Shaci-faɗi biyar da ake yaɗawa game da sauyin yanayi da ainihin gaskiyar su

    • Marubuci, Marco Silva
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Verify
  • Lokacin karatu: Minti 6

Yayin da ake ci gaba da gudanar da taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi a ƙasar Brazil, ƙarairayi game da sauyin yanayin na ci gaba da karakaina a shafukan sada zumunta, inda miliyoyin masu amfani da shafukan ke cin karo da su.

A wannan maƙale mun yi duba kan wasu ƙarairayi biyar tare da yin bayani kan abin da ya sa suka zama shaci-faɗi.

Iƙirari: 'Ba ɗan'adam ne ke haddasa sauyin yanayi ba'

Akwai saƙonni da dama da ke iƙirarin cewa ba ɗan'adam ba ne ke haddasa matsalar ɗumamar yanayi, ana wallafa irin wannan iƙirari a harsuna da dama ciki har da Ingilishi da Sifaniyanci da Rashanci da Faransanci da sauran su.

Da gaske ne duniya ta fuskanci lokuta da sanyi da zafi a tsawon zamunna, waɗanda kuma ƙaddarar ubangiji ne ke haifar da su, kamar amon duwatsu ko samun sauyi a yadda duniya ke juyawa.

Waɗannan sauye-sauye dama sun jima suna faruwa, kusan dubban shekaru in ma ba mu ce miliyoyi ba.

To amma a cikin shekara 150 da suka gabata kawai, duniya ta samu ƙarin ɗumama da kashi 1.3 a ma'aunin Salshiyos, a cewar Hukumar Kula da Yanayi da Duniya.

Yayin da wasu za su ga wannan ƙari a matsayin maras yawa, masana kimiyya sun ce wannan adadi na ƙari a ɗumin duniya ba a taɓa ganin irinsa cikin dubban shekaru.

Kuma wani kwamitin ƙasashen duniya kan sauyin yanayi (IPCC) ya ce wannan ''ko shakka babu'' ya faru ne sakamakon ayyukan ɗan'adam, musamman ta hanyar ƙonewar mayuka kamar fetur ko gas ko coal da sauransu.

IPCC hukuma ce ta MDD da ke haɗa kan masana kimiyya dominm nazarin bincike kan sauyin yanayi tare da fitar da rahotonni bisa hujjoji na abin da zai faru a duniya.

Ƙona makamashin mai kan fitar da yahakin da ke ɗumama duniya, mafi yawansa sinadarin 'carbon dioxide' (CO2), wanda ke zama tamkar bargo ga duniya, inda yake riƙe mafi yawan makamashi tare da sanya duniya ɗaukar ɗumi.

"Sauyin yanayi batu ne na imani ba; abu ne na hujja,'' a cewar Joyce Kimutai, ƙwararriya a fannin ilimin yanayi a jami'ar Imperial da ke London.

Iƙirari: Duniya sanyi take ƙarawa ba zafi ba

Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta - a wasu ƙasashe kamar Poland da Canada - na ganin cewa sanyi ya fi zafi yawa a ƙasashensu.

Suna kafa hujjarsu da hakan wajen rashin yarda da ɗumamar duniya.

Haka kuma akwai iƙirarin da ke yawo a shafukan intanet da ke cewa sanyi na ci gaba da mamaye duniya.

Kuma wannan kuskure ne.

Yayin da yanayi ke nufin gajeren yanayin duniya, Dumama kan ɗauki lokaci mai tsawo.

"Yanayin zafin duniya ya nuna cewa an samu ƙaruwar zafi a duniya, duk kuwa da cewa wasu yankunan sun samu sanyi,'' in ji Dokta Joseph Basconcillo, wani masanin yanayi a ƙasar Philippines.

Hukumar Hasashen Yanayi da Duniya, WMO ta ce tun shekarun 1980, bayan kowane shekara 10 ana samun ƙarin zafi a kan goman da suka gabata - a wani abu da ake tsammanin zai ci gaba.

WMO ta ce shekarar 2024 ce ta fio kowace zafi a duniya, inda aka samu ƙarin zafin da ya kai maki 1.55 a ma'aunin Salshiyos fiye da kowane lokaci tun 1800.

