Sai da haƙorana tara suka zube lokacin ɗaukar fim ɗin Squid Game – Darakta

Asalin hoton, Netflix
- Marubuci, Jean Mackenzie
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Seoul correspondent
- Lokacin karatu: Minti 5
Lokacin da na tambayi daraktan wasan kwaikwayon 'Squid Game' (da ke cikin cikin fina-finan Koriya) game da rahotannin da ke cewa sakamakon gajiya da wahala da ya fuskanta a lokacin ɗaukar kashin farko na fim ɗin ta sa har ya rasa haƙora shida, cikin hanzari ya gyara min da cewa, ''ba shida ba ne sun kai takwas zuwa tara,'' sannan ya yi dariya.
Hwang Dong-hyuk na magana da ni ne a lokacin da yake shirin ɗaukar kashi na biyu na shirin mai matuƙar farin jini da ka haska a dandalin kallon fina-finai da shirye-shirye na Netflix, wanda a ciki ɗaruruwan yara suka riƙa shiga gasar wasannin kasada daban-daban domin samun kyautar kuɗi, ta hanyar jefa rayuwarsu cikin kasadar a mutu ko a yi rai.
Amma kashi na biyu ba kamar na bayan ba ne. A baya ya taɓa rantsewa ba zai sake yin wani makamancinsa ba.
Saboda irin wahalar da ya sha a na baya, na tambaye shi ko me ya sauya tunaninsa.
Sai ya ce ''Kuɗi'', ba tare da wata-wata ba.
“Duk da cewa kashin farko na fim ɗin ya samu karɓuwa a duniya, amma magana ta gaskiya ban samu kuɗi sosai ba,'' kamar yadda ya bayyana min. ''Don haka yin kashi na biyu zai sa na mayar da kuɗina har ma na samu riba''.
“Sannan kuma wani ƙarin dalilin, shi ne ban kammala labarin a kashin farko ba'', in ji shi.
Kashin farko na fim ɗin mai dogon zango ya kasance wanda ya fi kowane shahara a dandalin Netflix zuwa yanzu, wanda kuma ya fito da fina-finan Koriya ta Kudu a dandalin. Yadda aka yi sharhin fim ɗin ya yi matuƙar ƙayatar da masu kallo a faɗin duniya.
To amma kasancewa an kashe kusan duka 'yan wasan da suka fito a fim ɗin tun a kashin farko, dole ne Hwang ya fara tun daga farko, tare da sabbin fuskoki da sabbin wasanni, kuma a wannan karon masu kallon za su zaƙu su ga abin da sabon shirin zai zo da shi.
“Gajiya da wahalar da nake sha a yanzu ta ma fi ta baya,” in ji shi.
Shekara uku bayan haska kashin farko da fim ɗin, Hwang ba ya tsammanin duniya za ta gyaru a wannan lokaci.
Ya bayyana dalilai kamar yaƙe-yaken da ake yi a yanzu da batun sauyin yanayi da ƙaruwar giɓi tsakanin masu kuɗi da talakawa.
Saɓani ba ya aukuwa tsakanin masu kuɗi da talakawa, sai dai tsakanin al'umomi daban-daban, ko tsakanin jinsi ko 'yan siyasa, kamar yadda ya bayyana.
“An shata sabbin iyakoki. Muna zamanin tsakanin mu da su ne. Wane ne kan daidai, wane ne kan kuskure.?”

Asalin hoton, Netflix
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yayin da na kewaya wurin da suke ɗaukar fim ɗin, wanda aka yi matuƙar ƙawatawa, na fahimci abin da daraktan ke nufi kan sabbin abubuwan da zai zo da su a wannan karon.
A wannan sabon shirin, wanda ya yi nasara a baya, Gi-hun, ya sake shiga wasannin da nufin sake dawowa domin shiga sabon kashin domin fafatawa
Lee Jung-jae, wanda ya taka rawar jarumi a kashin farko, ya ce "ya zaƙu, kuma a shirye yake yana da ƙwarin gwiwa” fiye da baya.
ɗakin kwanan, wanda a baya masu gasar ke kwana a cikinsa, an raba shi zuwa kashi biyu.
ɓangare na farko an yi masa kwalliya da alamar X da aka yi wa launin ja, ɗayan kuma da zagayen shuɗi.
Yanzu, bayan kowane wasa, dole ne ’yan wasan su zaɓi ɓangare, ya danganta da ko suna son fita daga gasar da wuri domin su huta, ko kuma su ci gaba da wasa, da sanin cewa kowane daga cikinsu daga ƙarshe zai mutu, in ban da guda. Wani matakin da mafi rinjaye za su ɗauka.
Wannan an faɗa min zai ƙara samar da ɓangaranci wanda kuma shi ne zai haifar da faɗa tsakanin 'yan wasan.
Yana daga cikin manufar Hwang ya bayyana ƙaruwar hatsarin samun matsaloli masu alaƙa da ɓangaranci.
Lamarin da ke tilasta wa mutane ɗaukar ɓangare, wanda yake ganin a matsayin abin da ke ƙara rura wutar rikici.
Duk da yadda fim ɗin 'Squid Game' ya ɗauki hankalin mutane musamman yadda aka bayyana wa mutane labarin, amma wasu sun kasa kallonsa saboda irin razani ko sosa rai da yake da shi.
Amma a lokacin zantawarmu da Hwang, ya ce duka waɗannan abubuwa na taɓa rai da ke cikin im ɗin baya a yanzu duka an cire su. Shi mutum ne mai tunani tare da damuwa game da yadda mutane ke ji, sannan yana aiki ne da abin da mutane ke so.

