An yanke wa wani mutum shekara 30 a gidan yari kan safarar yara masu nakasa.

Agnes Wahito
Bayanan hoto, Mai shari'a Agnes Wahito yayin hukuncin ta gano cewa mai laifin shi ma mai bukata ta musamman ne

An samu wani mutum da aka gudanar da shirin binciken kwakwaf na BBC Africa Eye a kan shi da laifin safarar mutanen da ke fama da nakasa a Kenya.

Mutumin mai suna James Zengo Nestory an yi masa umarnin ya biya tarar shilling 30,000,000 na kudin Kenya wanda ya yi daidai da dalar Amurka 242,000 ko kuma shekara 30 a gidan yari.

A watan Yunin da ya gabata, wani binciken kwakwaf da BBC ta yi, ya bankado yadda ake safarar yara masu nakasa daga Tanzaniya zuwa Kenya.

An kwaso yara da yawa daga wajen iyayensu kan alkawarin za su samu rayuwa mai kyau.

Maimakon haka, an rika tilasta musu yin bara a gefen tituna na tsawon shekaru – yayin da wadanda ke kula da su ke kwashe ladan barar da suke yi na yau da gobe.

An yi zargin ana dukan wadanda suka ki yin bara daga cikin wadan nan yara, ko kuma suka gaza kawo kudaden da suka kamata.

An kama James Zengo Nestory kuma wata kotu a Nairobi babban birnin Kenya ta yanke masa hukunci.

A yayin yanke hukuncin, alkaliyar kotun Mai shari’a Agnes Wahito ta ce “na fuskanci kaima kana da taka nakasar. Gidan yari ba zai taba yi maka dadi ba”.

"Wannan ne karon farko da aka kama ka da aikata babban laifi, na baka damar biyan tarar 30,000,000. In kuma baka da su, zaka yi zaman gidan yari na shekara 30.