Hotunan hatsarin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna

Asalin hoton, BBC Hausa
Da safiyar yau Talata ne aka samu wani hatsarin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna a yankin arewacin Najeriya.

Asalin hoton, BBC Hausa
Jirgin ƙasan ɗauke da fasinja da ya taso daga Abuja babban birnin Najeriya zuwa Kaduna ya goce daga kan layinsa ne, lamarin da ya sa wani ɓangare nasa ya faɗi jim kaɗan bayan ya bar Abuja.

Asalin hoton, BBC Hausa
Lamarin ya jefa fargaba a tsakanin fasinjoji da ke cikin jirgin da ma ƴan'uwa da abokan arziki.

Asalin hoton, BBC Hausa
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Asham da ke hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Asalin hoton, BBC Hausa
Har yanzu ba a san abin da ya jawo saukar jirgin daga kan layin dogo ba, kuma babu tabbacin ko an samu waɗanda suka jikkata.

Asalin hoton, BBC Hausa
Tuni dai hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta Najeriya NRC ta sanar dakatar da jigilar jiragen ƙasa tsakanin Abuja zuwa Kaduna har sai lokacin da aka gyara hanyar.

Asalin hoton, BBC Hausa
Shugaban hukumar sufurin jiragen ƙasa ta ƙasar, NRC, Kayode Opeifa, ne ya sanar da hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, sa'o'i bayan faruwar lamarin.

Asalin hoton, BBC Hausa
Opeifa ya ce wasu ma'aikatan hukumar tare da hukumar binciken sufuri ta Najeriya (NSIB) da sauran hukumomin da abin ya shafa, a halin yanzu suna nan a wurin da jirgin ƙasa ya tuntsure suna gudanar da bincike.

Asalin hoton, BBC Hausa
Wasu ƴan ƙasar sun alaƙanta hatsarin da rashin kyawu da ingancin jiragen ƙasan.

Asalin hoton, BBC Hausa
To sai dai shugaban hukumar sufurin jiragen ƙasar ya yi watsi da iƙirarin.

Asalin hoton, BBC Hausa
Shugaban na NRC ya kuma karɓi wasu fasinjojin da ke cikin jirgin a tashar Asham da kuma tashar jirgin ƙasa ta Idu.

Asalin hoton, BBC Hausa
Tuni dai shugaban hukumar sufurin jiragen ƙasan ya ce an fara mayar wa fasinjojin da ke cikin jirgin kuɗaɗen tikitinsu

Asalin hoton, BBC Hausa











