Me ya sa Putin yake jan ƙafa dangane da yaƙin Ukraine?

Asalin hoton, Reuters
Gabanin tattaunawa ta waya da aka yi a ranar Talata, Donald Trump ya kambama hirar tasa da shugaban Rasha Vladimir Putin.
Sai dai sakamakon tattaunawar ya nuna kamar babu wani abin kambamawa a ciki.
Shugaban Rasha ya bai wa shugaban Amurka iya abin da zai iya nuna cewa ya samar da cigaba wajen ƙoƙarin samar da zaman lafiya a Ukraine ba tare da nuna alamar ko fadar Kremlin ta yi wasa da hankalinsa ba ne.
Trump na iya nuna alwashin da Putin ya sha na dakatar da kai hare-hare kan kayyayakin samar da makamashi na Ukraine na tsawon kwana 30.
Idan har da gaske aka yi hakan, ba shakka zai kawo wa al'umma ɗan wani sauƙi.
Sai dai ko kusa bai yi ga cikakkiya kuma tsagaita wuta mara sharaɗi da Amurka ta so daga wurin Rasha ba.
"Mummunar yaƙi'' da Trump ya yi ikirarin zai iya kawo ƙarshen shi, har yanzu ana ci gaba da yi.
Kuma Putin, mutumin da kotun sauraron manyan laifuka na duniya ICC ya zarga da aikata laifin yaƙi, a yanzu an taimaka mishi ya dawo kololuwar fagen siyasar duniya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kafar yaɗa labaran Rasha ta ruwaito cewa tattaunawar ta waya da shugabannin biyu suka yi ya shafe fiye da sa'oi biyu.
Rahoton da fadar Kremlin ta fitar ma kan wayar na da tsawon kalmoli 500.
Rahoton ya bayyana cewa sun tattauna akan wasu abubuwan ma, a cewar su har da kan wasan Ice Hockey, irin bayanin da zai ƙayatar da ƴan Rasha.
Bayan shafe shekara 3 a matsayin saniyar ware ga ƙasashen yamma, da kuma alaƙa mara daɗi tun kafin nan, Rasha ta dawo ta na mu'amula kai tsaye da gwamnatin Amurka.
Har magana kan zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya da kuma 'tsaro a faɗin duniya' shugabannin biyu ke tattaunawa.
Da alama fadar Kremlin na fama wajen yarda cewa an samu irin wannan sauyi ko cigaba.
Gabanin tattaunawar ta waya, wasu na ta tunanin ko Donald Trump zai matsawa Rasha.
Duk da dai fiye da mako guda kenan ana gani ƙarara cewa Rasha na jan baya wajen batun tsagaita wutar.
Sai dai babu alamar Trump zai tsawatarwa Putin kamar irin wanda ya yi wa shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a ofishin shugaban Amurka makonni biyu da suka wuce.
Bayanai daga ƙasashen biyu na nuna babu abin da ya sauya.
Rasha na ta nanata cewa tana son zaman lafiya.
Amma maimakon ta ajiye makamanta, tana ta bayar da sharuɗɗan yadda za a sanya ido kan yarjejeniyar tsagaita wutar da ba a ma riga an samar ba.
A gefe guda kuma tana ta kara sharuɗɗai da ke da nufin karya ma Kyiv ƙarfin tirjiya.
Wata buƙata da suka gabatar ita ce dole ne a dakatar da shigo da makamai da samar da bayanan sirri ga Ukraine daga ƙasashe ƙawayenta.
Ga ƴan Ukraine kuwa, sauƙin abin kawai shi ne zuwa yanzu Amurka ba ta amince da duk wani sharaɗi ba.
Za kuma su iya nuna tattaunawar ta waya a matsayin ƙarin alama da ke nuna Rasha ba ta da sha'awar kawo ƙarshen mamayarta.
Sai dai duk waɗannan maganganun ba za su kawo wa Ukraine wani sauƙin a zo-a-gani ba game da wahalhalunta.
Ga diflomasiyyar Amurka ma, ga alama zai zama abin takaici.
Amma ga Rasha, zai zama kamar rana ce mai kyau gare su, rana irin wadda ba su taɓa tunaninta ba kafin Trump ya dawo fadar White House.