Iƙirari: Iskar Carbon ba ta gurɓata yanayi

Masu amfani da shafukan sada zumunta da ke musanta cewa ayyukan ɗan'adam ba sa gurɓata muhalli, sun kuma ƙara da cewa iskar Carbon na ba ''gurɓata duniya'', maimakon haka ma tana kasancewa ''abincin shukoki''.

Wasu saƙonni da BBC ta gani a harsunan Portugal da Croatian sun bayyana cewa ƙaruwar abubuwa a duniya kan taimaka wa yanayi.

Gurɓatattun abubuwa wasu al'amari ne da ke haifar da illa da muhalli da duniya ko lafiyar bil'adama.

A yanayi na yau da kullum, iskar carbon na da matuƙar amfani a duniya, idan babu iska irirn carbon, duniya ka iya zama mai tsananin sanyi, a cewar hukumar sararain samaniyar Amurka, Nasa.

Haka ma tsirrai kan yi amfani da iskar carbon da ruwa da kuma hasken rana - wajen samar da iskar Oxygen da ake shaƙa, wadda ta kasance ɗaya daga cikin ginshiƙin rayuwa.

To amma duk da amfanin iskar carbon ga duniya, masana kimiyya sun yi gargaɗin cewar idan ta yi yawa, takan iya ''gurɓata'' duniya saboda tana ɗumama duniya.

Yawan iskar carbon da ake fitarwa a duniya ta kai ƙololuwa a 2024, inda aka samu ƙari mafi yawa na iskar tun shekarun 1750, a cewar WMO.

Masana kimiyya sun bayayna cewa wasu ayyukan bil'adama ne ke haifar da ƙaruwar iskar carbon da ke ɗumama duniya, kuma sun ce suna haifar da barazana ga duniya.

"Dazuka na shiga barazanar gobara, amfanin gona na lalacewa sakamakon fari da ambaliya, sanna dabbobin daji na rasa muhallainsu,'' in ji Dr. Michelle Kalamandeen, Masanin muhalli a Canada.

Ikirari: Gobarar daji ba matsalar sauyin yanayi ba ce

A duk lokacin da aka samu ɓarkewar gobarar daji - kamar yadda aka samu a farkon wannan shekara a Amurka da Koriya ta Kudu da Turkiyya - wasu masu amfani da shafukan sada zumunta suna mayar da hankali da cewa wasu ne ke cinnata.

Suna masu ƙaryata batun cewa ɗumamar yanayi ke haddasata.

An kuma riƙa wallafa saƙonnin kame na mutanen da ake zargi cinna gobarar tare da zolayar masana kimiyya da ƴansiyasa dake alaƙanta matsalar da sauyin yanayi.

To amma yayin da gobara masu yawa kan samo asali daga ayyukan ɗaiɗaikun ƴan'adam, taƙaita matsalar ga dalili ɗaya ''babban kuskure ne'', in ji Dokta Dolors Armenteras, wanda ke bincike a fannin muhalli a Jami'ar Colombia.

Danganta wata gobara ga matsalar sauyin yanayi na da matuƙar wahala - saboda akwai matsaloli da dama da ke haifar da matsalar.

Iƙirarin: Babu alaƙar ɗumamar yanayi da bala'o'i

Iƙirarin cewa yawan ruwan sama da ambaliya da manyan guguwa ba su da alaƙa da sauyin yanayi, sun ci gaba da bayyana a shafukan sada zumunta.

A lokacin da aka samu mummunan ambaliya a Dubai da ke UAE da Valencia da ke Sifaniya, a shekarar da ta gabata, da dama masu amfani da shafukan sada zumunta sun riƙa ɗora alhakin hakan a kan wasu dalilai na daban.

To amma abin da ba su gane ba shi ne a wasu lokuta waɗannan matsaloli na faruwa sakamakon matsalar ɗumamar yanayi.

Duk da yake akwai wasu maganganu game da ingancin dabarun gyaran yanayi kamar shukar bishiyoyi, masana kimiyya sun yarda cewa hakan zai taimaka wajen raguwar yiwuwar ambaliya ko kuma guguwa mai girma.

To amma a wasu ƙasashen ciki har da Birtaniya, akwai ƙarin zuba jari tare da mayar da hankali kan makamashin da ba ya gurɓata muhalli, domin rage matsalar ɗumamar yanayi.

Masana kimiyyar sauyin yanayi sun ce ɗumamar yanayi na haifar da wasu matsaloli na munana yanayi, kamar samun tsananin zafi da samun mamakon ruwan sama.