Me ya sa har yanzu gwamnatin Najeriya ta gaza kawo ƙarshen garkuwa da jama'a?

Asalin hoton, Ifeanyi Immanuel Bakwenye / AFP via Getty Images
Najeriya na fuskantar ɗaya daga cikin matsalar garkuwa da mutane mafi muni a tarihin ƙasar.
Fiye da ɗalibai da malamai 300 ake hasashen ƴan bindiga sun yi garkuwa da su a makaratar Katolika ta St Mary da ke jihar Neja a ranar juma'ar da ta gabata, duk da dai rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin ɗaliban sun tsere kuma a yanzu suna tare da iyayensu.
Wannan shi ne hari irinsa na uku da ƴan bindiga suka kai a ƙasar cikin mako guda.
Matsalar satar mutane domin neman kuɗin fansa da ƴan bindiga ke yi na ci gaba da zama babban kalubale a sassa daban daban na Najeriya.
Fiye da shekaru goma kenan tun bayan da mayaƙan Boko Haram suka sace ƴanmata 276 daga makarantarsu da ke garin Chibok a 2014.
Lamarin dai ya ja hankalin ƙasashen waje, tare da janyo fafutukar a nemo su daga ƙasashen duniya.
Tun bayan wannan lokaci, da dama daga cikin ƴan matan sun tsere, ko kuma an sako su, amma zuwa yanzu ba a gano aƙalla mata 100 ba.
Me yasa har yanzu ake garkuwa da mutane?

Asalin hoton, John Okunyomih/ AFP via Getty Images
Makarantun da ke karkara

Asalin hoton, BBC VISUAL JOURNALISM
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Akasarin yankuna da ke arewacin Najeriya na fama da rashin tsaro mai muni.
Yankin arewa maso yammaci da arewa ta tsakiya ne suka fi fama da matsalar, inda ƴan bindigar ke cin karensu babu babbaka a yankuna karkara.
A nan, ƴan bindigar kan bi wani tsari - su zo a kan babura, su yi harbe harbe domin razana mutane, su kwashi mutane, sannan su tsere cikin dazukan da ke kusa.
Masana harkokin tsaro na ganin cewa ƴan bindigar na kai hari ne saboda samun kuɗi ba wai saboda addini ba, kuma suna kai hari ne kan makarantu saboda suna ganin basu da tsaro mai ƙarfi.
Masanan sun kuma ce masu garkuwa da mutanen na ganin iyaye za su fi samun ƙwarin gwiwar biyan kuɗin fansa domin ganin ƴaƴansu sun dawo gare su.
A can yankin arewa maso gabashi kuwa, ƙungiyoyi kamar su Boko Haram waɗanda su ma ke satar gomman mutane, na yin hakan ne da sunan addini ba saboda kuɗi ba, ƙarƙashin abin da suka kira ƙin amincewa da yin ilimin boko da kuma yadda suke ganin bai kamata a ce mata na samun ilimi ba.
Ta'addancin da suka shafe fiye da shekara goma suna yi, ya yi sanadiyyar raba dubban mutane daga gidajensu, a cewar Majalisar ɗinkin duniya.
Masana tsaro na kuma ganin matsalar tsaro na ƙara taɓarɓarewa ne saboda ƙaruwar shigo da makamai cikin Najeriya, sakamakon yadda mutuwar Muammar Gaddafi na Libya fiye da shekaru 10 da suka gabata ya janyo ƙara lalacewar iyakokin Najeriya.

Asalin hoton, Adam Abu-bashal/Anadolu via Getty Images
Ba kuɗin fansa kuma ba ilimi

Asalin hoton, Pius Utomi Ekpei/AFP via Getty Images
An haramta biyan kuɗin fansa, a yunƙurin katse yadda ƙungiyoyin ƴan bindiga ke samun kuɗaɗe, amma hakan bai yi wani tasiri ba.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ɗage tafiye tafiyen da zai yi zuwa ƙasashen waje saboda matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta.
An kuma kuma rufe makarantun gwamnati a wasu jihohin ƙasar.
Sai dai kuma ƙaruwar matsalolin tsaron na ci gaba da sanya fushi da farbaga a zukatan ƴan Najeriya, inda alummar ƙasar ke kiran a ƙara tsaurara matakan kare yara da alummomi.
Sojojin Najeriya na ƙoƙarin magance matsalar garkuwa da mutane a faɗin arewacin ƙasar, musamman arewa maso gabas, amma babu isassun kayyayakin aiki.
A arewa maso yammaci kuwa, gwamnati na dogaro da shugabannin alummomi da masu riƙe da sarautu su yi yunƙurin ƙulla yarjejeniyoyi da gungun ƴan bindigar domin su sako yaran da suka sace.
Rawar da tattalin arziƙi ke taka wa
Masu sharhi kan lamurran tsaro da dama na cewa akwai alaƙa ta ƙut da ƙut tsakanin yanayin tattalin arziƙin Najeriya da rashin abubuwan more rayuwa da ƙaruwar matsalar tsaro, musamman a arewaci.
A misali, rashin samun isashen wutar lantarki na durƙushe damarmaki da yin ƙirƙira da samar da aikin yi.
Wata maƙala da wani gidan jarida a Najeriya mai suna BusinessDay ya wallafa ya ce rashin aikin yi ya sa '' Satar mutane ga wasu matasa ya zama tamkar wani hanya mai sauƙi na samun arziki.
Wani kamfani mai bincike kan lamuran tsaro a Afirka, SBM, ya ce abin da ake buƙata shi ne 'fasahar zamani na gano inda mutum ya ke' domin tarwatsa masu samar wa ƴan bindigar kuɗaɗe, amma kuma wajibi ne a farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar domin kawo ƙarshen shigar mutane harkar.''
Abin da Trump ke cewa kan Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Harin da aka kai ranar juma'a na zuwa ne bayan wasu masu tsatsaurar ra'ayi a Amurka, ciki har da shugaba Donald Trump, sun yi zargin cewa ana kashe kiristoci a Najeriya, wani zargi da gwamnatin ƙasar ta musanta.
A tsawon watanni, ƴan gwagwarmaya da ƴan siyasa a Washington na ta zargin cewa ƴan bindiga masu tsatsaurar ra'ayi na kai hari da gangan kan Kiristoci a Najeriya.
A fakon watannan, Trump ya ce zai aika sojoji Najeriya idan har gwamnatin ƙasar '' ta bari aka ci gaba da kashe Kiristoci''.
Gwamnatin Najeriyar ta bayyana zargin ana kashe kiristoci a matsayin '' sauya asalin abin da ke faruwa''.
Wani jami'in gwamnati ya ce '' ƴan ta'addan na kai hari ne kan duk wanda ya ƙi yarda da aƙidar su, Musulmi ko Kirista, har waɗanda basu da addini.''
A arewa maso gabashi, ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi sun shafe fiye da shekara 10 suna ta'asa.
Ƙungiyoyin da ke sanya ido kan ayyukan masu tayar da ƙayar baya sun ce akasarin waɗanda lamarin ya rutsa da su musulmai ne saboda akasarin hare haren ana kai wa ne a arwacin ƙasar wanda akasarin alummar sa mabiya addinin Islama ne.
A tsakiyar Najeriya kuwa, ana samun munanan hare hare tsakanin makiyaya- waɗanda akasari musulmai ne, da manoma - waɗanda su kuma mafiya yawa kiristoci ne.
Sai dai masu sharhi na ganin abin da ke yawan kawo rikicin shi ne gasa wajen samun abubuwa kamar ruwa ko fili, ba wai don addini ba.










