Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotunan yadda 'yan Syria suka yi shagalin korar gwamnatin Bashar al-Assad
A sassan Syria, musamman Damascus babban birnin kasar, dubban mutane sun taru domin gabatar da sallar Juma'ah ta farko bayan kifewar gwamnatin Assad.
Daruruwan yan Syria sun isa massallacin Umayyad a cikin birnin kafin suka yi tururwa zuwa wani dandali da ke kusa.
Gungun mutane sun taru a dandalin Saadallah al-Jabiri da ke Aleppo domin murnar kawo karshen gwamnatin Assad, su na furta kalaman sauya gwamnati tare da daga abun da ake gani ita ce tutar yanci.
Birnin Aleppo yayi fama da fada mai tsanani tasakanin dakarun yan hamayya da dakarun gwamnati a lokacin yakin basasan.
A farkon wannan watan, birnin ya zama babban birni na farko da yan tawayen suka kwace.
Wadannan hotunan na nuna mutane a kan titunan Sweida, wani birni a kudancin Syria, kusa da iyakarta da Jordan.
Taron na yau zai tuna musu da zanga-zangar kin jinin Assad da aka yi a shekarar 2011 - kafin hambrarren shugaban ya yi kokarin murkushe masu bore, wanda ya kai ga shafe shekara 13 ana yakin basasa.
An kuma ga jami'an tsaro sanye da baƙaƙen kaya - ɗauke da bindigogi.
Mayaƙa ne na ƙungiyar Hayat Tahrir al-Sham wadda ta taka muhimmiyar rawa wajen kawar da gwamnatin Bashar al-Assad.
Ana kallon tarukan a matsayin na murna - wanda ke bayyana dalilan da suka sa aka ga wasu yan Syria sanye da kayan SpongeBob Squarepants - duk da suna kusa da jami'in tsaron kungiyar HTS da ke dauke da bindiga.