An ga hamshaƙin watan da ya haske sassan duniya a daren Litinin

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Daga Andre Rhoden-Paul da Rachel Russell
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, .
- Lokacin karatu: Minti 4
Mutane sun yi ta ɗaga kai sama cikin al'ajabi lokacin da wata ya bayyana cikin haske da girma fiye da yadda aka saba gani ranar Litinin da daddare.
A cewar hukumar binciken sararin samaniyan Amurka ta NASA, ana ganin hamshaƙin watan da ke bayyana a cikin Yuli, da siffar cikarsa har tsawon sama da kwana uku.
Watan kan yiwo ƙasa-ƙasa fiye da yadda aka saba gani a kan hanyar da yake zagaye Duniyar Az.
Hakan na faruwa ne saboda hanyar da watan yake bi, ba kammalallen zagaye ba ne sakamakon maganaɗisun janyo abu ƙasa da Duniyar Az ke yi, maimakon haka sai ya yi ta katantanwa kamar wani zobe.
Saboda haka, akwai lokutan da a zagayen kwana 27 da 'yan sa'o'i da watan ke yi, yana zuwa kusa da Duniyar Az, akwai kuma lokutan da yakan yi can ƙololuwar sama.

Ana samun irin wannan hamshaƙin wata ne, idan watan ya yiwo kusa-kusa sosai da duniyarmu a kan hanyar da yake zagaye.
A cewar Cibiyar Binciken Sararin Samaniya ta Royal Observatory, Amurkawan Asali ne suka yi wa cikakken watan na Yuli, laƙabi da sunan 'Buck Moon' saboda ƙahonnin dabbar gwanki na kai wa matuƙar girmansu a watan Yuli. Ƙahonnin suna kaɗewa sannan su suke tsirowa a lokacin.
Watan ya kai ƙololuwar haskensa da ƙarfe 12:39 agogon Najeriya ranar Litinin, a cewar Cibiyar nazarin hasashen yanayi ta Old Farmer's Almanac.
Cibiyar Almanac ɗin wadda ke wallafa bayanai kan al'amuran ilmin taurari ta ce Hamshaƙin Watan ya fi kusantar Duniyar Az a zagayen da yake yi idan an kwatanta da cikakkun watannin da muka riga muka gani a wannan shekara.
Cikakken watan Agusta zai kasance hamshaƙin watan da kawai zai fi kusa da Duniyar Az a wannan shekara, in ji cibiyar.
Ga wasu daga cikin hotunan hamshaƙin watan daga sassan duniya a ranar Lahadi da Litinin:

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, PA Media

Asalin hoton, JACK MARCH/BBC WEATHER WATCHERS

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, PA Media

Asalin hoton, EPA

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, AFP

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images














