'Mun gaji da 'yan gudun hijira a Turkiyya'

Asalin hoton, Reuters
Omer Faruk Cecen, wani lauya mai shekaru 30 daga Istanbul ya ce "Turkiyya ƙasa ce mai kaɓar baƙi, amma mun gaji da zuwan `yan gudun hijira."
Ya zaɓi dan takarar shugaban ƙasa mai adawa da `yan gudun hijira, Sinan Ogan a zagayen farko na zaben shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar 14 ga watan Mayu.
"Ba `yan siriya kadai ba, akwai kuma `yan Afghanistan, `yan Ukraine, da sauran ƙasashe, mun gaji. A yayin da al`ummata ke fafutukar ganin sun biya buƙatunsu, `yan gudun hijira a Turkiyya suna amfana da kuɗaɗen jama`a, da ililmi kyauta, wannan ba adalci, ba za mu dauka ba", ya qara da cewa.
Elif Arslan, enginner mai shekaru 24 tana goyon bayan abin da Omer ya ce.
Ta ce "Amurka ma ai tana cikin ƙasar da karɓan baqi, amma babancin mu shine ba mu da isashen arziƙi da zai riƙe yan gudun hijira kamar yarda Amurka za ta riƙe su."
Kyamar 'yan gudun hijira

Mutanen ƙasar turkiyya suna goyon bayan Adawar `yan gudun hijirar da Elif da Omer suke yi. Sun ce ƙasar ta karɓi yan gudun hijira fiye da ko wane ƙasa, sun kai wajen su million hudu.
Hauhawar hauhawar farashin kayayyaki da faɗuwar darajar kudi da kuma tsadar rayuwa ne ke haifar da ƙaruwar ƙyamar yan gudub hijira a ƙasar.
Elif ta ce, "Muna ganin za su samu kyakyawar rayuwa yanzu a siriya ba kamar lokacin da ƙasar ta ke cikin yaƙi ba.
"Ƙasar Syria ma tana buqatan mutanen ta da su koma, lokacin komawar su yiyi."
Mayar da dukkan `yan gudun hijirar dai shine abin da shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdoagan yayi alƙawari. Yana neman ci gaba da mulkinsa zuwa shekara talatin kuma hakama abokin hamayyarsa, Kemal Kilicdaroglu, dan takarar kawancen jam'iyyu shida na adawa, yana yin irin wannan alkawarin da fatan samun kuri'un masu zabe na kasa a zagaye na biyu na ranar 28 ga watan Mayu.
'Za mu mayar da su'
To me zai iya faruwa da kusan ‘yan gudun hijira miliyan hudu a Turkiyya bayan zaben?
Har zuwa kwanan nan, Shugaba Erdogan yana cewa ba zai taba mayar da Siriyawa zuwa kasashensu ba. Sai dai kwanaki kadan gabanin zagaye na biyu na zaben, ya sanar da cewa Turkiyya za ta maida da wasu 'yan kasar Siriya.
Da yake magana da tashar talabijin ta TRT Haber ta gwamnatin kasar a ranar Litinin 22 ga watan Mayu, shugaba Erdogan ya ce:
"Ƴan gudun hijira 450,000 sun riga sun koma gidajen briquet da muka gina. Yanzu, muna sa ran ƴan gudun hijira miliyan daya za su koma sabon gidan wanda za a gina shi a arewacin Siriya,"
Ya ƙara da cewa za a iya tattaunawa da wani shiri na hakan a tattaunawar da za a yi da gwamnatin Syria bayan zagaye na biyu na zaben.
Matsugunan Syria
Tuni dai Turkiyya karkashin Erdogan ta gina matsugunai da dama a arewa maso yammacin Siriya tare da taimakon kungiyoyi masu zaman kansu na Turkiyya.

