Ganduje ya sauka daga muƙamin shugaban jam'iyyar APC

Lokacin karatu: Minti 3

Shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga muƙaminsa bayan kwashe ƙasa da shekara biyu yana jagorancin jam'iyyar.

Wasu majiyoyi daga fadar shugaban Najeriya sun tabbatar wa BBC cewa Ganduje ya ajiye muƙamin ne bayan da fadar shugaban ƙasa ta umarce shi da yin hakan.

"Da gaske ne Ganduje ya sauka tun jiya (Alhamis) aka ba shi umarnin ya rubuta takardar murabus, a yau da safe (juma'a) ya miƙa takardar," in ji majiyar.

Hakan na zuwa ne bayan wani rudani da aka samu kimanin mako ɗaya da ya gabata a lokacin taron jam'iyyar ta APC na arewa maso gabashin ƙasar.

A lokacin taron, wasu daga cikin ƴan jam'iyyar sun nuna fushi kan rashin bayyana sunan mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shettima a matsayin wanda zai mara wa Tinubu baya takarar shugaban ƙasa ta shekara ta 2027.

Duk da cewa APC na samun tagomashi a baya-bayan nan ta hanyar karɓar ƴan siyasar da ke sauya sheƙa daga jam'iyyun adawa, masu sanya ido kan lamurran siyasa na ɗora ayar tambaya kan alaƙar shugaban ƙasar da mataimakinsa.

Ganduje ya zama shugaban jam'iyyar APC ne bayan ajiye aikin tsohon shugaban jam'iyyar Abdullahi Adamu, jim kaɗan bayan nasarar jam'iyyar a babban zaɓen shekara ta 2023.

Daga bisani, jam'iyyar ta sanar da naɗin Sanata Abubakar Kyari, wanda shi ne mataimakin shugaban APC shiyyar arewacin ƙasar, a matsayin shugaban riƙo na jam'iyyar.

Sai dai tun bayan saukar Abdullahi Adamu ne aka yi ta raɗe-raɗin cewar Abdullahi Ganduje, tsohon gwamnan na Kano zai iya maye gurbinsa a matsayin sabon shugaban APC, kafin daga bisani aka tabbatar da naɗin nasa.

Wane ne Abdullahi Ganduje?

An haifi Abdullahi Umar a ƙauyen Ganduje da ke cikin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano a 1949.

Ya fara karatun Ƙur'ani da Islamiyya a ƙauyensu, inda ya samu ilimin addini. Ya shiga firamare ta Dawakin Tofa daga 1956 zuwa 1963.

Ganduje ya fara makarantar sakandiren Birnin Kudu a 1964 inda ya kammala a 1968.

Ya shiga makarantar horar da malamai da ke Kano tsakanin 1969 zuwa 1972.

Tsohon gwamnan jihar Kanon ya samu digirinsa na farko a fannin ilmin malanta a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria cikin jihar Kaduna a 1975.

A 1979 ne kuma ya kammala digirinsa na biyu a Jami'ar Bayero ta Kano, sannan ya sake komawa Jami'ar Ahmadu Bello daga 1984 zuwa 1985 don karanta fannin gudanar da harkokin gwamnati.

A 1993 ne ya samu digirin-digirgir daga Jami'ar Ibadan.

Siyasarsa

Ganduje ya shiga jam'iyyar NPN a jamhuriyya ta biyu sannan ya zama mataimakin sakatare na jihar Kano daga 1979 zuwa 1980.

Ya tsaya takarar ɗan majalisar wakilai a 1979 ƙarƙashin jam'iyyar NPN, amma bai yi nasara ba.

A 1998, ya shiga PDP inda ya nemi jam'iyyar ta tsayar da shi takarar gwamna, amma bai yi nasara ba, maimakon haa sai ta tsayar da Rabi'u Musa Kwankwaso.

Amma aka zaɓi Ganduje a matsayin mataimakin Kwankwaso tsakanin 1999 da 2003, sun sake cin zaɓen gwamna da mataimakin gwamna a Kano a shekara ta 2011 zuwa 2015.

A 2015 ne kuma, aka zaɓi Dakta Abdullahi Umar Ganduje matsayin gwamnan Kano, inda ya yi wa'adin mulki biyu daga 2015 zuwa 2023.