Ƙasashen da ke samun ruwan shansu daga teku

    • Marubuci, Navin Singh Khadka
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Environment correspondent, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 6

Shekaru da dama da suka wuce, Muhammad Yaqoob Baloch da iyalansa sun kusan ƙaurace wa gidansu dake Keti Bandar, a kudancin Pakistan, saboda koguna da rijiyoyi sun bushe.

Yana da matuƙar wahala a samu ruwan sha mai kyau a yankin kuma amfanin gona sau da yawa yana lalacewa.

"Mazauna Delhi da Mumbai da China suna zuwa sayen shinkafa da alkama da kayan gona a wajenmu," in ji Mr. Baloch, wanda shi ma manomi ne.

"Amma sama da hekta dubu 50 na gonarmu ya zama maras amfani inda ba ma iya noma," in ji shi.

Mutane da yawa sun bar gonarsu ta kakanninsu, kuma Mr. Baloch shi ma yana shirin bin sawu har sai gwamnati ta buɗe wata masana'antar tace gishiri daga ruwan Teku da kuma fara samar da ruwa mai kyau daga Tekun Larabawa.

Yanzu da yawa daga cikin waɗanda suka rage a yankin suna samun riba ta hanyar kiwon ƙwari a cikin hanyoyin da ake janyo ruwa domin noman rani, yayin da suke ci gaba da noma duk abin da za su iya.

Pakistan na cikin ƙasashen duniya da suke ƙara amfani da fasahar tace gishiri daga ruwan teku saboda dumamar yanayi na duniya da ke sa ruwa mai tsafta yayi wahala.

A baya ana yin wannan aiki ne kawai a ƙasashe masu arziki da ke yankin Gabas ta Tsakiya da suke da hamada, amma ɗumamar yanayi ta duniya ta kawo canji.

Yanzu kusan ƙasashe huɗu cikin biyar suna samar da ruwansu daga teku da ake tacewa don sha da sauran buƙatu, in ji cibiyar gano sirrikan ruwa ta duniya.(GWI), kuma yawan ƙasashen na ƙaruwa.

A ƙasashen Kuwait da Oman da Saudi Arabia, fiye da kashi 80 cikin 100 na ruwan da ake amfani da shi yana fitowa ne daga tekun da aka tace ko kuma daga ruwan ƙarƙashin ƙasa mai gishiri kaɗan.

A lokacin harin da aka kai kan wuraren nukiliyar Iran da Isra'ila da Amurka suka yi kwanan nan, jami'an Qatar sun nuna damuwa game da yiwuwar gurɓata ruwan ƙasashen yankin Gulf saboda yanzu shi ne babban tushen samar da ruwa ga Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa da Kuwait.

Me ya sa babu wadataccen ruwa mai tsafta?

Babbar matsalar shi ne kusan kashi biyu bisa uku na doron duniya na lulluɓe ne da ruwa.

Amma Majalisar Dinkin Duniya ta ce daga cikin wannan ruwa, kashi 0.5% kaɗai ne ruwa mai tsafta da za a iya amfani da shi – kuma ma wannan na raguwa cikin sauri saboda ɗumamar yanayi da fari.

Hukumar kula da tattalin ruwa ta duniya a rahotonta na 2023 ta yi gargaɗi cewa nan da shekarar 2030 ana iya samun ragin isar ruwa har kashi 40 yayin da ake sa ran yawan mutane a duniya zai kai biliyan 9.7 nan da shekarar 2050.

Cin hanci da rashin kyakkyawan gudanarwa na albarkatun ruwa ya taimaka wajen tsananta ƙarancin ruwa a ƙasashe da dama.

Tunda tekuna suna ɗauke da fiye da kashi 95% na ruwan duniya, wasu na ganin ruwan teku na iya zama mafita, ko da yake a halin yanzu amfani da ruwan teku kaɗan ne a duniya baki ɗaya

Faɗaɗar tace ruwa a duniya

Bincike ya nuna cewa masana'antar tace gishiri daga ruwan teku ta ƙaru sosai, inda aka gina fiye da wurare 20,000 a duniya – kusan ninki biyu na adadin da ake da shi shekaru 10 da suka wuce.

"Kasuwar tace gishiri daga ruwan teku za ta ƙara girma cikin shekaru biyar masu zuwa, musamman a yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka da Asiya ta Pasifik, da kuma wasu ƙasashe a Turai," in ji Estelle Brachlianoff, shugabar kamfanin Veolia – ɗaya daga cikin manyan kamfanonin ruwa na duniya masu ƙwarewa a wannan fanni.

