Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tinubu zai ƙaddamar da titin Lagos-Calabar wanda aka yi kashi huɗu cikin ɗari kawai
A ranar Asabar din nan Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai kaddamar da babban titin nan na Lagos zuwa Calabar, wanda yawan kudin da gwamnatinsa ta ware don aikin ya jawo ka-ce-na-ce a kasar.
Za a gina duk kilomita daya na titin mai tsawon kilomita 750 a kan naira miliyan dubu hudu, inda gaba dayansa zai ci wajen naira triliyan uku, kamar yadda bayanin da ministan ayyuka na kasar Injiniya David Umahi ya bayyana a wata hira da gidan talabijin na TVC ya taba yi da shi a wani lokaci a can baya.
A tattaunawarsa da BBC karamin ministan ayyuka Bello Muhammad Goronyo ya ce titin yana da matukar muhimmanci wajen binkasa tattalin arzikin Najeriya da kuma bude hanyoyin hada-hadar kasuwanci da cigaban tattalin arziki da samar wa matasa aikin yi.
''Aikin wani bangare ne na wasu muhimman ayyuka da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kudiri aniyar yi a kasar nan, domin a bude tattalin arziki kuma jama'a su samu walwala, sannan kuma ya rage wahalhalu na sufurin jama'a da kayayyaki da abubuwan more rayuwa,'' in ji ministan.
Dangane da sukar da ake yi game da batu kaddamar da titin alhalin ko rabi-rabin aikin ba a y iba, ministan ya ce : ''Ai kaddamar da titi daban kammalawa daban. Akan ma kaddamar da titi ko an kare ko ba a kare ba.''
Ya kuma tabbatar da cewa zuwa yanzu tsawon kilomita talatin kawai aka yi na titin mai nisan kilomita 750.
Sannan ya ce a aikin da aka kammala an yi shuke-shuke da sanya fitilu, kana kuma an yi tanadin layin dogo a tsakiyarsa, wanda ana tunanin nan bada dadewa ba a cewarsa zuwa shekaru masu zuwa shi ma za a kaddamar da shi.
Ganin cewa a tsawon mulkin gwamnatin na shekara biyu tsawon kilomita talatin kawai aka yi na aikin, abin da ake ganin kamar aikin na tafiyar hawainiya, Hon Goronya ya ce, ya kamata a sani cewa titin yana daga cikin tituna da shugaban kasar ya kirkiro da kanshi, bai hada da wasu sauran tituna da gwamnatin ta gaji aikinsu ba.
''Mun gaji ayyuka da sun kai 2600 da kusan 52 kuma babu wanda shugaban kasa ya ce a daina,'' in ji shi.
''Kuma a sani cewa baya ga wannan titi a Lagos zuwa kalaba, akwai titin Sokoto zuwa Legas zuwa Badagry wanda zai shiga Sokoto ya bi ta Kebbi ya ratsa ta Naija ya bi Kwara ya keta ta Oyo, ya bi ta Ogun sannan ya shiga Legas, ana nan ana aikin.'' Kamar yadda ya ce.
Alhaji Bello ya kuma ce a halin da ake ciki gwamnatinsu ta bayar da kwangilar ci gaba da aikin Abuja zuwa Kaduna zuwa Zaria, inda ya ce ana nan ana aikin.
Haka kuma ya ce, gwamnatinsu ta gaji aikin titin Zaria zuwa Funtua zuwa Gusau zuwa Sokoto.
''Kuma wannan gwamnati da ta zo ta sake tsarin aikin inda a yanzu maimakon a yi shi kamar sauran tituna da aka saba, ta ce a yi na kankare domin ya kasance mai inganci sosai, ta yadda zai yi karko fiye da shekara 15 zuwa 20 da sauran tituna ke yi.
'' Baya ga wannan shigowar wannan gwamnati mun kammala aiki kusan260 saboda haka ba maganar wannan kilomita talatin ake magana ba,'' in ji karamin ministan