Mene ne alfanun shan madara ga lafiya?

Wata mata na shan madara.

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

A ƴan kwanakin nan, an cika gidajen talabijin da tallukan alfanun da shan madara yake da shi.

Yawanci ana faɗa cikin tallukan cewa, "biscuits ɗin mu na ɗauke da ƙarin madara. Idan ka yi amfani da madararmu ko kayanmu na dangin madara, ƴaƴanku za su zama zakaru."

Indiya ce ƙasar da ta fi samar da madara a duniya.

A cewar alƙaluman gwamnati, ƙasar ta samar da tan sama da miliyan 230 a shekarar 2022 zuwa 2023.

Abu ne da aka yi imani da shi a Indiya cewa madara na da muhimmanci ga jikin ɗan'adam da kuma lafiyarsa.

Mutane da dama na da ɗabi'ar shan kofin madara mai ɗumi kafin kwanciya barci.

Wane irin sinadarai madara ke da shi?

Wane adadin madara ne ya kamata a sha a kowace rana? Sannan waye ya kamata ya guji madara?

Ku biyo mu domin jin amsar waɗannan tambayoyi.

Kwai da nama.

Asalin hoton, Getty Images

Shin akwai buƙatar masu cin nama su sha madara?

Wani ƙwararre kan lafiyar yara da kuma abinci mai gina jiki, Arun Kumar, ya ce madara na da sinadarin calcium da kuma protein mai yawa a cikinsa.

Don haka idan mutum ya ci dangin abinci irin nama da kifi da kuma kwai, to ba wajibi ne sai ya sha madara ba.

Dakta Arun Kumar ya ce, "Mutanen zamanin da, ba su samun abinci masu ɗauke da sinadaran gina jiki''.

Ya ci gaba da cewa watakila wannan ne ya sa mutane suka fara kiwon dabbobi masu samar da madara.

Al'adar shan madara ta ƙaru saboda ba a iya dogaro da kayan noma wajen samun abinci mai gina jiki ba.

''Ɗabi'ar shan madara ta ƙaru a tsakanin mutane a tsawon shekaru dubu-goma da suka wuce', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa a yanzu abinci ya inganta matuƙa. ''Idan muka ci abinci yadda ya kamata, to ba lallai mu buƙaci madara ba."

Waɗanne sinadarai ne ke cikin madara?

Madarar shanu ita ce wadda aka fi sha a ko'ina, sai madarar buffalo.

Giram 100 na madarar shanu na ɗauke da sinadarin calories 67, yayin da giram 100 na madarar buffalo (jakin dawa) ke ɗauke da calories 117.

Wannan shi ne dalilin da ya sa shan madarar jakin dawa akai -akai ke ƙara ƙiba.

A cewar Arun Kumar, "giram 100 na madarar shanu na ɗauke da milligram 120 na sinadarin calcium, yayin da irin wannan adadi na madarar jakin dawa ke ɗauke da giram 210.

A ɗaya gefen, giram 100 na madarar shanu na ɗauke da giram 4.1 na sinadarin fat yayin da na jakin dawa ke da giram 6.5 na sinadarin fat.

Yarinya riƙe da kofin madara tana sha.

Wa ya kamata ya sha madara?

Dakta Arun Kumar, ya ce a baya, jariran da ke shan nono suna da abin da ke ƙarya sikarin da ke cikin madara, sai dai da zarar sun fara sabawa da shan madara a kowace rana, za a samu sauyi jikin ɗan'adam.

Don haka, kada manyan su sha madara.

Ya ce, "Madara na alaƙa da abin da ke narkewa. Wasu mutane kan sha lita ɗaya na madara ba tare da ya narke ba, sai dai ga wasu, ko da rabin kofi na madara zai janyo sinadarin gas, ciwon kirji da amai da gudawa."

Ya ƙara da cewa, " Tun da madara na ɗauke da sinadaran gina jiki, ya kamata a bai wa yara, sai dai zai sa su yi ƙiba''

Don haka, kada a bai wa yara madara kaɗai. Wasu yaran ba sa cin abinci saboda madara.

Yarinya na shan madara

Asalin hoton, Getty Images

Adadin madarar da ya kamata a sha a kowace rana

Shekaru kaɗan da suka wuce, "Madara ita ce abin da ɗan wasan cricket na Indiya Mahendra Singh Dhoni ya fi sha''.

''Bayan shan madara, yana iya buga wasa cikin sauki."

Batun cewa yana shan lita huɗu na madara a kowace rana ya karaɗe shafukan intanet cikin sauri.

Sai dai Dhoni ya mayar da martani cewa lita ɗaya na madara yake sha a kowace rana.

Ƙwararriya kan abinci mai gina jiki Dharini Krishnan ta ce, "Ba kowa ne ke shan ko da lita ɗaya na madara a rana ba.

Dhoni na iya shan litan madara saboda yana yawan motsa jiki, sai dai mutum mai lafiya zai iya shan mili-lita 400 na madara ko kuma giram 400 na yogurt."

Ya kamata a sha madarar da aka sarrafa?

Wani mutum na tatsar nonon shanu.

Asalin hoton, Getty Images

Dakta Shravan Kumar ya ce, "yana da kyau a sha madara mai nauyin ml 400 a kowace rana, ml 200 da safe da ml 200 da yamma, sai dai a guji shan madara da suga, saboda madara na ƙunshe da sinadarin calories.

Ya ce, "Idan mutum yana da ciwon olsa, to su guji shan madara. Idan mutum na fama da jinkiri wajen narkewar abinci, su guji shan madara."

Likitan ya ƙara da cewa, "Idan kana son sauya shan madara zuwa wani abu, to ka zaɓi wasu na'uka na abinci masu kyau.