Waiwaye: Hatsarin jirgi na Abuja zuwa Kaduna da kashe 'yan fashi 50 a jihar Neja

Lokacin karatu: Minti 5

Kamar kowane mako, wannan maƙala ta yi waiwaye kan wasu muhimman abubuwan da suka faru a makon da muka yi bankwana da shi.

Gwamnatin Najeriya ta dakatar da jigilar jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna

Jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna

Asalin hoton, Social Media

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta Najeriya NRC ta dakatar da jigilar fasinja a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna har sai abin da hali ya yi.

Shugaban hukumar ta NRC, Kayode Opeifa, shi ne ya sanar da hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, sa'o'i bayan jirgin ya goce daga kan titinsa kuma ya tuntsire ɗauke da fasinoji a cikinsa daga Abuja zuwa Kaduna.

Opeifa ya ce wasu ma'aikatan hukumar tare da hukumar binciken sufuri ta Najeriya (NSIB) da sauran hukumomin da abin ya shafa a halin yanzu suna nan a wurin da jirgin ƙasan ya tuntsure suna gudanar da bincike.

Ya yi watsi da iƙirarin cewa jiragen ba su da kyau kuma ya ce an fara mayar da kuɗaɗen tikiti ga duk fasinjojin da ke cikin jirgin.

Shugaban na NRC ya kuma karɓi wasu fasinjojin da ke cikin jirgin a tashar Asham da kuma tashar jirgin ƙasa ta Idu.

Jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna

Asalin hoton, NRC

Sojoji da DSS sun kashe ƴanbindiga 50 a jihar Neja

Sojojin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Sojojin Najeriya tare da jami'an tsaron farin kaya (DSS) sun kashe aƙalla ƴanbindiga 50, sannan suka kuɓutar da wasu daga cikin mutanen ake garkuwa da su a ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja.

Jami'an tsaron sun ce sun yi arangama da kusan ƴan bindiga 300 ɗauke da makamai a ranar Talata bayan sun yi ƙoƙarin kai hari a wani ƙauye da kuma kai farmaki a sansanin DSS.

Shugaban ƙaramar hukumar Mariga, Abbas Adamu, ya tabbatar wa BBC faruwar arangamar, yaa mai cewa an kashe ƴan bindigan da dama.

"Gaskiya ne, shekaran jiya ne muka samu rahoton fitowar 'yan bindiga daga jihar Zamfara suna tunkarar yankunanmu daga Katonkoro zuwa Kumbashi har zuwa Gulbin Boka."

"Amma kafin su isa, mun sanar da jami'an tsaro da muke da su, ciki har da sojoji da 'yansanda, da DSS, waɗanda suka yi iyakar ƙoƙarinsu wajen tare su domin hana su kai farmaki wuraren da suka saba."

Amma kuma ya ce ƴan bindigan sun samu hanyar shiga Gulbin Boka inda suka yi garkuwa da mutane da dama.

Kwalara ta kashe mutum bakwai a jihar Zamfara

Wasu mutane kwance a gadon asibiti

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A tsakiyar makon da ya gabata bayanai suka nuna cewa cutar amai da gudawa ko kuma kwalara ta barke a wasu kananan hukumomin jihar Zamfara inda zuwa yanzu ta hallaka aƙalla mutum bakwai a ƙananan hukumomin Gumi da Bukkuyum.

Hukumomin sun ce kusan mutum 200 cutar ta kwantar a asibitin kananan hukumomin biyu, tare da gargadin cewa adadin na iya karuwa.

Hon Sulaiman Abubakar Gumi wanda shi ne danmajalisar tarayya da ke wakiltar Gumi/Bukkuyum kuma shugaban kwamitin hukumar raya yankin arewa maso yammaci a majalisar wakilai, ta Najeriya ya sheda wa BBC cewa tun daga ranar 10 ga watan nan na Agusta, 2025 matsalar ta fara inda yanzu take ta karuwa.

Ya ce zuwa yanzu a Bukkuyum kadai an kwantar da mutum wajen 157, tare da fargabar yawan zai iya karuwa da kuma fargabar rasa wasu mutanen a sakamakon cutar.

Danmajalisar ya ce a Birnin Waje inda ba a kai rahoton bullar cutar ba ma da wuri har an yi mace-mace, inda aka rasa mutum bakwai.

