NDLEA ta gano yadda ake saka ƙwaya a jakunkunan matafiya a filin jirgin Kano

Asalin hoton, Femi Babafem
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA ta ce ta cika hannu da wani ƙasurgumin mai fataucin miyagun ƙwayoyi da wasu mutum biyar da take zargi da harƙallar saka miyagun ƙwayoyi a jakunkunan matafiya a filin jirgin saman Aminu Kano.
Hukumar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakin hukumar na ƙasa, Femi Babafemi ya fitar.
Sanarwar ta ce wani mai suna Mohammed Ali Abubakar mai shekara 55 da aka fi sani da Bello Karama da wasu mutum biyar ne suke harƙallar a filin jirgin, inda suke haɗa hannu da wasu ma'aikata wajen harƙallar.
Wannan na zuwa ne bayan samun labarin kama wata mai suna Maryam Hussain Abdullahi a Saudiyya da zargin fataucin miyagun ƙwayoyi a daidai lokacin da take aikin Umara.
Da yake bayyana yadda aka banƙado harƙallar ta hanyar, wadda ke jefa mutanen da ba su ji, ba su gani cikin masifa, ya ce ƴan'uwan wasu ƴan ƙasar guda uku ne suka kawo ƙorafi ga hukumar NDLEA cewa an kama ƴan'uwansu a Saudiyya, inda cikin gaggawa hukumar ta ƙaddamar da bincike.
"Ƴan Najeriya da aka kama a Saudiyya su ne: Maryam Hussain Abdullahi da Abdullahi Bahijja Aminu da Abulhamid Sadiq waɗanda suka hau jirgin Ethiopian Airline mai lamba ET940, wanda ya bar Kano a ranar 6 ga watan Agustan bana zuwa Jeddah, sai aka ƙara wasu jakunkuna da sunan su da ke ɗauke da miyagun ƙwayoyi."
Ya ce bayan mutanen sun je karɓar jakunkunansu ne sai a tsare su bisa zargin fatauzin miyagun ƙwayoyi zuwa ƙasar.
"Bincikenmu ya gano Ali Abubakar Mohammed wanda ake kira da Bello Karama ne ya kai jakunkunan a ranar 6 ga watan, wadda ita ce ranar da waɗanda ake zargib suka yi tafiya''.
''Amma sai shi ya hau jirgin Egypt Air zuwa Saudiya, amma ya saka jakunkunan a jirgin Ethiopian da waɗanda suka hau."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Femi ya ce wasu ma'aikatan kamfanin Skyway Aviation Handling Company ne suka shigar da jakunkunan da ke ɗauke da ƙwayoyin, sannan suka rubuta sunan waɗanda aka zargi ba tare da saninsu ba, wanda hakan ya sa hukumomi a Saudiyya suka tsare mutanen.
"Amma bayan bincike, mun tabbatar da cewa waɗanda ake zargi ba su da laifin komai, kawai gungun wau mutane ne suka shirya harƙallar a filin jirgin Aminu Kano."
Hukumar ta ce tuni mutum shida sun shiga hannu, sannan akwai huɗu da an riga an gabatar da su a kotu.
Waɗanda ya ce an gabatar a kotu su ne: Ali Abubakar Mohammed (aka Bello Karama) da Abdulbasit Adamu da Murtala Akande Olalekan da Celestina Emmanuel Yayock.
"Sun tabbatar da hannunsu a aukuwar lamarin, inda Ali ya tabbatar da zuwa jakunkunan. Celestina ta ce ita ta shigar da jakunkuna biyu a kan naira 100,000, wani mai suna Jazuli Kabir ya ce shi ya shigar da jakunkuna biyu a kan naira 100,000."
Ya ce hukumar na aiki da hukumomin Saudiyya wajen wanke waɗanda ake zargi, "Shugabanmu zai tafi Saudiyya domin gabatar da sakamakon binciken da muka yi domin ganin an saka tare da wanke Maryam Hussain Abdullahi da sauran mutanen guda biyu."
Hukumar ta nanata cewa a shirye take ta ci gaba da yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a ƙasar, inda ya ƙara da cewa "babu sani ba sabo" a aikinsu.











