Hodan Mahmoud: Matar da aka zartar wa hukuncin kisa kan kashe ƴar aiki

    • Marubuci, Fardowsa Hanshi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Weriye BBC
  • Lokacin karatu: Minti 3

Hukumomi a yankin Puntland na ƙasar Somaliya sun zartar da hukuncin kisa kan matar da aka samu da kisan wata yarinya ƴar shekara 14, wani hukunci da ba a saba gani ba a yankin.

Wannan ya nuna yadda ake zartar da hukunce-hukunce na qisasi bisa tsarin shari'ar Musulunci a yankin, da kuma yadda dangi ke iya neman hakkinsu kai-tsaye ba tare da neman diyya ta kuɗi ba.

An zarta wa Hodan Mohamud hukuncin kisan ranar Talata a birnin Galkayo, bayan da kotun ta same ta da laifin kisan Sabirin Saylaan Abdille, ƴar aikinta wadda yar dangin mijinta ce.

An aikata kisan ne watanni da dama da suka gabata, bayanai sun nuna cewa Sabirin ta rayu a gidan matar cikin ƙunci da takurawa da cin zarafi daban-daban.

An aiwatar da hukuncin kisan ƙarƙashin dokokin qisasi, wanda ke bai wa dangin wanda aka kashe damar zaɓen hukuncin kisa ga wanda ya kashe musu ɗan'uwa maimakon karɓar diyya.

Dangin Sabirin sun zaɓi qisasi, lamarin da ya sa aka kashe Hodan Mahmoud ta hanyar harbin bindiga.

Aiwatar da hukuncin na zuwa ne bayan yi wa dokokin yankin gyare-gyare, domin tilasta amfani da dokokin Musulunci kan shari'o'in da suka shafi kisan kai, bayan da yankin ya fuskanci yawan kashe-kashe a baya.

Birnin, wanda ke tsakanin Puntland da Galmudug, ya sha fama da matsalolin tsaro inda ake yawan samun rigingimun siyasa da rikice-rikice.

Tun da farko kotun Galkayon ta samu mijinta, Abdiasis Nur Xashi, da kaifin nuna halin ko-in-kula kan halin da Sabirin ke ciki, inda kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara ɗaya tare da cinsa tarar dala 500.

Alkalin kotun Mai shari'a, Mahmoud Abdisalan Abdulle, ya ce hukuncin ya yi daidai da tanadin dokokin Somaliya da ta yarda ta yi aiki da dokokin Musulunci, inda kuma ayar Qur'ani ta nuna cewa hukuncin wanda ya kashe shi ne a kashe shi.

Mutuwar Sabiri ya ɗauki hankalin al'ummar yankin Puntland, inda ƙungiyoyin fararen hula da na mata da masu kare haƙƙin yan aiki suka riƙa kiraye-kirayen yin adalci ga wadda aka kashen.

An adana gawar Sabirin a firji zuwa wani lokaci kafin yi mata jana'iza, inda wasu mata suka riƙa kiran a jinkirta janazar har sai an yi mata adalci.

Rahotonni sun ce an ɗauki gawar Hodan Mohamud zuwa asibitin Galkayo a yau bayan zartar mata hukuncin kisan, inda mata da yawa suka taru suna son ganin gawar, don ''tabbatar da ita aka aiwatar wa hukuncin''.

Gwamnan yankin Mudug da abin ya faru ya halarci wurin da aka zartar da hukuncin kisan, ya kuma shaida wa BBC cewa:

"Ta yaya za a aiwatar da hukuncin da aka yanke wa wata a kan wata daban, wannan ba zai taɓa faruwa ba, a yau an zartar da hukunci kan Hodan da aka samu da laifin kisan Sabirin,'' in ji Faysal Sheikh Ali.

Ya ƙara da cewa an nuna wa wasu mutane gawar domin tabbatar da aiwatar da hukunci kan Hodan.

Wace ce Sabirin?

Sabirin Saylaan Cabdille Ƙaramar yarinya ce da ke matsayin ƴar aikin gida - wadda ke zaune da danginta.

Sakamakon binciken gwaji da aka yi wa gawarta ya nuna cewa ta mutu ne sakamakon tsananin azabtarwa, inda aka samu taɓo-taɓo da sabbin raunuka a jikinta.

Lamarinta ya nuna irin halin uƙuba da ƴan aikin gida da ƙananan yara ke fuskanta a a yankin Puntland, inda aka buƙaci ɗaukar matakan kare ƴan aiki a yankin.

Haka kuma hukuncin da aka yanke wa Hodan Mahmoud ya janyo muhawara game da ƙarfin tsarin shari'ar yankuna da aiki da shari'ar Musulunci kan shari'o'in kisan kai.

Mutane da dama sun bayyana fushinsu kan kisan a kafofin sada zumunta da gidajen yaɗa labaru, inda suka nuna kaɗuwa kan lamarin tare da buƙatar yin adalci.