Kisa bakwai da gangan masu ta da hankali a arewacin Najeriya

Asalin hoton, KANO POLICE COMMAND/FACEBOOK
Al'ummar wasu sassan arewacin Najeriya sun shiga tashin hankali da ruɗani a 'yan makonnin nan, sakamakon samun ƙaruwar rahotannin kisan ganganci, waɗanda a mafi yawan lokuta ma makusantan mamatan ne ake zargi.
Kashe-kashen da hukumomin tsaro ke ba da rahotannin an aikata cikin wasu jihohin arewa kamar Kano da Bauchi da kuma Jigawa, na ƙara jefa alamar tambaya a zukatan al'umma cewa: 'shin me yake faruwa ne?'
A wannan rahoto, mun duba wasu kashe-kashen gilla masu tayar da hankali da suka faru cikin wata ɗaya a waɗannan jihohi.
Kisan angon da ya ɗimauta Kano
Matasan unguwar dai sun tunzura, inda suka yi gungu-gungu da safiyar ranar talata 6 ga watan Mayu, suna juyayin abin da ya faru, kafin zuwan 'yan sanda, waɗanda suka tabbatar lamarin bai daɗa ƙazancewa ba.
An ɗaura auren zumuncin ne ranar Lahadi 27 ga watan Afrilun 2025 kamar yadda bayanai suka ce, tsakanin marigayin Salisu Idris Ɗan Larai (Mallam) ɗan shekara 30 da amarya Saudat Jibril Adam mai shekara 18.
Gidan rediyon Dala FM Kano ya ruwaito cewa maƙwabta ne suka jiyo hayaniya, abin da ya sa suka kutsa cikin gidan domin kai ɗauki.
An garzaya da Salisu asibiti daga bisani likitoci suka tabbatar cewa angon ya riga mu gidan gaskiya.
Wasu maƙwabtan ma'auratan sun ce sai a asibitin ne ma, da yawa suka lura da cewa cikin raunukan da angon ya ji har da yanka a maƙogwaro.
Kisan magidanci da Asuba
Duk dai a Kano, 'yan sanda sun kuma ba da rahoton kashe wani magidanci ɗan shekara 30, mai suna Shehu Muhammad a unguwar Danbare cikin ƙwaryar birni.
Mai magana da yawun 'yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce mutum biyu ake zargi da auka wa gidan mutumin cikin daren Talata, inda suka fara masa da sara da adda.
Ya ce an kama wani matashi da ake zargi da hannu, Aliyu Umar ɗan shekara 20 kuma an gano makamin da aka yi amfani da shi wajen aikata kisan.
Jaridar Aminiya a intanet ta ruwaito cewa wani abokin kasuwancin marigayin, Haruna Nuhu Hussain, ya ce 'yan fashin sun shiga gidan Shehu Muhammad ne daidai lokacin da suke shirye-shiryen tafiya sallar Asuba.
Ta ce mazauna unguwar ne suka yi kukan-kura suka kama ɗaya daga cikin 'yan fashin, wanda ake zargi shi ne jagoran gungun, daga bisani kuma suka damƙa shi hannun 'yan sanda.

Asalin hoton, KANO STATE POLICE/FACEBOOK
Kashe mahaifi a Gwaram
A ranar Litinin kuma, 5 ga watan Mayun nan, 'yan sanda a jihar Jigawa suka ba da rahoton kama wani matashi ɗan shekara 20 mai suna Muhammad Salisu bayan sun zarge shi da far wa mahaifinsa da adda.
Wata sanarwa da SP Lawan Shiisu Adam ya fitar ta ce lamarin ya faru ne a unguwar Bakin Kasuwa cikin yankin Sara na ƙaramar hukumar Gwaram.
A cewarsu, Mallam Salisu Abubakar, wanda likitoci a wani asibiti da ke Birnin Kudu suka ce ya riga mu gidan gaskiya, magidanci ne mai shekara 57 kuma ya ji raunuka a kafaɗa da wuyansa sannan da ƙirji.
'Yan sanda sun ce an tura batun hannun sashen binciken manyan laifuka na rundunar da ke Dutse don ci gaba da bin diddigi kuma da zarar sun kammala bincike za a gurfanar da wanda ake zargi a kotu.
Kashe tsohon shugaban ƙaramar hukuma

