Gwamnatin Najeriya ta gaza kare rayukan al'ummarta — Amnesty International

Amnesty International

Asalin hoton, AMNESTY INTERNATIONAL

Lokacin karatu: Minti 3

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International ta zargi gwamnatin Najeriya da gaza kare yara ƙanana a fadin ƙasar, yayin da ake ci gaba da samun ƙaruwa a hare-hare da sace-sacen mutane da ake kai wa wasu makarantu a arewacin ƙasar.

Amnesty ta ce ta na nuna damuwa akan yadda gwamnatin Najeriya ke kara nuna gazawa a wajen kare rayukan mutane da dukiyoyinsu musamman ma yara 'yan makaranta.

Isa Sanusi, shi ne daraktan ƙungiyar ta Amnesty International a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, abin da ke faruwa yanzu ya nuna cewa ilimi zai kara samun koma baya duk da ya ke dama can akwai koma bayan, amma bisa ga yadda abubuwa ke faruwa a yanzu na rashin tsaro da satar dalibai abin zai kara yawa.

Ya ce," Rufe-rufen makarantu da ake yi yanzu a arewacin Najeriya, wasu yaran har abada ba za su koma makaranta ba, don haka mu muna gani wannan babban bala'i ne don haka ya kamata gwamnati ta tashi tsaye ta yi abin da ya dace."

Isa Sanusi, ya ce,"Aikin gwamnati ba wai shi ne gina kwalta gina gadar sama bane,kare dukiya da rayukan mutane shi ne abin da ya ke na farko da ya rataya a wuyan gwamnati kuma ta gaza akansa."

Ya ce." Ba mu ce gwamnati bata kokari ba, kokarin nata ne baya tabuka komai, domin abin da ya faru a 2021, shi ne ya ke faruwa a yanzu, domin a 2021 a cikin wata biyar wato daga watan Fabrairu zuwa Yunin shekarar, an sace yara a makarantu takwas, sannan a kowacce makaranta an sace yara fiye da 100, to abin da ya ke nema ya maimaita kansa ke nan."

Daraktan kungiyar ta Amnesty a Najeriya, ya ce,"Da gwamnati tana abin da ya dace wajen daukar matakai da ma koyon darasi akan abubuwan da suka faru a baya , to da ba fuskanci abin da ke faruwa a yanzu ba."

Isa Sanusi, ya ce," Mu yanzu abin da muke so shi ne a bawa tsaro fifiko, sannan idan akwai dabaru da ake amfani da su na yaki da matsalar tsaron to ya kamata a canja su, kuma a tabbatar da cewa komai nisan kauye to yara za su je suyi karatu kuma manoma za su je gona su yi nomansu ba tare da wasu sun zo sun kashe su ko sun sace su ba."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya ce,"Muna kuma so mu ga cewa idan an gama tunkarar wannan abu da ya taso na sace sacen dalibai, to ya kamata a zakulo masu satar yaran da ma wadanda ke kai hare hare makarantu don ka iwa makaranta hari laifi ne na yaki,kuma ba zai yiwu ace ana sace mutane, ana yi wa mata fyade, ana kona kauyuka, sannan kuma ace wai akwai gwamnati a irin wannan kasa, ai wannan wasa ne."

Amnesty International dai ta yi wannan zargi na gazawar gwamnatin Najeriya ne bayan da a ranar 17 ga watan Nuwambar 2025, wasu 'yan bindiga suka afka Makarantar Sakandaren 'Yan Mata ta Gwamnati da ke garin Maga, a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta Jihar Kebbi, inda suka yi awon gaba da 'yan mata 25, ciki har ƴan shekaru 13.

Sannan, kwanaki kadan bayan nan 'yan bindigar suka sake kai hari da kuma sace fiye da ɗalibai 300 daga Makarantar Firamare da Sakandare ta St. Mary's da ke Jihar Neja, lamarin da ya sanya ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta duniya ta ce ƴar manuniya ce rashin tsaro ya daɗe yana addabar ƙasar.