Me ke jawo tankiya tsakanin Algeria da Mali?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Chris Ewokor
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Reporter, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 4
Algeria da Mali ƙasashe ne maƙwabtakan juna a nahiyar Afirka, amma a ƴan kwanakin nan dangantaka ta yi tsami a tsakaninsu, musamman bayan Algeria ta kakkaɓo wani jirgin Mali mara matuƙi mai tattaro bayanan sirri a ranar 31 ga watan Maris.
Ma'aikatar tsaron Algeria ta ce jirgin ya shiga ƙasar ne ba tare da izini ba, wanda hakan ya sa sojoji suka ɗauki matakin gaggawa.
Wannan matakin ne ya fara jawo tankiya a tsakanin ƙasashen biyu, waɗanda duk da suna maƙwabtaka, sun daɗe suna kwan-gaba-kwan-baya wajen samun alaƙa mai kyau.
A daidai lokacin da ƙasashen biyu ke fama da matsalar tsaro, ciki har da barazanar ƙungiyoyin ta'addanci masu ikirarin jihadi, batun jirgi mara matuƙin ya ƙara dawo da maganar tsaron sararin samaniya da ma tsaron iyakokin ƙasa.
Algeria, wadda ta daɗe tana da tsarin rashin katsalandan a harkokin cikin gida na wata ƙasa, haka kuma ba ta wasa wajen ɗaukar zafi a duk ƙasar da ta yi yunƙurin yi ma kutse ta sararin samaniya.
A ɗaya gefen kuma, Mali wadda a yanzu haka take fama da matsalolin cikin gida, ita ce ta fi shan suka a game da matsalar.
Wannan matsalar za ta iya kawo tsaiko a haɗin kan ƙasashen a nan gaba, wanda hakan zai iya yin tarnaƙi wajen magance tsaron yankin.
Ƴan siyasa da ƙungiyoyi ba sa jin daɗi katsalandan ɗin sojoji a harkokin siyasa, amma shugabannin soji na amfani da hare-haren mayaƙan Tuareg da masu ikirarin jihadi domin cigaba da zama a mulki, da kuma ƙulla alaƙa da Rasha bayan raba gari da Faransa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ƙasar na fama da hare-haren mayaƙa masu alaƙa da Al Qaeda, waɗanda suka fi yawa a arewacin ƙasar. Yadda mayaƙan suke karakaina a biranen yankin ne ya sa ake fargabar arewacin ƙasar na iya zama tarkon mutuwa da shirya hare-haren ta'addanci.
Algeria, wadda ita ce ƙasa mafi girman ƙasa, tana kuma ƙoƙarin ganin ta zama giwar arewacin Afirka. Ƙasa ce da ba ta cika fama da rikice-rikice ba idan aka kwatanta da maƙwabciyarta ta kudanci.
Iyaƙar ƙasar Mali da Algeria na da tsayin kusan kilomita 1,359 (mil 844) da ya shafi Mauritania ta arewa maso yamma da Nijar ta kudu maso gabas.
Mali ta fara fuskantar rikice-rikice ne a ƙarshe-ƙarshen 2011 lokacin da mayaƙan Tuareg suka faɗa ƙasar daga Libya ɗauke da muggan makamai.
Rashin daidaiton siyasar ƙasar ya sa mayaƙan suka ƙwace manyan biranen arewacin ƙasar, sannan da lamarin ya yi ƙamari, sai sojojin da suke fargabar mayaƙan za su iya hamɓarar da gwamnatin ƙasar, sai suka yi juyin mulki, suka karɓe mulki daga shugaba Amadou Toumani Touré a shekarar 2020.
Mene ne zarge-zargen?
Mali ta daɗe tana zargin Algeria da taimakon mayaƙan Tuareg, duk da cewa Algeria ta daɗe tana ƙaryata zargin. Amma dai wannan sabon saɓanin ya samo asali ne daga kakkaɓo jirgin mara matuƙi na Mali da Algeria ta yi a ranar 31 ga Maris.
Rundunar sojin Algeria ta ce jirgin ya kutsa sararin samaniyarta har zuwa kusa da bakin iyakar birnin Tin Zaoutine, wanda hakan ne ya sa suka ɗauki mataki. Ita kuma Mali a ɗaya ɓangaren ta ce ba ta karya doka ba domin jirgin bai tsallake bakin iyaka ba.
Lamarin ya jawo martani mai zafi daga sauran maƙwabtan Mali, musamman Nijar da Burkina Faso, waɗanda suka nuna goyon bayansu ga Mali.
Dukkan ƙasashen sun nuna takaicinsu kan matakin da Algeria ta ɗauka, sannan suka ce ta karya dokokin duniya.
Domin nuna rashin jin daɗinsu ne ƙasashen suka yi wa jakadunsu kiranye daga Algeria, wanda hakan ya ƙara ta'azzara rikicin na diflomasiyya.
Yaya matsalar za ta shafi ƙasashen yankin Sahel
Mali ta daɗe tana rataya da Algeria wajen tallafin yaƙin da take yi da ƴanbindiga, inda ta kasance kan gaba wajen shiga tsakanin Mali da mayaƙan Tuareg kafin juyin mulkin 2020.
Algeria, wadda ke da mutane kusan miliyan 46, faɗin ƙasar ya kusa ruɓanya na Mali, kuma tana da ƙarfi sosai a yankin. Ita kuma Mali, wadda ta fice daga ECOWAS, ta daɗe tana ta'allaƙa da Algeria a kasuwanci, musamman ta teku.
Amma yanzu da Algeria ta aika sojojin bakin iyakarta da Mali ya nuna akwai alamar za a raba gari.
Haka kuma ƙasashen AES sun ƙaƙaba haraji a kan kayayyakin ƙasashen Afirka ta yamma, wanda shi me zai shafi kasuwancinta da ECOWAS. A ƙarshen wannan watan ne dai ƙasashen ECOWAS za su zauna su tattauna domin harajin, amma lallai Mali na fuskantar matsalolin tattalin arziki.
Shin akwai alamar samun maslaha?
Yanzu dai Algeria da Mali suna cigaba musayar yawu ba tare da wata alamar tsagaitawa ba.
Sannan tsammanin da ake yi cewa Mauritani da Moroco za su shiga tsakani ya samu tsaiko. Yadda Algeria da Moroco suka daɗe ba sa ga maciji ya sa zai yi wahala ƙasar ta Moroco ta iya shiga tsakani.
Ita kuma Mauritani tana da alaƙa da mai kyau da Algeria da Mali, wanda hakan ya sa ta tsaya a tsakiya.
Masana suna ganin Mauritania za ta iya shiga tsakani domin samar da maslaha, duk da har yanzu ƙasar ba ta ce komai ba game da takun-saƙar.
A shekarar da ta gabata, ministan tsaron Mauritania ya ziyarci Mali domin rage zafin matsalar da ta fara kunnuwa a lokacin, bayan sun zargi sojojin Mali da mayaƙan Wagner da biyo ƴanbindiga har cikin yankinta.
Duk da cewa wasu na ganin wannan rikicin tsakanin Algeria da Mali ba zai daɗe ba, ana fargabar rikicin zai jawo taɓarɓarewar tsaro a yankin.
A watan Janairun 2024, shugannin mulkin sojin Mali sun janye daga yarjejeniyar tsagaita wuta da mayaƙan Tuareg ta Algiers Accord da aka yi a shekarar 2015, wanda ya dawo da rikicin ƴanbindiga a ƙasar da wasu ƴanbindiga.










