane ko da yana nuna barazana ga tsaron kasa, don yin nazari ko hana amfani da yarjejeniyar da Isra'ila." In ji shi.

Wannan ya samo asali ne daga yarjejeniyar Vienna kan Yarjejeniya ta 1969, wadda ta bai wa duk wani mai hannu na kasa da kasa damar soke ko hana amfani da ita gaba daya ko a wani bangare, idan har akwai wata barazana kai tsaye ga ƙasa ko ‘yancin kai na kasa ga yarjejeniyar.

Masar ta yi watsi da kalaman da wasu manyan jami'an gwamnatin Isra'ila suka yi game da aniyarsu ta kaddamar da farmakin soji a birnin Rafah, tare da gargadin fuskantar "mummunan sakamako" kan wannan mataki.

Wannan ya zo daidai da karin kashedin kasa da kasa da Larabawa kan yi kan "mummunan yanayi a Gaza" idan Isra'ila ta ci gaba da aniyarta.

Masar dai na fargabar cewa dubban Falasdinawa za su tsallaka kan iyakarta idan lamarin ya ƙara taɓarɓarewa a birnin, wanda a yanzu yake ɗauke da Falasdinawa kusan miliyan 1.4.

Ra'ayi daban-daban a Isra'ila

Yohanan Tzoreff, wani babban mai bincike a cibiyar nazarin harkokin tsaron ƙasa a Isra'ila, ya ce yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Masar da Isra'ila ba ta hana Isra'ila 'yancin kare tsaronta da tsaron iyakokinta ba.

Ya jaddada mahimmancin yarjejeniyar ga kasashen biyu, ya kuma yi watsi da damuwar Masar game da yiwuwar kai farmakin soji a cikin Rafah, yana mai cewa akwai yunƙurin Isra'ila na hada kai da Masar dangane da halin da ake ciki.

Ana sa ran Alkahira za ta karɓi baƙuncin tattaunawar da za ta hada da daraktan hukumar tattara bayanan sirri ta CIA William Burns da wata tawagar jami'an tsaron Isra'ila domin tattauna shirin Isra'ila na yiwuwar kai farmaki a Rafah.

Kazalika za su tattauna batutuwan baya-bayan nan a tattaunawar tsagaita buɗe wuta, da kuma musayar fursunoni da aka yi garkuwa da su tsakanin Isra'ila da Hamas, in ji kafofin yaɗa labarai.

Haɗin gwiwar Masar da Isra'ila?

Masar ta sha musanta wanzuwar wani haɗin gwiwa tsakanin Masar da Isra'ila kan ayyukan soji da ke gudana a yankin Zirin Gaza a halin yanzu, musamman a yankin Philadelphi ko kuma yankin Zone D.

A cikin 'yan makonnin nan dai an samu saɓani tsakanin Masar da Isra'ila, yayin da jami'an Isra'ila suka sanar da yiwuwar kai farmakin soji a Rafah, da kuma yiwuwar karbe iko da mashigin Philadelphi, suna masu zargin Alkahira da gazawa wajen hana Hamas safarar makamai zuwa Gaza.

Masar ta yi watsi da waɗannan zarge-zargen, tare da jaddada ikonta na sarrafa iyakokinta gaba ɗaya.

Har ila yau, ta musanta wanzuwar ramuka, ko safarar makamai da abubuwan fashewa, ko kayan aikinsu daga yankin Masar zuwa Zirin Gaza.

Masar ta kuma yi gargadin abin da ta bayyana a matsayin "kokarin da Isra'ila ke yi na samar da halaccin mamaye mashigin Philadelphi", inda ta yi nuni da cewa hakan zai haifar da "mummunar illa ga dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu".