Farashin ƙanƙara ya ninninka na burodi a Mali saboda tsananin zafi

Asalin hoton, Courtesy of Fatouma Yattara
"Na zo sayen ƙanƙara ne saboda tsananin zafi yanzu,” in ji Fatouma Yattara mai shekaru 15 lokacin da ta je wurin wani mai sayar da ƙanƙara a Bamako babban birnin kasar.
Na'urorin sanyaya ruwa ba su aiki saboda rashin hasken lantarki, don haka ta koma amfani da ƙanƙara don adana abinci yayin tsananin zafin wanda ya kai maki 48 a ma'aunin celcius.
Yana aiki zuwa taƙaitaccen lokaci, amma hauhawar farashi ta jefa mutane a wahalar rayuwa.
"A wasu wurare CFA1,000 ne daidai da dala $0.20; £0.16 na karamar jaka," in ji ta tana mai cewa har da ta CFA300,500.
Wannan ya sanya ƙanƙara ta fi burodi tsada wanda ake sayarwa CFA 250.
Al'amarin yana da wahalar gaske. Nana Konaté Traoré na girki kullum amma a baya tana girki ne a wasu kwanaki cikin mako.
"Mukan shafe kwana ɗaya ba tare da samun hasken lantarki ba," in ji ta, "don haka kayan abinci suke lalacewa sai dai a zubar".
Matsalolin dai sun faro ne kusan shekara guda da ta gabata, inda kamfanin samar da lantarki na kasar Mali ya kasa samar da wadataccen hasken lantarki saboda tarin basukan miliyoyin dala a shekarun nan. Yawancin 'yan kasar Mali ba su da injin jenereto saboda tsadar man fetur.
Rashin hasken lantarki na nufin babu na'urar sanyaya daki da dare, abin da ke tilasta wa mutane kwana a waje. Hakan kuma na cutar da lafiyar mutane.
"Muna shan wahala," cewar Soumaïla Maïga, wani matashi daga Yirimadio da ke kusa da Bamako.
"Cikin dare yanayin zafi na kaiwa maki 46 a ma'aunin celcius, muna ɗanɗana kuɗarmu. Sai na zuba wa jikina ruwa sannan nake iya jurewa."

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tun a watan Maris, yanayin zafi ya kai sama da maki 48 a wasu sassan kasar Mali, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 100 da suka hada da tsoffi da yara ƙanana.
Farfesa Yacouba Toloba ma'aikaci a asibitin koyarwa na Bamako ya bayyana cewa: "A kullum ana kwantar da mutane kusan 15 a asibiti.
"Da dama daga cikin majinyatan na fuskantar rashin ruwa a jikinsu, alamomin cutar kuma sun hada da tari da sarƙewar numfashi."
A wasu yankunan an rufe makarantu a matsayin rigakafi, an shawarci mabiya Addinin Islama wadanda suka fi yawa a ƙasar da kada su yi azumin watan Ramadan wanda aka kammala ba jimawa.
Matsanancin yanayin zafi ya shafi ƙasashe maƙota irinsu Senegal da Guinea da Burkina Faso da Najeriya da Nijar da kuma Chadi.
Jama'a na ƙoƙarin sabawa da sabon yanayin a yanzu da ake sa rai zafi zai kai maki 40 a ma'aunin celcius tsawon makwonni a Bamako babban birnin ƙasar Mali.
Yayin da rana ke dab da faɗuwa, Matar Konaté Traoré ta fito da tabarmi tsakar gida don shimfida.Ta kara da cewar:
"Dole mu fito waje a kowanne lokaci saboda zafi.''











