Hotunan yadda gobara ta lalata tsakiyar ƙasar Chile

Motoci da gidaje sun ƙone a cikin gundumar El Olivar, a Viña del Mar

Asalin hoton, AFP/Getty

Bayanan hoto, Motoci da gidaje sun ƙone a cikin gundumar El Olivar, a Viña del Mar
    • Marubuci, BBC Mundo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo

Gobarar daji a kasar Chile ta kashe mutane aƙalla 64 a yankin Valparaíso, yayin da ƙasar ke fuskantar bala'i mafi muni cikin shekaru da dama.

Masu aikin ceto na fafatawa wajen isa yankunan da lamarin ya fi kamari kuma ministar harkokin cikin gida, Carolina Tohá ta ce ana sa ran adadin wadanda suka mutu zai zarce haka kuma sama da mutane 370 ne suka bace.

An yi imanin ita ce gobarar dajin Chile mafi muni a tarihi.

Yawancin waɗanda abin ya shafa sun ziyarci yankin gaɓar teku a lokacin hutun bazara.

"Yanayin Valparaiso shi ne mafi muni," in ji Toha, yana mai cewa ƙasar na fuskantar bala'i mafi muni tun bayan girgizar ƙasa a shekara ta 2010 da ta kashe kusan mutum 500.

El Olivar dake Viña del Mar na daya daga cikin wuraren da gobarar ta shafa

Asalin hoton, EPA-EFE

Bayanan hoto, El Olivar dake Viña del Mar na ɗaya daga cikin wuraren da gobarar ta shafa
Wata mata na ƙoƙarin kashe gobarar a cikin gundumar Quilpe, a Valparaíso

Asalin hoton, AFP/Getty

Bayanan hoto, Wata mata na ƙoƙarin kashe gobarar a cikin gundumar Quilpe, a Valparaíso

Shugaban ƙasar, Gabriel Boric dai ya ayyana dokar ta ɓaci.

Gobarar ta ƙona gidaje tsakanin 3,000 zuwa 6,000

Rodrigo Mundaca, gwamnan yankin Valparaiso, ya fada a ranar Lahadin da ta gabata cewa ya yi imanin cewa wasu daga cikin gobarar na iya kasancewa da gangan, yana mai nanata ka'idar da shi ma shugaba Gabriel Boric ya ambata ranar Asabar.

"Wadannan gobarar ta fara ne a lokaci guda," in ji Mundaca. "A matsayinmu na hukumomi za mu yi aiki tukuru don gano wanda ke da alhakin wannan gobarar."

Maƙwabta na ƙoƙarin kashe wutar da abin da suke da shi a hannu, kamar waɗannan masu sa kai daga Viña del Mar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Maƙwabta na ƙoƙarin kashe wutar da abin da suke da shi a hannu, kamar waɗannan masu sa kai daga Viña del Mar
Jiragen sama masu saukar ungulu sun yi aiki tuƙuru domin shawo kan gobarar

Asalin hoton, EPA/EFE

Bayanan hoto, Jiragen sama masu saukar ungulu sun yi aiki tuƙuru domin shawo kan gobarar
Ƴan sanda, Carabineros na shan ruwa tare da huta wa bayan fafatawa da gobarar a Viña del Mar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ƴan sanda, Carabineros na shan ruwa tare da hutawa bayan fafatawa da gobarar a Viña del Mar

Gwamnatin Chile ta bukaci mutane da ka da su je wuraren da abin ya shafa, kuma an sanya dokar ta-ɓaci a cikin al'ummomi da dama don bai wa kungiyoyin agaji damar gudanar da ayyukansu cikin inganci da aminci.

Masu kashe gobara sun ceci zomaye a cikin gundumar Quilpe, a Valparaíso

Asalin hoton, AFP/Getty

Bayanan hoto, Masu kashe gobara sun ceci zomaye a cikin gundumar Quilpe, a Valparaíso

An ayyana dokar ta-baci a Viña del Mar, da garuruwan da ke makwabtaka da Quilpé da Villa Alemana a wani bangare na kokarin hana satar dukiyar jama'a da saukaka zirga-zirgar jami'an gaggawa.

Gobarar ta bazu zuwa garuruwa kamar wannan a Viña del Mar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Gobarar ta bazu zuwa garuruwa kamar wannan a Viña del Mar
Akwai mutane da yawa waɗanda kusan ba su da komai sakamakon gobarar, kamar a cikin wannan unguwar ta Los Olivos, a cikin Viña del Mar.

Asalin hoton, AFP/Getty

Bayanan hoto, Akwai mutane da yawa waɗanda sun kusan rasa komai sakamakon gobarar, kamar a cikin wannan unguwar ta Los Olivos, a cikin Viña del Mar.
Hayaki mai kauri ya rufe garuruwa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An ga hayaki mai kauri na tashi a garuruwa
Gobarar ta lakume daukacin unguwanni, kamar wannan a Viña del Mar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Gobarar ta kuma lakume daukacin unguwanni, kamar wannan a Viña del Mar
Wannan wani gida ne da gobarar ta lalata a Villa Independencia,da ke Villa del Mar

Asalin hoton, EPA/EFE

Bayanan hoto, Wannan wani gida ne da gobarar ta lalata a Villa Independencia,da ke Villa del Mar

Jami’an kashe gobara sun kwashe sa’o’i suna ƙokarin kashe wutar da ta tashi a ɗaruruwan gidaje da masana’antu a birnin.

Gobarar ta kuma shafi dabbobin gida da dama kamar wannan magen a El Salto, a Viña del Mar

Asalin hoton, EPA/EFE

Bayanan hoto, Gobarar ta kuma shafi dabbobin gida da dama kamar wannan magen a El Salto, a Viña del Mar
Gobarar dajin a yanki na El Patagual, kusa da Viña del Mar, ta yaɗu a cikin birane.

Asalin hoton, EPA/EFE

Bayanan hoto, Gobarar a yanki na El Patagual, kusa da Viña del Mar, ta bazu zuwa cikin birane.