Wane tasiri kame da kisan shugabannin ƴan ta da ƙayar baya zai yi ga matsalar tsaron Najeriya?

Ansaru

Asalin hoton, ONSA

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

A ranar Alhamis ne sojojin Jamhuriyar Nijar suka sanar da samun nasarar kashe wani jagoran Boko Haram mai suna Ibrahim Mahamadu wanda aka fi sani da Bakura, a yankin Tafkin Chadi, inda ƙasar ke iyaka da Najeriya da Chadi da Kamaru.

A wata sanarwa da sojojin suka fitar a ranar Alhamis, sun ce an kashe Bakura ne yayin wani aikin soji a wani tsibiri a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin Nijar a makon da ya gabata.

Bakura dai ya jagoranci wani ɓangare na ƙungiyar Boko Haram wadda ke biyayya ga tsohon shugaban ƙungiyar, Abubakar Shekau, inda ya ƙi shiga reshen abokan hamayyar su na ISWAP inda ya koma tsibirin da ke gefen Nijar na tafkin tare da mayaƙansa.

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan an kama wasu mutum shida, ciki har da ɗan autan wanda ya assasa Boko Haram, Muhammad Yusuf mai suna Musulim Muhammad Yusuf.

Ko da yake jami'an tsaron ƙasashen da suke fama da rikicin na Boko Haram sun ce suna ci gaba da ƙara ƙaimi domin daƙile matsalar, tuni wasu suka fara murnar ganin ana kamawa ko kashe jagororin.

Sai dai kuma a wani ɓangaren, wasu na ganin an daɗe ana ruwa ƙasa na shanyewa wajen kama jagororin ko kashe su, amma sai lamarin ya sake kunno kai bayan wani lokaci.

Wannan ya sa wasu ke tambayar shin yaushe za a daddale tare da kawo ƙarshen lamarin? Shin kame da kashe manyan jagororin zai daƙile matsalar tsaron da Najeriya ta shafe sama da shekara 10 tana fama da ita?

'Akwai sauran aiki'

A game da nasarar da ake ganin an samu, Audu Bulama Bukarti, mai bincike kan harkokin tsaro a ƙasashen Afirka ya ce duk da cewa nasara ce, amma yana ganin akwai sauran aiki a gaba.

"Kamawa ko kashe shugabannin ƙungiyoyin ƴanta'adda ba zai ɗurkusar ko tsayar da su baki ɗaya ba, amma hakan zai taimaka wajen janyo wa ƙungiyoyin tawaya da ma yayyafa wa matsalar ruwa."

Sai dai ya ce wannan sauƙi da yake ganin taƙaitacce ne, "matuƙar gwamnati ba ta ɗauki matakan da suka dace ba wajen ci gaba da yaƙin har sai an kai ƙarshe baki ɗaya."

Bulama ya yi misali da kashe shugaban Boko Haram na farko Muhammad Yusuf, wanda kashe shi ƙara dama lamura ya yi.

"A loacin da aka kashe Muhammad Yusuf a watan Yulin 2009, sai gwamnati da jami'an tsaro suka ɗauka sun gama da ƙungiyar, amma saboda ba su ɗauki matakan ci gaba a yaƙin ba, sai ƴan ƙungiyar suka ja da baya suka sake shiri, suka naɗa sabon shugaba Abubakar Shekau wanda ya zo ya fi rashin tausayi."

Me hakan ke nufi?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shin kamen ko kisan na da wani tasiri? A nan ne Bulama ya ce alama ce da ke nuna cewa gwamnati da jami'an tsaro suna yin abin da ya kamata.

A cewarsa, "irin wannan nasarar ko dai a Najeriya ko a Chadi ko Nijar na nufin jami'an tsaronmu sun fara samun nasarar tattara bayanan sirri tare da amfani da shi," in ji shi.

