Kwalara ta kashe mutum bakwai a jihar Zamfara

Asalin hoton, Getty
A Najeriya, bayanai na nuna cewa cutar kwalara ta barke a wasu kananan hukumomin jihar Zamfara inda zuwa yanzu ta hallaka aƙalla mutum bakwai a ƙananan hukumomin Gumi da Bukkuyum.
Hukumomin sun ce kusan mutum 200 cutar ta kwantar a asibitin kananan hukumomin biyu, tare da gargadin cewa adadin na iya karuwa.
Hon Sulaiman Abubakar Gumi wanda shi ne danmajalisar tarayya da ke wakiltar Gumi/Bukkuyum kuma shugaban kwamitin hukumar raya yankin arewa maso yammaci a majalisar wakilai, ta Najeriya ya sheda wa BBC cewa tun daga ranar 10 ga watan nan na Agusta, 2025 matsalar ta fara inda yanzu take ta karuwa.
Ya ce zuwa yanzu a Bukkuyum kadai an kwantar da mutum wajen 157, tare da fargabar yawan zai iya karuwa da kuma fargabar rasa wasu mutanen a sakamakon cutar.
Danmajalisar ya ce a Birnin Waje inda ba a kai rahoton bullar cutar ba ma da wuri har an yi mace-mace, inda aka rasa mutum bakwai zuwa yanzu.
Hon Gumi ya ce, a karamar hukumarsa ta Gumi ma a Unguwar Gamji wajen mutum 24 aka kwantar a asibiti.
Ya kara da cewa a kasar gaftu akwai wata kungiya da ba ta gwamnati ba - kungiyar likitoci masu bayar da agaji ta duniya , MSF, suna taimakawa.
Hon Abubakar ya yi gargadin cewa muddin ba a dauki matakin gaggawa ba abin zai iya zama annoba.
Bayanai dai sun nuna cewa kusan duk shekara akan fuskanci barkewar wannan cuta ta kwalara a jihar ta Zamfara a daidai irin wannan lokaci na damuna, wanda hakan ya sa ake ganin rashin daukar wani kwakkwaran mataki na hana hakan.
Dangane da hakan ne sai danmajalisar ya ce a wannan karon matsalar ta taso ne a sanadiyyar 'yan gudun hijira da ke zaune a kasar Bukkuyum.
''Suna zaune ne a makaranta a tsakiyar gari, to matsalar da nake ji, masansu ta rufta saboda ruwan sama, sai ya zama cewa babu wajen zuwa makewayi sai nan cikin gari magudanar ruwa inda suke tsugunawa cikin dare su biya bukatarsu, ina ganin daga nan ne matsalar ta fara yaduwa,'' in ji shi.
Dangane da tallafin gwamnati, danmajalisar ya ce har dai zuwa lokacin da yake yi wa BBC bayani babu wani tallafi da gwamnati ta kai sai dai wanda mutanen gari da kuma su suke yi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kan matakan da ya kamata a dauka domin magance wannan matsala da ke addabar jihar kusan a duk shekara ya ce, ya kamat hukumomi su rika daukar matakan da suka hada da fadakar da jama'a kan su guji yin bahaya barkatai musamman ma a lokacin damuwa, don kaucewa gurbatar ruwa da kayan abinci da jama'a ke amfani da su, da dagwalon bahaya.
Daman tun a baya kungiyar likitoci ta duniya masu bayar da agaji - MSF, ta nuna damuwa tare da ankararwa game da yawan mutanen da ke kamuwa da cutar ta kwalara a jihar ta Zamfara, inda ta ce mutum 1,500 ne suka kamu daga tsakiyar watan Yuni da ya wuce zuwa farkon watan nan na Agusta.
Babban jami'in kula da lafiya na kungiyar a Najeriya, Dr David Kizito, ne ya bayyana fargabar a wata sanarwa da ya fitar a Birnion Kebbi - babban birnin jihar ta Zamfara a kwanakin nan nan.
Ya ce ana fama da barkewqar cutar yayin da jihar ke fama da matsalar tsaro da gudun hijira inda jama'a ba sa samun ruwan sha mai tsafta da kuma tsaftar muhalli - lamarin da ya ta'azzara a sanadiyyar ruwan sama.
Jami'in ya ce cutar ta kwalara wadda ta zama annoba a Najeriya tsawon gomman shekaru, takan barke kusan duk shekara lokacin damuwa inda take tsananta a tsakanin watan Afirilu da Oktoba.
Dakta Kizito ya ce ambaliya a wannan lokaci na damuna na gurbata ruwan da jama'a ke amfani da shi, lamarin da ya ce yana kara ta'azzara barkewar cutar ta kwalara a yankunan da ke fama da matsalar tsafta.