Bayanan da GWI ta tattara sun nuna cewa kusan ƙasashe 160 a duniya yanzu suna da injinan tace gishiri daga ruwan teku.

A matsakaici, kashi 60 na ruwan da ake samar wa ana amfani da shi ne a matsayin ruwan sha na jama'a.

"Tace gishiri daga ruwan teku na taimaka wa ƙasashe da dama wajen magance matsanancin ƙarancin ruwa," in ji Rachael McDonnell, mataimakiyar darakta a cibiyar kula da ruwa ta duniya (IWMI), wata cibiyar bincike da ke mai da hankali kan tsaron ruwa.

"Kodayake tace ruwan teku ba ita ce magani gaba ɗaya ga dukkan yankunan da fari ke damun su ba, amma tana taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa ƙasashe su ƙara samun tabbacin ruwa a lokacin fari da ƙaruwar buƙatar ruwa."

Cibiyar GWI ta ƙiyasta cewa wannan fanni na ƙaruwa da sama da kashi 10 a duk shekara.

Ta ce cikin shekara 15 da suka gabata, samar da ruwan sha ta hanyar tace gishiri daga ruwan teku ya ƙaru sosai a ƙasashe fiye da 60 a dukkan yankunan duniya.

Rahoton ya nuna cewa yayin da da dama daga cikin waɗannan ƙasashe suka samu ƙarin ninki biyu, uku ko huɗu (misali, Singapore ta samu karin kashi 467), wasu kuma sun samu ƙaruwa mai ban mamaki har sau 10 zuwa 50.

Ƙasar Saudiyya ce ke samar da ruwa ta teku da aka tsarkake aka tace gishirin fiye da kowacce, wato lita biliyan 13 a rana – wanda ya yi daidai da cike tafkunan wasan iyo na Olympic guda 5,200 – in ji GWI.

Bangladesh da India da Pakistan ba wai suna amfani da fasahar tace gishiri daga ruwan teku ba ne kaɗai har ma da tsarkake gurɓatattun ruwa ko na rijiya ko na koguna.

Afghanistan kuma tana amfani da ita don tsarkake ruwa da kuma wasu dalilai daban.

Ta yaya ake tace gishiri daga ruwan teku?

Ana iya tace gishiri daga ruwan taku ta hanyoyi guda biyu.

Hanya ta farko ita ce wadda ba ta buƙatar makamashi sosai, inda ake amfani da ƙarfi wurin matse ruwan ta cikin abin tacewa

Hanya ta biyu ita ce tace gishiri daga ruwa ta hanyar amfani da zafi (thermal desalination).

Wannan hanyar tana ɗumama ruwan teku har sai turiri ya tashi ya daskare sannan a tattara turirin da ya huce a matsayin ruwan sha mai tsafta.

Sauƙin samu

Tace ruwan gishiri daga ruwan teku a baya fasaha ce mai tsada, amma sabbin makamashin da ke akwai da kuma ingantacciyar fasaha sun rage farashinsa a 'yan shekarun nan.

Masana sun ce farashin tace gishiri daga ruwan teku ya ragu har zuwa kashi 90 tun daga shekarar 1970.

Binciken IWMI ya nuna cewa haɗa tace gishiri daga ruwan teku da na'urar hasken rana zai iya sa ya fi araha nan da shekarar 2040 a yankunan bakin teku da dama.

Sai dai, a cewar kamfanin Veolia, babban injin tace ruwa teku da ke samar da lita miliyan 500 a rana yana buƙatar jarin kusan dala miliyan 500.

Haka kuma, jigilar ruwan da aka tace zuwa yankunan ƙasa masu bushewa na ƙara tsada.

Ƙalubalen da ke tattare da tace ruwan teku

Ɗaya daga cikin manyan ƙalubale a aikin tace ruwan teku shi ne yadda za a zubar da yawan gishirin da aka fitar bayan an cire ruwan sha.

Zubar da shi cikin teku na ƙara gishiri da zafin ruwa, yana iya lalata rayuwar halittun ruwa har ma ya haifar da "matattun yankuna" a wurin da ake zubarwa.

UNEP ta ce, a yawancin hanyoyin tace ruwa, lita 1 na ruwan sha na haifar da kusan lita 1.5 na gishiri mai sinadaran chlorine da tagulla da aka fitar, wanda idan ba a rage gubarsa ba, zai iya lalata bakin teku da halittun ruwa.