Rasha da Ukraine na zargin juna kan karya yarjejeniyar tsagaita wuta

Wani gida da hari ya fada wa da wata mace da namiji

Asalin hoton, Reuters

Lokacin karatu: Minti 3

Ukraine da Rasha sun zargi juna da saba yarjejeniyar dakatar da bude wuta ta sa'a 30- ta lokacin bikin Easter – wadda Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ayyana a shekaran jiya Asabar, wadda yanzu ta kawo karshe.

Rahotanni sun ce an samu tsagaitawar hare-hare a yakin a wasu yankunan.

A zargin da suke yi wa juna na saba yarjejeniyar dakatar da bude wutar ta sa'a 30, wadda Shugaba Putin na Rasha ya ayyana bisa radin kansa – albarkacin bikin Easter kamar yadda ya ce, Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya ce dakarun Rasha sun saba yarjejeniyar kusan sau 3000 ranar Lahadi.

Haka ita ma ma'aikatar tsaron Rasha ta ce ta kare wasu hare-hare da Ukraine ta kai mata, tana mai zargin Kyiv da kaddamar da daruruwan hare-hare na kananan jiragen yaki marassa matuka da kuma makamai masu linzami.

Sai dai duka wadannan zarge-zarge da kasashen biyu ke wa juna BBC ba ta iya tantance sahihancinsu ba.

Sabanin tsagaita wutar ta Putin ta sa'a 30 Shugaba Zelensky ya nemi ta kwana 30 ne, yana mai cewa kin yarda da hakan na tabbatar da cewa Rasha na son tsawaita yakin ne.

A wata hira da BBC 'yar majalisar dokokin Ukraine -Yulia Sirko – wadda ta ziyarci fagen daga, ta bayyana halin da ake ciki a babban birnin kasar, Kyiv a ranar Easter - Lahadi;

''Ba mu samu hare-hare ta sama ba jiya a Kyiv ko Kyiv Oblast, to amma kuma abin takaicin babu dakatar da bude wuta a fagen daga ko kuma a yankunan da ke kusa da fagen daga.''

Ta ce: ''Sojojinmu sun ce akwai kusan sabawa 3000 da suka lissafa ranar Easter – jiya Lahadi daga bangaren Rasha.''

Shi kuwa Shugaba Trump na Amurka – wanda ke kokarin ganin an daina yakin ya ce akwai fatan kasashen biyu za su cimma matsaya a wannan makon – amma kuma bai bayar da wani cikakken bayan a kan yadda za a kai ga hakan ba.

A ranar 24 ga watan Fabarairu ne na 2022 Rasha ta kaddamar da cikakken kutse a Ukraine, kuma a yanzu tana rike da kusan kashi 20 cikin dari na yankin kasar Ukraine din, ciki har da kudancin yankin Crimea da ta mamaye a 2014.

An yi kiyasin cewa zuwa yanzu dubban mutane yawancinsu sojoji ko dai sun rasu ko kuma sun jikkata a sanadiyyar yakin, a bangarorin biyu tun daga shekara ta 20222.

A watan da ya gabata na Maris, Rasha ta fitar da wasu tarin sharudda – a martaninta na yarjejeniyar dakatar da yakin – wadda Amurka da Ukraine suka amince da ita.