Asalin hoton, NIGERIA POLICE FORCE/FACEBOOK
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ranar Juma'a kuma 2 ga watan Mayu, rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta ba da rahoton kisan da ta ce mai yiwuwa na ganganci ne kan wani tsohon shugaban ƙarama Mallam Isa Muhammad Wabi mai shekara 66.
Ta ce harin na da alaƙa da gungun wasu matasa da suka auka wa dattijon kuma suka yi masa jina-jina a unguwar Fadaman Mada cikin birnin Bauchi.
A cewar 'yan sanda waɗanda suka far wa Mallam Isa Wabi, abokan Abdulgafar Isa Mohd ne, matashi mai shekara 24 kuma ɗan marigayin.
Ta ƙara da cewa cikin tsakar dare ne wani Ahmad Abdulƙadir wanda aka fi sani da suna Abba da Faruk Malami ko Ajebo suka kutsa kai cikin gidan da misalin ƙarfe 3:00 sannan suka ƙulla kashe Isa Wabi, wanda ya ji raunuka a wuyansa.
'Yan sanda sun ce ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi mai suna Ajebo shi ma ya ji raunuka mai yiwuwa saboda ramuwar gayya daga wani da ya fusata, kafin daga bisani likitoci su tabbatar da cikawarsa.
Sun ce suna yi wa Abdulgafar Isa tambayoyi kuma yana ba su haɗin kai da muhimman bayanai

Asalin hoton, BAUCHI STATE POLICE/FACEBOOK
Amaryar da ta rasu a hannun ango
Sai kuma a ranar Asabar 26 ga watan Afrilu ne, wata amarya ta gamu da ajalinta bayan angonta ya tursasa mata mu'amalar aure a ƙauyen Tungo na ƙaramar hukumar Sule Tankarkar, in ji 'yan sanda.
Bayanai sun ce angon ya gayyaci abokansa uku ne Nura Basiru da Muttaƙa Lawan da kuma Hamisu Musa dukkansu 'yan shekara 20 zuwa gidansa su je su riƙe masa amarya don ya biya buƙatarsa ta aure.
Binciken 'yan sanda ya nuna cewa ango ya shiga damuwa bayan shafe mako biyu da aure amma amarya ta ƙi yarda da shi.
Mai magana da yawun 'yan sandan Jigawa, SP Shiisu Lawan Adam ya faɗa wa BBC cewa wadda aka rirriƙe ɗin ta yi ta kururuwa, lamarin da ya ja hankalin maƙwabta da jami'an tsaro, waɗanda suka je suka kai mata ɗauki.
Ya ce bayan kai ta asibiti ne likitoci suka tabbatar musu da cewa abin da ya faru cikin wannan dare ya yi sanadin mutuwarta.
Shiisu Adam ya ce angon wanda ba su bayyana sunansa da na amaryar ba, sun kama shi tare da abokan da suka rirriƙe ta, bisa zargin haɗa baki da aikata kisa.
Jami'in 'yan sandan ya ce a hasashensu amaryar ta ƙi yarda da angon ne saboda mai yiwuwa ba ta son shi, amma aka dage wajen haɗa auren da ya zama ajalinta.
Matar ƙanin da aka bugawa taɓarya
Duk dai a wannan mako cikin jihar Jigawa a ranar Alhamis, 24 ga watan Afrilu 'yan sanda sun sanar da kama wani matashi ɗan shekara 25 mai suna Buhari Sule bisa zargi kashe matar ƙaninsa mai suna Ummi Saleh bayan ya mangare ta da taɓarya.
Sanarwar da mai magana da yawun 'yan sanda SP Shiisu Lawan Adam ya fitar ta ce wanda ake zargin ya kuma buga wa Hauwa Alkassim, 'yar maƙwabcinsu taɓarya, inda ta samu ranuka.
Lamarin dai ya faru ne ranar Laraba a ƙauyen Gunka cikin ƙaramar hukumar Jahun, amma 'yan sanda sun ƙara da cewa ana kyautata zaton wanda ake zargi yana da taɓin hankali.
Matashiyar da ta mutu wajen zubar da ciki
A ranar Alhamis ɗin dai, 'yan sanda a jihar Bauchi suka sanar da kama wasu matasa uku 'yan garin Misau bisa zargin haɗa baki kwartanci da sanadin ɓarin ciki da kuma yiwuwar aikata kisa da gangan.
Sanarwar mai magana da yawun 'yan sandan jihar Bauchi, CSP Ahmed Muhammad Wakili ta yi zargin cewa biyu a cikin waɗanda aka kama Usman Umar da Sallau Ayuba sun ja ra'ayin matashiyar 'yar shekara 18 suka sadu da ita a karo da dama, lamarin ya kai ga ta samu juna biyu.
Bayan sun farga ne, in ji 'yan sanda, sai suka gayyaci wani Abubakar Mohammed mai shekara 35 inda suka yi tayin ba shi ladan kuɗi idan ya yi wa mai juna biyun allura domin zubar da cikin da take ɗauke da shi.

Asalin hoton, BAUCHI STATE POLICE/FACEBOOK
Sai dai bayan an yi allurar, sai ta matashiyar ta kamu da tsananin rashin lafiya, lamarin da ya sa aka rankaya da ita zuwa asibiti, daga bisani kuma likitoci suka tabbatar da cewa ta rasu.
Sanarwar 'yan sanda ta kuma ce matasan sun kuma ambaci sunayen mutum shida, waɗanda ake zargin sun haɗa baki wajen aikata laifi.










