Abin da muka sani kan zargin badaƙalar kuɗi a fadar gwamnatin Kano

Asalin hoton, Sanusi Bature D-Tofa
Labarin badaƙalar rashawa da karkatar da kuɗaɗen gudanar da ayyukan gwamnati da aka zargi wani jami'in gwamnatin jihar Kano da aikatawa ya tayar da ƙura, lamarin da ya ja hankulin mutane da dama har ake ta tsokaci tare da tafka muhawara musamman a kafofin sadarwa na zamani.
Ana dai zargin darakta-janar na gudanar da tsare-tsaren ofishin gwamna watau Abdullahi Ibrahim-Rogo ne da karkatar da wasu kuɗaɗe daga lalitar gwamnati da suka kai naira biliyan shida da rabi.
Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta tabbatar wa BBC cewa tana binciken wannan jami'in da ke aiki a fadar gwamnatin jihar Kano.
Wannan sabuwar dambarwar ta ja hankali matuƙa ganin a kwanakin baya ne kwamishinan sufuri na jihar, Ibrahim Ali Namadi ya ajiye aikinsa bisa zarginsa da belin fitaccen dilar miyagun ƙwayoyi a jihar bayan rahoton wani kwamiti da gwamnatin jihar ta kafa kan bincikenhannun jami'in gwamnati.
Zarge-zargen cin hanci da rashawa na cikin abubuwan da aka yi amfani da su wajen yaƙi da gwamnatin Kano da ta gabata, musamman bidiyon dala da ake zargin tsohon gwamna Ganduje da wasu suke tunanin ya yi tasiri matuƙa. Duk da cewa Gandujen ya sha musanta zargin.
Wannan ya sa wasu suke ganin samun zarge-zarge irin wannan a gwamnatin Abba Gida Gida zai iya sanyaya gwiwar wasu daga cikin waɗanda suka dage wajen ganin nasarar gwamnatin.
Badaƙalar da ta kunno kai

Asalin hoton, Kano State Government
Tun da farko, jaridar Daily Nigerian ta intanet mai zaman kanta ce ta ruwaito cewa hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa na Najeriya watau EFCC da ICPC suna binciken badaƙalar naira biliyan 6.5 da ake zargin an karkatar a ofishin darakta-janar na tsare-tsare a ofishin gwamna, Abdullahi Ibrahim-Rogo.
A binciken da ICPC da EFCC ke yi, an zargi babban jami'in gwamnatin da amfani da wasu kamfanoni wajen karkatar da kuɗaɗe daga lalitar gwamnati tare da biyan wasu kuɗaɗen kwangilolin da ba a aiwatar ba a tsakanin watan Nuwamban 2023 da Fabrailun 2025.
Har yanzu dai hukumomin na yaƙi da cin hanci da rashawa na ci gaba da bincike kan lamarin, kamar yadda gwamnatin jihar itama ta tabbatar a wata sanarwa, inda ta ce ba ta da burin saka baki a binciken da ake gudanarwa.
Martanin gwamnatin Kano
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A nata ɓangaren, Gwamnatin jihar Kano, ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta kare darakta-janar ɗinta, inda ta ce ofishin wanda ake zargin, watau Abdullahi Rogo ne ke kula da manyan ayyuka da suka haɗa da jigilar baƙi, masauki, walwala, da kuma tsara tafiye-tafiyen gwamna a cikin gida da wajen Najeriya.
A wata sanarwar da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar, ya ce da cewa ofishin ne ke da alhakin samar da kayan aiki da buƙatun jigila da manyan baƙi kamar Shugaban Ƙasa, Ministoci, jami'an ƙasashen waje, da sauran baƙi na diflomasiyya da ke zuwa Kano a hukumance.
A sanarwar, gwamnati ta bayyana cewa ba ta da shakku kan gaskiya da amincin Abdullahi Ibrahim Rogo, sannan ta ce ai ba kanta farau ba, inda ta ce "Gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta ci gaba da zama mai kishin gaskiya, ingantacciyar tafiyar da kudi, bayyana gaskiya, da rashin yarda da cin hanci da rashawa, ba tare da ta yarda mutuncin jami'anta ya zube a hannun makirci na siyasa daga wasu marasa kishin ƙasa ba."
Sai dai gwamnatin ta zargi wasu waɗanda da ta kira ƴan adawa da ke ƙoƙarin ɓata mata suna, sannan ta bayyana wasu badaƙalolin da ta ce gwamnatin baya ta aikata, waɗanda a cewarta mutanen jihar ba za su manta ba.











