Da gaske tsarin Tinubu kan tattalin arziki ne ya dace da Najeriya?

Tinubu

Asalin hoton, State House

Lokacin karatu: Minti 2

Masana tattalin arziki a Najeriya na ci gaba da tsokaci kan rahoton Bankin Duniya wanda ya ce matakan da shugaba Bola Tinubu ya ɗauka ne suka dace da ci gaban tattalin arzikin kasar.

Rahoton na Bankin Duniya ya ce akwai buƙatar Najeriya ta ci gaba da ɗaukar tsauraran matakan har nan da shekara 10 zuwa 15 domin dawo da tattalin arzikin Najeriyar kai saiti duk da kuncin da za a fuskanta.

Rahoton na ya haifar da saɓanin ra’ayi tsakanin masana tattalin arziki a kasar.

Bankin na duniya ya ce matakan da shugaba Bola Tinubu ke ɗauka su ne alkiblar da ta dace da tattalin arzikin Najeriya tare da cewa tattalin arzikin ƙasar ya fara ɗaukar saiti, duk da wahalar da matakan suka jefa yan ƙasa.

Masana tattalin arziki kamar Farfesa Maryam Abdu ta jami’ar jihar Kaduna a Najeriya na cikin wadanda suka yi suka ga rahoton na Bankin duniya tana mai cewa matakan da ake dauka ba su dace da halin da Najeriya ke ciki ba.

‘‘Gaskiya ni ban ga yadda za a yi su ce waɗannan matakan ne daidai bayan ana wahala ba. Ta ina ya zama daidai? Wannan kuɗin ruwan ya yi yawa, a duniya babu masu biyan irin wannan kuɗin ruwan.

‘‘Idan ka je Ingila ko Amurka, kuɗin ruwan su ko ɗaya bai kai haka ba.’’

Ta ƙara da cewa ‘‘idan har aka ci gaba da ƙara farashin man fetir, aka kuma ƙara kuɗin ruwa to babu yadda tattalin arzikin ƙasa zi gyaru, sai dai ya ƙara lalacewa’’

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai Dr Bashir Muhammad Acida na sashen nazarin tattalin arziki a jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto ya goyi bayan rahoton na Bankin Duniya amma a cewarsa ya rage ga gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakan da suka dace na rage wa yan ƙasa tasirin radadin matakan.

‘’Kamar kai ne ka haifi yaro ka kai shi makaranta, ya ƙare karatu ki masa aure, ya haihu kuma kai masa suna sannan ka ciyar da shi ka ciyar da dan ka ciyar da matar.

‘‘To irin wannan tsari ba tsari bane maganar gaskiya, domin duk lokacin da mahaifin ya rasu, ko kuma ya kasa ya kasance babu kuɗin da zai ɗauki wannan nauyin to za a yi faɗuwar guzuma,ƴan kwance, uwa ƙwance’’

Gwamnatin shuga Bola Ahmed Tinubu dai ta ce za ta ci gaba da matakanta na tattalin amma ko za a dauki tsawon shekara shekara 10 zuwa 15 na tsananta matakan kamar yadda bankin duniya ya bayar da shawara kafin yan kasa su ga sauki.

Matakan da bankin duniya ke yaba wa gwamnatin shugaba Tinubu na Najeriya sun haɗa da janye tallafin mai wanda ya haifar da tsadar fetur da ba a taɓa gani a kasar da kuma tsarin barin naira ta neman wa kanta daraja da ƙoƙarin bunƙasa kayan da ƙasar ke fitarwa, matakan da kuma yan ƙasar ke cewa sun jefa su cikin ƙunci.