Ya ƙara da cewa, "Na biyu yana da tasiri wajen sanyaya gwiwar ƴan ƙungiyar domin idan aka kama shugaba da rai, kowane daga cikin mabiyansa zai shiga tsoro da fargabar cewa shi ma ana bibiyarsa kuma za a iya kama shi."

Bukarti ya ce a halin da ake ciki yanzu bayanan sirri na da matuƙar muhimmanci domin samun nasara, sai dai ya ce akwai waɗanda za a fi murna idan an kama su ko an kashe su.

"Kama shugabannin Ansaru abu ne na farin ciki, amma abin da ya fi tayar da hankali a yanzu shi ne matsalar ƴanbindiga a arewa ta yamma, don haka kamata ya yi gwamnati ta yi amfani da irin dabarun wannan wajen kamawa ko kashe Bello Turji da Ado Aleiro da Dogo Giɗe da Kachalla Ɗan Sadiya da sauran manyan shugabannin su."

Masanin harkokin tsaron ya ce idan ma gwamnatin taraya za ta shiga yarjejeniya ko za ta buɗe ƙofar tuba ga masu tayar da ƙayar baya, "to babbar hanyar samun wannan nasarar ita ce kashewa ko kama manyan shugabannin su. Amma kiran ƙungiyar a lokacin da take ganin tana da ƙarfi akwai wahala, amma idan ka nuna mata an fi ƙarfinta, za su fi amsawa."

Tsarin shugabancin masu tayar da ƙayar baya

A duk lokacin da aka kashe ko aka kama wani shugaban masu tayar da ƙayar baya, akan samu wanda zai maye gurbinsa, lamarin da Bulama ya ce suna yi ne ba tare da wani tsari mai kyau ba.

"Tsarin shugabanci na da muhimmanci sosai a ƙungiyoyi irin su, kuma duk da cewa ƙungiyoyi ne da ba aiki mai kyau suke yi ba, suna da tsari mai kyau kuma za ka ga shugaba ne mai cikakken iko wanda idan ya bayar da umarni dole kowa ya bi."

Ya ce suna da dokokin ciki gida masu kyau da kuma tsarin hukunta waɗanda suka karya dokokin.

"Sai dai ba su da tsari tartibi na wanda zai maye gurbin wani shugaba idan ya mutu. Abin da ke jawo wannan shi ne za ka ga shugaban yana so ya zama mai cikakken iko shi ya sa ba sa son naɗa mataimaki."

Amma Bulama ya ce a cikin manyan yaran shugaban ne ƙananan ciki suke lura da waɗanda suka fi ƙarfi da kusanci da shi shugaban, sai su riƙa yi musu biyayya.

Amma Bulama ya ce wannan na iya zama nasara ga jami'an tsaro domin idan babu shugaban, rikici kan shiga tsakanin manyan yaran game da wanda zai maye gurbin shugaba.

Abubuwan da ya kamata gwamnati ta yi

Barista Bulama ya ce akwai wasu matakai da suka kamata gwamnati ta ɗauka a gaba:

  • Kama mage ba yanka ta ba ne: Kamen ko kashe shugaban ba zai zama ƙarshen yaƙin ba. An yi irin wannan kuskuren a baya kan kashe Muhammad Yusuf
  • Sanarwar ta wucin gadi ce: Idan aka yi sakaci ba a ci gaba da musu wuta-wuta ba, za su sake taruwa su sake shiri su dawo da ƙarfi.
  • Bayanan sirri: Wannan dama ce ta tattara bayanan sirri ta hanyar bibiyar wayoyoyinsu da iyalansu da garuruwansu.

A ƙarshe Bulama ya ce tunda an fahimci cewa dabarar ta yi aiki, "ya kamata a riƙa inganta dabarun saboda su ma za su riƙa canja salo. Ya kamata wannan nasarar ta zaburar da jami'an tsaro su ƙara ƙaimi wajen bin ƴan ƙungiyoyin a yanzu da suke cikin ruɗu da rashin tabbas na rashin shugabanci."