Modric ya cika shekara 39 da haihuwa

Asalin hoton, Getty Images
Luka Modric na bikin cika shekara 39 da haihuwa ranar Litinin.
An haifi ɗan wasan mai taka leda daga tsakiya a Zadar a Croatia ranar 9 ga watan Satumbar 1985, wanda ya koma Real Madrid a 2012/13.
Daga nan ɗan ƙwallon ya taka rawar da ya yi fice a duniya da ta kai ya lashe kofi 27 a ƙungiyar ta Sifaniya.
Cikin kofunan da ya ɗauka sun hada da Champions League shida da Club World Cup biyar da Europa Super Cup huɗu da La Liga huɗu da Copa del Rey biyu da Spanish Super Cup biyar.
Ƙwwazon da ya yi a tawagar Croatia da ƙungiyar Real Madrid ta kai ga ya lashe ƙyautar Ballon d'Or da ta fitatcen ɗan wasan Fifa a 2018.
Ƙyaftin ɗin Real Madrid yana kaka ta 13 a Sifaniya, wanda ya buga karawa 539 da cin ƙwallo 39.

Asalin hoton, Getty Images
Ya fara taka leda a matashin ɗan wasa
- 1996–2000 Zadar
- 2000–2003 Dinamo Zagreb
Ya fara tamaula a matakin ƙwararren ɗan ƙwallo
- 2003–2008 Dinamo Zagreb
- 2003–2004 → Zrinjski Mostar
- 2004–2005 → Inter Zaprešić - wasannin aro
- 2008–2012 Tottenham
- 2012– Real Madrid
Wasannin da ya buga wa tawagar Croatia
- 2001 Croatia U15
- 2001 Croatia U17
- 2003 Croatia U18
- 2003–2004 Croatia U19
- 2004–2005 Croatia U21
- 2006– Croatia 180 Babbar tawagar Crotia











