Buƙatu huɗu da gwamnonin Arewa suka miƙa wa Tinubu

...
Lokacin karatu: Minti 4

Gwamnonin jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya a ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, sun miƙa buƙatu huɗu ga shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu, a yayin ziyarar da suka kai masa ranar Laraba.

Zulum wanda ya gabatar da jawabi a madadin sauran gwamnonin yankin, ya gode wa shugaba Tinubu bisa ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Arewa maso Gabas da kuma ɗaukar nauyin shirye-shiryen da suka shafi yaƙi da ta'addanci, musamman a dazuka da yankunan da ke da wahalar shiga.

Ya bayyana cewa yankin Arewa maso Gabas na da manyan ƙalubale na tsaro da muhalli saboda girman shi da kuma kasancewar akwai dazuka da hamada da tsaunuka da koguna da ba a iya sarrafawa yadda ya kamata.

Wannan, in ji shi, ya haifar da barazana da kuma ƙara tsananta matsalar tsaro.

Duk da haka, gwamnonin sun nuna goyon bayansu ga shirin shugaban ƙasa na buƙatar jami'an tsaro su canza salo tare da amfani da fasahar zamani wajen murƙushe ta'addanci da bunƙasa harkokin noma yayin da kuma suka yaba da matakan Tinubu wajen yaƙi da ambaliya da fari .

A cikin buƙatun da suka miƙa, akwai muhimman fannoni guda biyar da suka fi maida hankali a kai:

Ci gaba da ayyukan soji a muhimman yankuna

Gwamnonin sun nemi shugaban Tinubu ya tabbatar da ci gaba da gagarumin ayyukan soji a yankunan da ke fama da ta'addanci kamar gaɓar tekun Chadi da Dajin Madama da tsaunukan Mandara da Sambisa.

Akwai kuma wasu dazukan a jihohin Bauchi da Taraba da Yobe da suka haɗa da Mansur da Yelwa da Futuk da yankunan Kolmani da Karin Lamido da sauran wurare da 'yan ta'adda ke fakewa.

Sambisa da ke jihar Borno na daga cikin dazukan da suka yi ƙaurin suna tun bayan fara rikicin Boko Haram.

Dajin ya zama tamkar mafaka ga mayaƙan Boko Haram, inda suke fakewa suna shiryawa da kuma kitsa munanan hare-hare kan ƙauyuka da biranen arewa maso gabas.

Duk da cewa gwamnati sha yin ikirarin cin galabar Boko Haram, amma har yanzu mazauna yankin ba sa iya gudanar da ayyukan noma ko kamun kifi a yankin.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu da gwamnonin jihohin Arewa maso gabashin ƙasar a ranar Laraba 3 ga watan Satumba 2025

Asalin hoton, STATE HOUSE

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Tinubu da gwamnonin jihohin Arewa maso gabashin ƙasar

Tallafin kuɗi ga rundunar haɗin gwiwa ta MNJTF

Gwamnonin sun kuma buƙaci da a samar da ƙarin kuɗi ga rundunar haɗin gwiwar ƙasashen tafkin Chadi (MNJTF) domin gudanar da ayyukan tsaro a yankin Tumbus na Tafkin Chadi, inda aka daɗe ana samun matsalar 'yan bindiga da masu safarar makamai.

MNJTF ita ce runduna ce ta sojoji daga ƙasashen Najeriya, Nijar, Chadi, Kamaru da kuma Benin, wadda aka ɗora wa aikin kawar da mayaƙan ƙungiyoyin da suka ɗauki makami a yankin tafkin Chadi, musamman rikicin Boko Haram.

Kammala ayyukan hanyoyi da gina sababbi

Gwamnonin sun kuma bukaci shugaban ƙasar ya kammala aikin manyan hanyoyin mota da kuma gina muhimman hanyoyin da ke haɗa jihohin Arewa maso Gabas da sauran sassan ƙasar.

Ciki har da hanya daga Kano zuwa Maiduguri da layin dogo daga Port Harcourt da Jos da Bauchi da Maiduguri, da kuma hanyoyin da suka haɗa Bama da Mubi da Yola, Damaturu da Geidam da Bauchi da Ningi da Nasaru da Babaldo da Maiduguri – Monguno da Baga da dai sauransu.

Ɗaya daga cikin waɗannan manyan hanyoyi da aikinsu ya daɗe yana tafiyar hawainiya shi ne babban hanyar Kano zuwa Maiduguri, wanda aka ba da shi tun a shekara ta 2007.

Cigaba da aikin haƙo mai a Arewa maso Gabas

Gwamnonin sun buƙaci gwamnatin tarayya ta ci gaba da aikin hako mai a Kolmani da Tafkin Chadi, waɗanda aka haƙo mai tun a baya amma aka dakatar da aikin.

Sun ce hakan zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin yankin da ƙasar baki ɗaya.

A watan Nuwambar 2022 ne, tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya ƙaddamar da aikin fara hako man a yankin Kolmani da ke iyakar jihohin Bauchi da Gombe.

A ƙarshe, gwamnonin sun tabbatar wa shugaba Tinubu cewa za su ci gaba da mara masa baya wajen aiwatar da manufofin gwamnatinsa domin tabbatar da kyakkyawan mulki da ingantaccen ci gaba ga al'ummar Najeriya.