Mu na son sanin dalilin dakatar da aikin hako mai a Kolmani - Majalisa

Asalin hoton, OTHER
Majalisar wakilan Najeriya ta nemi gwamnatin tarayya ta yi mata karin bayani a kan dalilan da suka janyo dakatar da ci gaba da aikin hako mai a yankin arewacin kasar.
A watan Nuwambar 2022 ne, tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya ƙaddamar da aikin fara hako man a yankin Kolmani da ke iyakar jihohin Bauchi da Gombe.
Sai dai shekaru biyu, bayan fara wannan aiki, ‘yan majalisar sun ce aikin ya tsaya.
Hon. Inuwa Garba, ɗan majalisar tarayyar ne daga jihar Gombe da ya gabatar da kudurin, ya shaida wa BBC cewa a gaban jama’a da dama tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi alkwarin ci gaba da wannan aiki hasali ma shi kansa shugaban kasa na yanzu ya na wajen, to amma abin mamaki shi ne kullum aikin komawa baya yake.
Ya ce,“A yanzu kamfanonin da ke aikin hako man sai tattara kayansu suke suna barin wajen, kamar dai kokari ake a yi watsi da wannan aiki.”
“ Ni da kai na gudanar da bincike, don na je wajen na duba kuma muna magana da mutanenmu ni fa dan yankin ne domin daga jihar Gombe na ke, kuma wannan man da ake tonowa a tsakanin jiharmu ta Gombe da Bauchi wajen yake.” in ji shi.
Hon. Inuwa Garba, ya ce wannan tono man da aka ce za a yi duk dan yankin hankalinsa a tashe ya ke domin dakatar da aikin ko tafiyar hawainiyar da aikin ke yi baya musu dadi.
Ya ce,”Wannan dalili ne ya sa na gabatar da kuduri domin a ceto mu daga cikin halin da muke ciki ganin yadda ita kanta Najeriyar ke tafiya.”
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dan majalisar wakilan ya ce tunanin da mutane ke yi ko matsalar tsaro ce ta sa aka dakatar da wannan aiki, ba haka bane, domin batun matsalar tsaro gwamnonin yankin ko jihohi biyu na Gombe da Bauchi, sun hada kai da sarakunan gargajiyar yankin da ma ‘yan majalisun yankin don kawar da matsalar, kuma Alhamdulillahi babu wannan matsala, don haka ba rashin tsaro ne ya sa aka dakatar da aikin tono mai a wajen ba.
“Yanzu wannan waje na nan ana ta noma da kiwo babu wata matsala, mu dai kawai mun ga kamfanonin da ke wannan aiki suna ta kwashe kayansu suna tafiya aiki ya tsaya ai dole hankalin duk wani dan yankin ya tashi.” In ji dan majalisar tarayyar.
Hon. Inuwa Garba, ya ce,”Mu abin da muke so yanzu a yi shi ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinibu, ya tuna da alkawarin da ya yi a gaban mutane cewa lallai zai tabbatar da an ci gaba da wannan aiki na tono mai, don haka muna so yanzu mu ga an ci gaba da wannan aiki tare da sanya kudin da zai isa a yi aikin don muma muna so mu ga an yi wani abin a zo a gani a bangaren arewa.”














