Matsalar Fyaɗe: Kungiyar Amnesty ta bukaci Najeriya ta gaggauta ɗaukar mataki

Wata mata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yawanci masu aikata laifin fyade ba a hukunta su a Najeriya, abin da ke sa matsalar kamari

Ƙungiyar Amnesty International ta ce gazawar Najeriya wajen tunkarar matsalar aikata fyaɗe, na ƙarfafa gwiwar masu wannan aika-aika da kashe bakin waɗanda ake yi wa.

A wani sabon rahoto da ta fitar a ranar Laraba, Amnesty ta ce gazawar 'yan sandan ƙasar ta bincike kan aikata lalata, na tauye damar samun adalci ga waɗanda aka yi wa fyaɗe.

Ƙungiyar ta yi kira ga mahukuntan Najeriya kan su ɗauki matakai yanzu, don kare mata da 'yan mata daga cin zarafin lalata da ya zama ruwan dare.

A rahoton, Amnesty International ta ce fyaɗe na ci gaba da zama ɗaya daga cikin take haƙƙin ɗan'adam mafi ƙamari a Najeriya.

Tana mai ƙarin bayani da cewa duk da matakin hukumomi na ayyana dokar ta-ɓaci kan cin zarafin jinsi, fyaɗe na ci gaba da ta'azzara a wani yanayi mai kama da annoba, inda ake tauye wa waɗanda aka yi wa fyaɗen damar samun adalci.

Masu fyaɗen kuma suna guje wa hukunci yayin da ɗaruruwan fyaɗe ke wucewa ba tare da an kai rahoto ba saboda ƙamarin cin hanci da tsangwama da kuma ɗora laifi kan waɗanda aka cutar.

Ƙungiyar ta yi gagarumin suka kan 'yan sandan Najeriya, waɗanda ta zarga da karɓar cin hanci da nufin dakatar da bincike kan laifukan da masu fyaɗe suka aikata.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufai

Asalin hoton, Kaduna Government

Bayanan hoto, Gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya ce ,'' A cire kayan aikin masu yin fyade''

A cewarta, ana sanyaya gwiwar waɗanda da aka yi wa fyaɗe daga bin kadinsu saboda gurɓataccen halin 'yan sanda kan batun cin zarafin jinsi, da ke bayyana cikin sigar tambayoyin muzantawa da ɗora laifi kan wanda aka cutar.

Rahoton ya ambato shugabar ƙungiyar Amnesty a Najeriya, Misis Ossai Ojigho na cewa ba fyaɗe kawai mata da 'yan mata ke fama da shi a Najeriya ba, ''idan ma sun yi jarumtar kai ƙara, 'yan sanda kan hantare su da cewa ƙarya ko kukan ƙarya suke yi- zolayar da takan ƙara musu zafin ciwo.''

Ƙungiyar ta kuma koka kan yadda al'adun ƙasƙantarwa na cuta da gazawar jami'an tsaro wajen yin bincike da mummunan raina mata da ƙarancin tallafi ga waɗanda aka yi wa fyaɗe, suka janyo wata al'adar rufe bakin kowa da galatsi.

Amnesty International

Asalin hoton, iStock

Amnesty ta ce hakan na ci gaba da sanyaya gwiwar ɗaruruwan mata da 'yan mata duk shekara.

Ta kuma nusar kan yadda ƙananan yara waɗanda ke ci gaba da fuskantar cin zarafin lalata, ke fama da matsaloli wajen kai rahoton irin waɗannan laifuka saboda rashin tsarin kai rahoto mai sakin fuska ga yara.

Amnesty ta ce babu ƙwaƙƙwaran matakin da ake ɗauka don tunkarar matsalar fyaɗe da gaskiyar da ta dace.

Ta nuna cewa tsakanin watan Janairu zuwa Mayun bara, 'yan sandan Najeriya sun karɓi rahoton fyaɗe fiye da 700.

An kuma ba da rahoton ministar mata ta ƙasar Pauline Tallen tana iƙirarin cewa aƙalla ƙorafin fyaɗe 3,600 aka shigar lokacin kullen korona.

Yayin da Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Najeriya ta bayar da rahoton karɓar ƙorafe-ƙorafen fyaɗe 11,200 a gaba dayan shekarar 2020.

Zuwa yanzu hukumomin 'yan sandan Najeriyar ba su ce komai ba dangane da rahoton na kungiyar ta Amnesty International wanda ya yi kakkausar suka a kansu.