Ƙasashen da ba su yanke hukuncin kisa a duniya

Igiyar rataye masu laifi
    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

Adadin mutanen da ake zartar wa hukuncin kisa na ƙaruwa a duniya duk da cewa ƙasashe da yawa sun daina amfani da kisa a matsayin hukuncin manyan laifuka.

A watan Janairun 2024 ne aka yanke wa wani ɗan Amurka hukuncin kisa ta hanyar amfani da iskar gas, karo na farko da aka yi amfani da irin wannan tsari.

Sannan aka yanke wa wani ɗan Japan hukuncin kisa saboda wutar da ya cinna wadda ta yi ajalin mutum 36.

Waɗanne ƙasashe ne suka daina amfani da hukuncin kisa?

Wani filin aiwatar da hukuncin kisa a Afghanistan

Asalin hoton, Getty Images

Zuwa ƙarshen 2024, akwai ƙasashe aƙalla 145 da suka daina amfani da hukuncin kisa gaba ɗaya a yanzu, idan aka kwatanta da 48 kacal da suka daina ya zuwa shekarar 1991.

A 2022, ƙasashe shida ne suka daina yanke hukuncin kisa - ko dai gaba ɗaya ko kuma wani ɓangare.

Huɗu daga cikinsu - Kazakhstan, Papua New Guinea, Saliyo, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya - sun jingine shi kwatakwata.

Equatorial Guinea da Zambia sun ce za a rika amfani da shi ne kawai kan laifuka mafiya ƙololuwar muni.

A watan Afrilun 2023, majalisar dokokin Malaysia ta kaɗa ƙuri'ar daina amfani da shi a matsayin tilas kan laifuka 11, ciki har da kisa da kuma ta'addanci.

Majalisar dokokin Ghana ma ta kaɗa ƙuri'ar soke hukuncin kisa a watan Yulin 2023.

Waɗanne ƙasashe ne suka fi yanke hukuncin kisa?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƙasashe 20 ne suka zartar da hukunbcin kisa a 2022, idan aka kwatanta da 18 da suka yi hakan a 2021.

Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta ce jimillar mutum 1,518 aka zartar wa hukuncin kisa a duniya, inda aka samu ƙarin kashi 32 cikin 100. Sai dai ta ce haƙiƙanin adadin ya zarta haka sosai saboda yadda ƙasashe ke ɓoye batun.

Bayan China, Amnesty ta ce ƙasashen da suka fi kashe mutane a 2024 su ne Iran (972), da Saudiyya (345), da kuma Iraƙi (63). Su ne suka zartar da kashi 91 cikin 100 na duka ƙasashen duniya.

Ana yi wa China kallon ƙasar da ta zarta kowacce aiwatar da hukuncin kisa a duniya, amma ba a sanin haƙiƙanin adadin mutanen, saboda gwamnati ba ta bayyana su.

Ƙasashen Koriya ta Arewa da Vietnam ma na amfani da hukuncin kisa sosai amma ba su bayyanawa a hukumance.

Amnesty ta ce ta samu rahoton zartar da hukuncin kisa a bainar jama'a aƙalla sau uku a 2022 a Iran.

Ta ce Iran ɗin ta kashe aƙalla mutum biyar saboda laifukan da suka aikata a lokacin da suke ƙasa da shekara 18 da haihuwa.

Saudiyya ta kashe mutane mafiya yawa a duniya a 2022 cikin shekara 30.

Ƙasashe biyar - Bahrain, Comoros, Laos, Nijar, Koriya ta Kudu - su ne suka yanke wa mutane hukuncin kisa a 2022 bayan sun shafe tsawon lokaci ba su yi amfani da shi ba.

Duk da cewa adadin na raguwa a Amurka, amma ya ƙaru a 2021, amma duk da haka ya yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da shekarar 1999.

Mutum nawa aka kashe saboda safarar miyagun ƙwayoyi?

Amnesty International ta ce sama da kashi 40 cikin 100 na mutanen da aka zartar wa hukuncin kisa a 2024 saboda laifukan ta'ammali da miyagun ƙwayoyi ne.

A 2022, an kashe mutum 325 saboda laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi. Ƙasashen da suka aikata hakan su ne:

  • Iran - 255
  • Saudiyya - 57
  • Singapore - 11

A 2023, Singapore ta zartar da hukuncin kisa kan mace ta farko cikin shekara 20. A 2018 aka kama Saridewi Djaman da laifin safarar hodar ibilis.

Ta yaya ƙasashe ke zartar da hukuncin kisa?

Saudiyya ce kaɗai ta zayyana fille kai a matsayin hanyar aiwatar da hukuncin kisa a 2022.

Sauran hanyoyin sun haɗa da rataya, da allura mai guba, da kuma harbi da bindiga.

A watan Janairun 2024 jihar Alabama ta Amurka ta zartar wa wani mai laifin kisa Kenneth Smith hukuncin kisa ta hanyar amfani da iskar nitrogen gas.

Ya zama mutum na farko a duniya da aka zartar wa hukuncin ta irin wannan hanyar, a cewar cibiyar Death Penalty Information Center da ke Amurka.

Lauyoyin Mista Smiths sun ce salon da ba a taɓa gwadawa ba kafinsa "rashin imani ne".

Alabama da wasu jihohin Amurka biyu ne suka amince da amfani da iskar gas ɗin saboda ƙwayoyin da ake amfani da su wajen yi wa mutum allura mai guba ba sa samuwa cikin sauƙi.