Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne AM Yerima, matashin sojan da ya yi sa-in-sa da Wike?
Tun bayan da aka samu wata hatsaniya a ranar Talata da yamma 11 ga watan nan na Nuwamba 2025, a tsakanin ministan babban birnin Najeriya, Abuja, Nyesom Wike da jami'an sojin ƙasar saboda sojojin sun hana ministan shiga wani fili, ake ta yaɗa labarai da ra'ayoyi daban-daban a kan lamarin.
Baya ga fassara da ake yi wa lamarin ta ɓangarori daban-daban - na siyasa da mulki da kuma dokoki da ƙa'idoji na mulki, wani abu kuma da ke ɗaukan hankalin jama'a shi ne, jagoran sojojin da suka yi wannan dambarwa da ministan na Abuja da tawagarsa.
Jagoran tawagar sojojin shi ne Laftanar AM Yerima, wanda matashin ƙaramin hafsan sojin ruwa na Najeriya ne, wanda kuma ya kasance ne a wajen bisa umarnin mai gidansa tsohon shugaban rundunar sojin ruwa ta Najeriya, Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo (mai ritaya), wanda shi ne mai filin da ake taƙaddama a kansa.
Abin da ya faru a tsakanin ministan na Abuja da wannan matashin soja ya ɗauki hankalin jama'a da dama, musamman yadda wasu ke mamakin yadda wannan matashin sojan ya kasance a lokacin ba tare da nuna wata fargaba ko tsoro ba.
A dangane da wannan abu da wasu ke ganin kamar wata jarunta ce sojan ya nuna, duk da irin kalamai da barazana da Wike yake yi masa a lokacin, BBC ta yi nazari kan rayuwar wannan matashi, Laftanar AM Yerima.
Wane ne AM Yerima?
Sunansa Laftanar Ahmed Yerima kuma sojan ruwa ne wanda aka haifa a birnin Kaduna kuma ya girma a can da kuma birnin Fatakwal na jihar Rivers, duk da cewa ɗan asalin garin Fune ne da ke jihar Yobe.
A shekarar 2011 ne Ahmed Yarima, mai shekaru 33 da haihuwa ya fara karatu a sashen koyar da aikin jarida a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
Wani abokin karatun Yerima ya shaida wa BBC cewa suna yi wa matashin laƙabi da MD.
"Tun a lokacin matashi ne siriri, dogo kuma marar tsoro sannan kuma mutum ne mai iya hulɗa da abokan karatunsa."
To sai dai kuma bayan Yerima ya bar jami'ar Ahmadu Bello bayan shekara ɗaya sakamakon samun gurbi a kwalejin horas da sojoji ta NDA da ke Kaduna a 2012.
Yerima ya fito a matsayin Laftanar na sojan ruwa a shekarar 2017.
A 2018 ne Yerima ya fara atisayen haɗin gwaiwa na ƙasa da ƙasa domin yaƙar ta'addanci da ake kira da "Exercise Flintlock" a birnin Agadez da ke jamhuriyar Nijar.
Gaske ne mahaifin Yerima soja ne?
Rahotanni dai sun nuna cewa matashin sojan ɗa ne ga tsohon daraktan yaɗa labarai na rundunar tsaro ta Najeriya, Birgediya Janar Mohammed Yerima.
To sai dai binciken da BBC ta yi ya gano cewa mahaifin AM Yerima ba soja ba ne - ɗan kasuwa ne da ke da yawan shagunan a wani birni da ke kudu maso kudu.
"Gaskiya ba haka ba ne. Mahaifinsa fitaccen ɗan kasuwa ne da ke gudanar da al'amuransa a kudancin Najeriya. Ya kwashi iyalansa daga Kaduna zuwa birnin inda a can ne suka ƙarasa girma ciki har da shi Lafatanar Yerima," in ji wani abokin AM Yerima.
Wane ne Awwal Zubairu Gambo?
Shi ne mutumin da aka ce filinsa ne AM Yerima da wasu sojoji ke gadi.
A watan Janairu 2021, ne marigayi shugaba Muhammad Buhari ya naɗa Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo a matsayin babban hafsan rundunar sojin ruwa na 21, inda ya maye gurbin Ibok Ekwe Ibas.
An haifi Awwal Zubairu a ranar Afrilu 22 a shekarar 1966 a ƙaramar hukumar Nassarawa da ke jihar Kano.
Vice Admiral Awwal ya shiga kwalejin horar da sojoji ta NDA da ke Kaduna a watan Satumban 1984, inda ya fito a matsayin ƙaramin laftanar a 1989.
Bayani kan filin da ake rigima a kansa
Ana dai zargin cewa filin da ake taƙaddama a kansa mallakar Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo ne.
Mai magana da yawun ministan na Abuja, Nyesom Wike, Lere Olayinka ya fayya ce yadda al'amarin take, a wata tattaunawa da gidan talbijin na Channels.
Olayinka ya ce "wasu mutane ne suka damfari tsohon hafsan dangane da filin amma maimamakon ya nemi ɗauki sai ya ƙwammace ya yi amfani da ƙarfin soji."
Ya ƙara da cewa a baya an sayar wa da wani kamfani filin ne.
"A 2007, an bai wa kamfanin yin gidajen na Santos Estate Limited domin gina wani dandalin shaƙatawa. Kamfanin bai gina komai ba saboda titi ne kenan ba za a iya gina titi ba."
"A 2022, kamfanin ya rubuta wa ma'aikatar raya birnin tarayya cewa suna son mayar da filin zuwa wani abun da zai rinka kawo musu kuɗin shiga amma kuma suna jiran amincewar minista kafin su sayar wa da mutane filin."
" Ɗaya daga cikin mutanen da suka sayi filin shi ne tsohon babban hafsan sojin na ruwa."
Sai dai kuma har kawo yanzu, tsohon hafsan sojin ruwan na Najeriya bai ce uffan ba dangane da bayanan da ofishin ministan Abujar ya fitar, idan har ta tabbata filin nasa ne.