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
“Sadar da alakar da ke tsakaninta da Syria wata manufa ce da shugaba Erdogan da Kilicdaroglu suka amince da shi, wanda zai ba da damar komawar ‘yan gudun hijira.
A watan Janairun 2023, Shugaba Erdogan ya ce zai iya ganawa da shugaban Syria Bashar al Assad don "kawo zaman lafiya" a yankin. Amma da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Rasha RIA-Novosti a watan Maris, shugaban na Syria ya ce a shirye yake da ya gana da Erdogan bisa sharadin cewa Turkiyya za ta janye dakarunta daga arewacin Siriya - wanda banu alamun zai iya faruwa yanzu ba.
Sai dai Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Mevlut Cavusoglu ya kasance mai sassaucin ra'ayi game da mayar da 'yan gudun hijirar zuwa gida.
A ranar Litinin 22 ga watan Mayu, ya bayyana cewa ba dukkan ‘yan gudun hijirar Syria ne za a mayar da su ba, domin kasar na bukatar ma’aikata a fannin noma, masana’antu da kasuwanni.
Kilicdaroglu, wanda aka san shi da natsuwa da tattarowa, yana kuma yin amfani da fushin da ke ci gaba da nuna yadda gwamnatin Erdogan ke tafiyar da 'yan gudun hijira a lardin. Ya karasa sautin muryarsa cikin.
Kilicdaroglu ya soki manufar ‘maraba’ da gwamnati mai ci ta yi wa ‘yan gudun hijirar da suka tsere daga yakin Syria, ya ce: “Erdogan, da gangan ka ba wa ‘yan gudun hijira miliyan 10 izinin shiga Turkiyya, har ma ka sanya takardar izinin zama dan kasar Turkiyya a kasuwa domin samun kuri’u daga kasashen waje,” ba tare da ya tanadar da wata hujja kan tuhumar da ya yi ba.
"Ina fada a nan: zan mayar da duka 'yan gudun hijira gida da zaran an zabe ni a matsayin shugaban kasa, shikenan" ya jaddada.
A ranar 22 ga watar Mayu, yayin da ya ziyarci garin Hatay da ke kudancin Turkiyya inda girgizan kasa ya auku, Kilicdaroglu ya maimaita taken sa na neman zabe "Ba za mu taba maida Turkiyya wurin ajiyar 'yan gudun hijira ba."
Garin Hatay da ke iyaka da Syria na tsugunar da 'yan gudun hijira da dama.
Koke-koke da mu ke ji kan 'yan gudun hijira a Hatay yayi kama da wanda muke ji a larduna 81 na Turkiyya. Ku tsaida shawara kafin 'yan gudun hijira su mamaye kasar," in ji Kilicdaroglu a cikin jawabinsa ga mazauna yankin.

Asalin hoton, EPA-EFE
A baya dai ya bayyana shirinsa na mayar da ‘yan Syria da suka rasa matsugunansu zuwa kasarsu cikin shekaru biyu bayan kulla yarjejeniya da shugaban Syria Bashar al Assad, tare da tabbatar da tsaron lafiyarsu, da kuma hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya.
Kilicdaroglu ya kuma yi barazanar ficewa daga wata yerjejeniya da Tarayyar Turai inda Turkiyya ta amince da karbar miliyoyin ‘yan gudun hijira daga Syria, tare da hana su tsallakawa cikin kasashen kungiyar ta EU domin neman mafaka. ita kuma Turkiyya za ta karbi Yuro biliyan 6. Kilicdaroglu ya ce EU ba ta cika bangarenta na yarjejeniyar ba.
A cikin watan Maris, ya maida martani ga wani sako da wata kafar yada labarai ta wallafa a shafukan sada zumunta, inda ake tambayar abin da zai faru da yarjejeniyar da kungiyar tarayyar turai , Kilicdaroglu ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa "Tun farko na fito fili kan wannan batu, Turkiyya farko."
Ko ya halatta a mayar da 'yan gudun hijira?
Ko za a iya sanya 'yan gudun hijira su koma gida? Shin ya dace da dokoki na duniya?
A cewar Birol Baris, mataimakin shugaban kungiyar lauyoyi ma su kula da hakkin ‘yan gudun hijira da bakin haure ta Istanbul, ba bisa ka’ida ba ne a mayar da ‘yan gudun hijirar ba tare da tabbatar da cewa an kyautata yanayin da ya sa su gudo daga kasashensu ba.
A hirar da ya yi da wakilin BBC Burak Abatay a Turkiyya, ya ce: "Har ila yau yana da matukar muhimmanci a tabbatar da cewa sun amince da cewa za su koma. ma'ana ya kamata a binciki halin komawar su, ba a tilasta masu da komawa ba ta hanyar tsarin lakabin na sa kai."
Dr Neva Ovunc Ozturk da ke Sashen Shari'a na Jami'ar Ankara ta yi imanin cewa akwai yuwuwar samun komawar Siriyawa bisa son rai, amma "da wuya a iya tantance ko guda nawa ne za su yi hakan."
Komarwan dole fa? za su yiwu?
A cewar kwararrun da ke magana da BBC, hakan zai dogara ne kan yadda kungiyoyin kasa da kasa suka tantance kasar da za a koma. Amma a halin da ake ciki yanzu, idan aka yi la'akari da rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar kan kasar Siriya, Dr Ovunc Ozturk ya ce ba zai yiwu a tilasta wa 'yan kasar su koma kasarsu ba, domin har yanzu an san halin da ake ciki yana da muni.
Don haka, yayin da makomar 'yan gudun hijira a Turkiyya bayan zabuka ya dogara da sakamakon zaben, matsayinsu zai kasance kan gaba a tunanin 'yan takara da na gwamnatocinsu.
Duk da cewa ra'ayin 'yan takaran biyu ya banbanta kan manufofi da dama, kasancewar 'yan gudun hijira a kasar shi ne kadai abin da dukkansu suka yi alkawarin za su tunkara.










