Dole ne tsagaita wuta a Gaza ta faru bisa daftarin da Amurka ta gabatar - Hamas

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Raffi Berg, Sofia Ferreira Santos & Rushdi Aboualouf
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, London & Istanbul
- Lokacin karatu: Minti 3
Hamas ta ce duk wani shirin tsagaita wuta a Gaza zai dogara ne kan tattaunawar da aka yi tun a watan Yuli, wato wata ɗaya da rabi da ya gabata kenan, maimakon fara sabon zagaye na shawarwari.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi da dare, ƙungiyar ta buƙaci masu shiga tsakani "su gabatar da wani shiri na aiwatar da abin da kungiyar ta amince da shi a ranar 2 ga Yulin 2024, bisa manufar Shugaban Amurka Joe Biden da kuma ƙudirin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya".
A ranar 2 ga watan Yuli Hamas ta mayar da martani ga shawarar tsagaita buɗe wuta da Shugaba Biden ya gabatar a ranar 30 ga watan Mayu.
Yayin da ba a bayyana cikakken martanin Hamas a filli ba, an fahimci cewa kungiyar ta nemi a kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya a farkon kwanakin yarjejeniyar maimakon a tsakiyar yarjejeniyar kamar yadda Biden ya gabatar.
An kuma ci gaba da tattaunawar mako guda bayan martanin Hamas, amma tattaunawar ta yi tsami saboda sabbin sharuɗɗaan da Isra'ila ta gabatar.
A cewar majiyoyin Hamas da ke magana da BBC, wadannan sharuddan sun hada da tantance Falasdinawa yayin da suka koma arewacin Gaza da kuma iko da hanyar Philadelphi da ke kan iyaka da Masar.
Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun kuma bayar da rahoton cewa, Firaminista Benjamin Netanyahu ne ya gabatar da wadannan sabbin buƙatu, lamarin da ya haifar da rashin jituwa tsakanin tawagar da ke tattaunawa.
A makon da ya gabata ne masu shiga tsakani daga Qatar da Egypt da kuma Amurka suka buƙaci Isra'ila da Hamas su dawo da tattaunawar tsagaita wuta, da kuma yarjejeniyar sakin waɗanda aka yi garkuwa da su.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masu shiga tsakanin sun ce a shirye suke su gabatar da wani daftarin da zai shawo kan bambancin aiwatar da yarjejeniyar bisa daftarin Biden.
Isra'ila dai ta faɗa a ranar Alhamis cewa ta ce za ta aike da tawagar masu shiga tsakani su halarci taron.
Hamas kuma ta yi watsi da sabuwar shawarar, amma BBC ta fahimci cewa ƙungiyar a shirye take ta dawo da tattaunawar a kafin Isra'ila ta gabatar da sabbin sharuddan.
A ranar Litinin ne shugabannin Birtaniya da Faransa da Jamus cikin wata sanarwar haɗin gwiwa suka yi kira da a dawo da tattaunawa, inda suka ce.
"Mun yarda da cewa bai kamata a ci gaba da samun wani jinkiri ba." in ji sanarwar.
"Muna aiki matuƙa tare da dukkan bangarori don hana yaɗuwar rikicin, kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen rage tashe-tashen hankali da neman hanyar samun kwanciyar hankali."
Ƙasashen sun kuma yi kira da a kwantar da tarzoma a yankin Gabas ta Tsakiya - wadda ta taso tun bayan kisan manyan jami'an Hamas da kungiyar Hezbollah ta Lebanon.
Sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin ya bayar da umarnin tura jirgin yaƙi mai tafiya a ƙarƙashin ruwa zuwa yankin Gabas ta Tsakiya, wanda zai je ya haɗe da jirgin ruwan yaƙinta mai dakon jiragen sama na yaƙi mai suna Abraham Lincoln.
Iran ta faɗa a baya cewa za ta mayar da martani kan kisan shugaban Hamas Isma'il a lokacin da ya dace kuma ta hanyar da ya kamata, inda ta ƙara da cewa Amurka ce ke da alhakin kisan shugaban saboda goyon bayan da take bai wa Isra'ila.
Iran tana ɗora alhakin kisan ne kan Isra'ila, kodayake Isra'ilar ba ta ce komai ba kan batun har zuwa yanzu.
A gefe guda kuma, rundunar sojin Isra'ila ta umarci dubban mazauna yankin Khan Younis na kudancin Gaza da su sauya matsuguni zuwa wuraren da ta kira "tudun tsira".
Umarnin ya zo ne bayan wani harin Isra'ila da ya kashe aƙalla mutum 70 a kan wata makaranta.










