Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotunan yadda gobara ta lalata tsakiyar ƙasar Chile
- Marubuci, BBC Mundo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo
Gobarar daji a kasar Chile ta kashe mutane aƙalla 64 a yankin Valparaíso, yayin da ƙasar ke fuskantar bala'i mafi muni cikin shekaru da dama.
Masu aikin ceto na fafatawa wajen isa yankunan da lamarin ya fi kamari kuma ministar harkokin cikin gida, Carolina Tohá ta ce ana sa ran adadin wadanda suka mutu zai zarce haka kuma sama da mutane 370 ne suka bace.
An yi imanin ita ce gobarar dajin Chile mafi muni a tarihi.
Yawancin waɗanda abin ya shafa sun ziyarci yankin gaɓar teku a lokacin hutun bazara.
"Yanayin Valparaiso shi ne mafi muni," in ji Toha, yana mai cewa ƙasar na fuskantar bala'i mafi muni tun bayan girgizar ƙasa a shekara ta 2010 da ta kashe kusan mutum 500.
Shugaban ƙasar, Gabriel Boric dai ya ayyana dokar ta ɓaci.
Gobarar ta ƙona gidaje tsakanin 3,000 zuwa 6,000
Rodrigo Mundaca, gwamnan yankin Valparaiso, ya fada a ranar Lahadin da ta gabata cewa ya yi imanin cewa wasu daga cikin gobarar na iya kasancewa da gangan, yana mai nanata ka'idar da shi ma shugaba Gabriel Boric ya ambata ranar Asabar.
"Wadannan gobarar ta fara ne a lokaci guda," in ji Mundaca. "A matsayinmu na hukumomi za mu yi aiki tukuru don gano wanda ke da alhakin wannan gobarar."
Gwamnatin Chile ta bukaci mutane da ka da su je wuraren da abin ya shafa, kuma an sanya dokar ta-ɓaci a cikin al'ummomi da dama don bai wa kungiyoyin agaji damar gudanar da ayyukansu cikin inganci da aminci.
An ayyana dokar ta-baci a Viña del Mar, da garuruwan da ke makwabtaka da Quilpé da Villa Alemana a wani bangare na kokarin hana satar dukiyar jama'a da saukaka zirga-zirgar jami'an gaggawa.
Jami’an kashe gobara sun kwashe sa’o’i suna ƙokarin kashe wutar da ta tashi a ɗaruruwan gidaje da masana’antu a birnin.