Ana tattaunawa kan rikicin Rasha da Ukraine a Saudiyya

Asalin hoton, Global Images Ukraine via Getty Images
- Marubuci, Frank Gardner
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Security Correspondent
- Aiko rahoto daga, Riyadh
- Lokacin karatu: Minti 4
Masu shiga tsakani na Amurka na tattaunawa da Ukraine a Riyadh, babban birnin Saudiyya, hakazalika za su yi wata tattaunawar a gefe guda da Rasha a yau litinin.
Burin Amurka shi ne samar da tsagaita wuta cikin gaggawa a yaƙin da ake yi a Ukraine, daga bisani kuma a samar da yarjejeniyar zaman lafiya.
Ko waɗannan tattaunawar a Riyadh za su samar da abin da mutane da yawa ke fata?
''Ina ji kamar Putin na son zaman lafiya,'' a cewar wakilin Trump na musamman Steve Witkoff, inda ya ƙara da cewa: ''Ina tunanin za ku ga ci gaba sosai a Saudiyya a yau Litinin''.
Sai da kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya rage ƙwarin gwiwar da ake da shi '' har yanzu muna farkon wannan batu ne,'' ya shaida wa kafar talabijin ta Rasha.
Kyiv ta fuskanci ɗaya daga cikin hare-hare mafi muni daga jirage marasa matuƙa na Rasha a daren Asabar wanda ya kai ga mutuwar mutane uku, ciki har da yarinya ƴar shekara biyar.
''Ya kamata mu matsa wa Putin ya bayar da umurnin hana kai waɗannan hare-hare,'' In ji shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a jawabinsa na yammacin Lahadi. ''Wanda ya yi sanadiyyar soma yaƙin nan wajibi ne ya kawo ƙarshensa.''
A gefe guda kuma, da alamu Kremlin ba ta cikin gaggawa na amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta, ganin cewa Vladimir Putin na ta ƙara sharuɗɗa kafin amincewa da yarjejeniyar na kwanaki 30 da Amurka ta gabatar kuma Kyiv ta riga ta amince.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A Riyadh, tattaunawa tsakanin Amurka da Ukraine ta soma ne a daren Lahadi cikin sirri a cikin ɗaya daga cikin gine-gine masu ƙasaita na Saudiyya inda Ministan tsaron Ukraine Rustem Umerov yake jagorantar tawagar Ukraine.
Ya ce waɗannan tattaunawa ne da za su mayar da hankali kan yadda za a kare kayyyakin samar da makamashi da ma wasu muhimman ababen more rayuwa.
Bayan ganawar, Umerov ya bayyana tattaunawar a matsayin wanda ake samun 'nasara' a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, kuma ya ce suna ƙoƙarin cika burin Zelensky na cimma ''zaman lafiya mai ɗorewa kuma wanda akayi bisa adalci.''
Ana kuma tattauna batun fitar da hatsi, inda ake ganin Rasha na ƙoƙarin farfaɗo da yarjejeniyar da zai bai wa Ukraine damar ci gaba da safarar kayan hatsi daga filin jirgin ruwanta ba tare da an kai mata wani hari ba wanda za a yi musayarsa da sassauci kan takunkumai.
Dukannin ɓangarorin wato Rasha da Ukraine sun kai manyan hare-hare da suka lalata ababen more rayuwa ga junansu.
Moscow ta ƙuduri aniyar jefa alummar Ukraine cikin sanyi da duhu ta hanyar kai hari kan kayyayakin samar da wutar lantarki, yayin da Kyiv ke ci gaba da samun nasara wajen kai hare hare da makamai masu linzami masi cin dogon zango kan kayyaykin samar da man fetir wanda ke da muhimmanci ga yaƙin.
Shugaba Trump na son a kawo ƙarshen yaƙin cikin gaggawa, wanda shi ne yaƙi mafi muni a Turai tun 1945, kuma wanda ya kai ga mutuwa da kamawa da jikkatawa da kuma ɓacewar dubun dubatar mutane a duka ɓangarorin.
Shugabannin Ukraine - waɗanda har yanzu ba su farfaɗo daga sa-in-sar da aka samu a ofishin shugaban Amurka a watan da ya gabata ba- na ƙoƙarin gaske wajen tabbatarwa Amurka cewa ba ita ce ke kawo cikas ga samun zaman lafiya ba.
A lokacin da Amurka ta ƙaddamar da yarjejeniyar tsagaita wuta a sama da ruwa da kuma ƙasa na kwanaki 30 a yayin tattaunawa da akayi a Jeddah cikin wannan watan, Ukraine ta yi gaggawar amincewa da matakan.
A cewar sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, a lokacin zaɓi ya rage ga Rasha.
Sai dai duk da rashin nasarar da Amurka ta yi wajen sa Moscow ta amince da tsagaita wutar, gwamnatin Trump ba ta wani matsa wa Rasha ta amince, musamman ma a fili. Haƙiƙanin gaskiya, kamar akasin hakan take yi.
A wani hira a ƙarshen mako da ɗanjarida mai goyon bayan Trump Tucker Carlson, mutumin da ke jagorantar ƙoƙarin Amurka na samar da tsagaita wuta Steve Witkoff, da alama matsayarsa ta sha ban-ban da ta Turai.
Ya ce Ukraine '' ba ƙasar gaske bace'', kuma an tunzura Rasha ne, hakazalika Putin mutum ne mai cika alƙawari da za a iya amincewa da shi.
Witkoff, wanda a baya mai harkar gine-gine da gidaje ne a birnin Newyork, kuma abokin buga wasan golf da Donald Trump, ya kuma yi watsi da ƙoƙarin Firaminsta Sir Keir Starmer na haɗa dakarun soji da zasu taimaka wajen kare yarjejeniyar zaman lafiya da za a yi a Ukraine.