Zanga-zangar malaman jami'a kan rashin kuɗi da yanayin aiki

Mambobin ƙungiyar ASUU a Najeriya

Asalin hoton, Channels TV

A ranar Talata ne malaman jami'a a Najeriya sun gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya a ranar Talata, suna neman gwamnati ta cika yarjejeniyar da suka ƙulla tun 2009.

Zanga-zangar ta jawo tsaiko a wasu jami'o'i inda ɗalibai suka rasa kulawar karatu.

Malaman da ke ƙarƙashin ƙungiyar ASUU sun koka da cewa suna wahala da kuma koyarwa cikin yunwa, da rashin kayan aiki a ɗakunan karatu da dakunan gwaji tare da fama da matsalolin rayuwa da aiki.

Shugaban ASUU, Farfesa Christopher Piwuna, ya ce idan gwamnati ba ta ɗauki mataki ba, za a iya shiga wani yajin aiki na dindindin.

Ƙungiyar na buƙatar ƙarin kuɗaɗen tallafi ga jami'o'i da inganta yanayin aiki da 'yancin gudanarwa da kuma 'yancin yin bincike.

ASUU ta sha shiga yajin aiki tun 2012 saboda gazawar gwamnati wajen cika yarjejeniyar 2009, kuma ta ce gwamnati tana zaɓar abin da ta ga dama kawai daga cikin alƙawuran.

Shekaru biyu kenan da ƙungiyar ta yi yajin aikin ƙasa na ƙarshe.

Mambobin ASUU sun haɗa da malamai daga jami'o'in tarayya da na jihohi a faɗin ƙasar.

NDLEA ta gano yadda ake saka ƙwaya a jakunkunan matafiya a filin jirgi na Kano

NDLEA

Asalin hoton, NDLEA

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA ta ce ta cika hannu da wani ƙasurgumin mai fataucin miyagun ƙwayoyi da wasu mutum biyar da take zargi da harƙallar saka miyagun ƙwayoyi a jakunkunan matafiya a filin jirgin saman Aminu Kano.

Hukumar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakin hukumar na ƙasa, Femi Babafemi ya fitar.

Sanarwar ta ce wani mai suna Mohammed Ali Abubakar mai shekara 55 da aka fi sani da Bello Karama da wasu mutum biyar ne suke harƙallar a filin jirgin, inda suke haɗa hannu da wasu ma'aikata wajen harƙallar.

Wannan na zuwa ne bayan samun labarin kama wata mai suna Maryam Hussain Abdullahi a Saudiyya da zargin fataucin miyagun ƙwayoyi a daidai lokacin da take aikin Umara.

Da yake bayyana yadda aka banƙado harƙallar ta hanyar, wadda ke jefa mutanen da ba su ji ba su gani cikin masifa, ya ce ƴan'uwan wasu ƴan ƙasar uku ne suka kawo ƙorafi ga hukumar NDLEA cewa an kama ƴan'uwansu a Saudiyya, inda cikin gaggawa hukumar ta ƙaddamar da bincike.

Zargin badaƙalar kuɗi a fadar gwamnatin Kano

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

Asalin hoton, KNSG

Labarin badaƙalar rashawa da karkatar da kuɗaɗen gudanar da ayyukan gwamnati da aka zargi wani jami'in gwamnatin jihar Kano da aikatawa ya tayar da ƙura, lamarin da ya ja hankulin mutane da dama har ake ta tsokaci tare da tafka muhawara musamman a kafofin sadarwa na zamani.

Ana dai zargin darakta-janar na gudanar da tsare-tsaren ofishin gwamna watau Abdullahi Ibrahim-Rogo ne da karkatar da wasu kuɗaɗe daga lalitar gwamnati da suka kai naira biliyan shida da rabi.

Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta tabbatar wa BBC cewa tana binciken wannan jami'in da ke aiki a fadar gwamnatin jihar Kano.

A binciken da ICPC da EFCC ke yi, an zargi babban jami'in gwamnatin da amfani da wasu kamfanoni wajen karkatar da kuɗaɗe daga lalitar gwamnati tare da biyan wasu kuɗaɗen kwangilolin da ba a aiwatar ba a tsakanin watan Nuwamban 2023 da Fabrailun 2025.