Amnesty ta caccaki Najeriya kan kasa kawo ƙarshen hare-haren ƴan bindiga

Iyaye mata

Asalin hoton, AMNESTY INTERNATIONAL

Bayanan hoto, Ƙungiyar ta ce daga rantsar da Tinubu an kashe sama da mutum 120

Kungiyar kare hakkin dan’Adam ta duniya, ta Amnesty International ta nuna takaicinta kan yadda ta ce ana samun ci gaba da kashe mutane a Najeriya ba tare da hukumomin kasar sun dauki kwararan matakai da za su magance hakan ba.

Kungiyar ta nuna ta damu ganin yadda ta ce a dan takadirin lokacin nan bayan rantsar da sabon shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu, an hallaka rayukan mutum har sama da 120.

Amnesty International tana nuna takaicin ne ganin yadda ta ce munanan hare-hare na ban tsoro da takaici da ‘yan bindiga ke kaiwa a kan jama’a na ci gaba da karuwa.

Kuma kusan ba kakkautawa inda masu aikata ta’asar ta ce suna cin karensu ba babbaka.

A bisa dalilai na gaza daukar matakan hukunci daga hukumomin kasar ta Najeriya, ganin yadda ta’adar wadda ke ci gaba da wakana har a yanzu da aka samu sabuwar gwamnati ta Bola Ahmed Tinubu.

Mukaddashin darektan kungiyar a Najeriya Isa Sanusi, a wata sanarwa ya ce a dan tsakankanin nan, da aka rantsar da sabuwar gwamnatin kasar ta, ranar 29 ga watan Mayu, 'yan bindiga da ke addabar jama’a a yankuna na karkara sun hallaka mutum akalla 123 a fadin Najeriyar.

Ya ce abin takaicin shi ne yadda al’ummomin karkara da ke shan akubar wadannan 'yan bindiga kusan a ko da yaushe suke zaman jiran tsammani na tashin hankalin da za su gani na miyagun hare-haren 'yan bindiga.

A kan hakan kungiyar ke jaddada kira ga sabuwar gwamnatin ta Najeriya da ta tashi tsaye haikan domin kare rayukan jama’a, wanda hakan shi ne babbar dawainiyar da ta rataya a wuyanta a cewar kungiyar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Amnestyn ta ce wajibi ne hukumomin na Najeriya su dauki matakan kawo karshen zubar da jinin haka.

Ta ce yadda gwamnati ta gaza karara wajen kare al’ummar kasar, abin na neman zama jiki.

Duk da irin alkawuran da hukumomin ke yi na daukar matakan hana hare-haren kungiyar ta ce har yanzu babu wata alama ta hakan, don kare al’ummomin da ke cikin wannan tasku.

Wadanda ta ce ba su da wata madogara in ba gwamnatin ba wadda ita kuma ta kasa sauke nauyinta a kansu.

Kungiyar ta kara da cewa dadin dadawa gazawar hukumomin Najeriyar wajen gudanar da kyakkyawan bincike mai zaman kansa kan wadannan kashe-kashe, domin magance su, ya sa abin sai karuwa yake.

A don haka kungiyar ta kare hakkin dan’Adam ke cewa ya kamata kamar yadda dokokin duniya da ma na kasar suka tanada, hukumomin Najeriya su tashi tsaye domin kare al’umma ba tare da nuna wani bambanci ba.

Kuma su hanzarta daukar matakan hukunci na shari’a ta gaskiya da adalci a kan wadanda ake zargi da aikata wadannan kashe-kasahe.

Amnestyn ta yi nuni da irin yadda aka yi irin wadannan kashe-kashe na jama’a da ‘yan bindiga ke yi su kuma sha.

Ta ce a ranar 11 ga watan Yunin nan wani dan bindiga ya kashe mutum akalla 21 a jihar Plateau.

Kwana biyu kafin wannan ‘yan bindiga sun hallaka mutum 25 a kauyen Katako, kafin wannan sun kuma kashe wasu 13 a garin Kushrki ranar 10 ga watan nan na Yuni.

Ta ce a cikin gaba dayan watan Mayu da ya gabata an kashe mutum akalla mutum 100 a garuruwa da dama a jihar Benue.

Sannan a tsakanin ranar 15 zuwa 17 ga watan na Mayu, sama da mutum 100 aka hallaka a yankin Mangu a jihar Plateau.

Kungiyar ta ce can a kudancin jihar Kaduna ma ‘yan bindiga sun kashe sama da mutum 100 a tsakanin watan Disamba na shekarar da ta wuce zuwa watan Afirilu na wannan shekara.