Asalin hoton, Getty Images
Hwang ya shafe shekara 10 kafin kammala fim ɗin 'Squid Game', lamarin da ya sa ya ci bashi mai yawa domin tallafa wa iyalinsa, kafin Netflix su biya shi.
Sun biya shi kafin alƙalami, lamarin da ya sa ya kasa samun dala miliyan 650 da aka ƙiyasta fim ɗin ya samar a dandalin.
Wannan ya ƙara fito da yadda masu shirya fina-finai a Koriya ta Kudu ke kaffa-kaffa ga dandalin nuna fina-finan.
Cikin shekarun da suka gabata, dandalin Netflix ya bazama kasuwar fina-finan Koriya ta Kudu, tare da zuba jarin biliyoyin kuɗaɗe, lamarin da ya ƙara fito da masana'antar shirya fina-finan ƙasar a duniya, amma duk da haka har yanzu wasu masu shirya fina-finan ba su iya sakin jiki da dandalin.
Suna zargin dandalin da tilasta musu sarayar da hakkin mallakar a lokacin da suka sanya hannu a kwantiragin, kuma hakan ya sa ba sa iya riƙe haƙƙin mallakar fina-finansu.
Wannan kuma wata matsala ce ta duniya.
Matsalar na da sarƙaƙiya a Koriya ta Kudu, in ji masu shirya fina-finai, saboda tsoffin dokokin haƙƙin mallaka, domin yakar tsarin bai ɗaya.
A wannan kakar, taurari, da marubuta da daraktoci da masu shirya fina-finai sun haɗa kai domin yaƙar tsarin bai ɗaya.
“A Koriya, zama daraktan fim, muƙami ne kawai, ba hanya ce ta samun kuɗi ba,” kamar yadda mataimakin ƙungiyar daraktocin ƙasar Guild, Oh Ki-hwan, ya bayyanawa masu kallo a wani biki a birnin Seoul.
Wasu daga cikin abokansa, sun ce suna aikin wucin gadi a rumbunan ajiyar kayyaki ko direbobin tasi.
Park Hae-young wata matashiyar marubuciya ne, a lokacin da Netflix ya sayi labarinta, ta ce ta ji dadin yadda 'Fasaharta ta samu karɓuwa', sannan duniya ta santa.
“Na kwashe tsawon rayuwata ina rubuce-rubuce, don haka samun shiga takara da manyan marubuta a duniya abun alfahari ne kuma abin a ayaba ne,” in ji ta.
“Na kwashe shekara biyar ina rubuta labarin dramar cike da fatan cewa idan fim ɗin ya yi nasara, zai taimaki rayuwata a gaba, saboda zan samu wani kaso na ribar da aka samu, inda ba don wannan ba wahala kawai na yi''.
Ita da sauran marubuta na yunƙurin ganin gwamnatin Koriya ta Kudu ta sauya dokokin haƙƙin mallaka domin tilkasta wa kamfanonin nuna fina-finai su riƙa raba ribar da su.
Cikin wata sanarwa gwamnatin ƙasar ta shaida wa BBC cewa yayin da take la'akari da sauya dokokin haƙƙin mallakar domin samun ribar, ya rage wa masana'antar shirya fina-finan ta gyara matsalar. To sai dai kamfanin Netflix ya ƙi cewqa komai game da buƙatar tsokaci da muka yi daga gare shi.
Za a fitar da kashi na biyu na Squid Game a dandalin Netflix ranar 26 ga watan Disamban 2024.











