Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An fara kwashe dubban mutane daga Malaga kan ambaliyar ruwa a Spain
Dubban mutane aka kwashen daga yankin Costa del Sol da ke kudancin Spain bayan sanarwar da masu hasashen yanayi suka fitar ta samun mamakon ruwa da ambaliya a nan gaba.
Hukamar agajin gaggawa ta Spain ta aika sakon gargaɗin samun ambaliya ta wayar tarho a yankin na Malaga bayan ƙarfe tara na yammacin Talata.
Yankunan da za su fuskancin tsattsauran yanayin da ake kira "Dana" sun haɗa da na 'yan yawon buɗe ido Marbella da Velez da kuma Estepona.
Akwai wasu yankuna a Spain da su ma aka turawa gargaɗin samun sabon yanayin mamakon ruwan sama kwanaki kaɗan bayan mummunar ambaliyar da aka samu a ƙasar da ya kashe sama da mutum 220.
An sanya yankin Tarragona da ke yankin arewa maso gabashin Catalonia cikin waɗanda za su fuskanci wannan ambaliya a yammacin Laraba.
An rufe kafatanin makarantu a yankin Malaga da ke kudancin ƙasar yayin da aka rufe manyan shagunan zamani wasu kuma a buɗe.
Kimanin mazauna yankin Guadalhorce da ke kusa da ruwa su 3,000 aka nemi su bar gidajensu, kamar yadda gwamnatin yankin Andalusia ta bayyana.
Ministan gwamnatin yankin Antonio Sanz ya ce: "Ba duka mutanen yankin muka kwashe ba, amma mun kwashe waɗanda suke kusa da gabar teku.
"An tattauna da gwamnatin Spain kan wannan hukunci domin ta karɓi mutanen da aka kwashe daga jami'an tsaro da hukumomin jihar."
Yanayin da aka furgita da shi a yankin Malaga ya sa an ɗage wasan farko da aka tsara na kofin Billie Jean tsakanin Spain da Poland kamar yadda hukumar Kwallon Tennis ta duniya ta bayyana.
An tsara ƙasashen biyu ne za su yi wasa a Malaga a ranar Litinin.
A wasu yankunan Spain ɗin an fara ɗaukar matakan kariya - a yankunan gabashi da kudancin Tekun Bahar Rum wanda su ne mafi fuskantar haɗari.
Hukumar hasashen yanayi ta Spaniya Aemet ta sanya wasu yankunan Valencia da Andalusia da kuma Tsibirin Balearic cikin waɗanda za a rika lura da su har zuwa ranar Alhamis.
Aemet ta yi gargaɗin samun ruwa kamar da bakin kwarya da tsawa da za su haifar da babbar ambaliya.
Wannan ne gargaɗi na biyu da aka yi mafi girma wanda ke nuna girma da haɗarin matsalar kamar yadda ma'aikatar ta bayyana.
A Valencia an rufe makarantu da harkokin wasanni a wasu yankunan da laka ta yi wa ɓarna a tsakiyar garin Aldaia.
Wa wani wuri da tawagar masu aikin ceto ke neman gawar wasu yara 'yan uwa su biyu waɗanda ruwa ya tafi da su a Valencia makonni biyu da suka gabata, an ce an gano gawarsu.
Iza Matia mai shekara 5 da Ruben Matia mai shekara 3 ruwa ne ya wufce su daga kafaɗar mahaifinsu a cikin gidansa da ke Valencia a yammacin ranar 29 ga watan Oktoba.
Yar uwar mahaifiyarsu Barabara Sastre ta tabbatarwa da BBC an gano gawarsu.
An kuma gano gawarwakin ne a wurare daban-daban.
"An gano gawar masoyana daga ƙarshe" in ji wani ɗan uwansu David Garcia wanda ya wallafa hakan a intanet.
A ranar Talata tawagar masu ceton ta mayar da hankali ne kan wani ɓangare na kogin Pollo da ke da nisan kilomita 6 daga gidansu.
Kafin gano su wani ɗan uwan mahaifinsu Ivan ya shaida wa BBC cewa sun gode da taimakon da kuma goyon bayan da suka samu har aka gano yan uwansa.
A ranar Litinin, an gano wani karen gidan a mace a wani gareji da ke kusa da Paiporta, sama da kilomita 12 daga gidansu da ke La Curra, kusa da garin Mas del Jutge.