Bayern tana da tabbacin kwallaye daga Kane

A

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Tsohon ɗan wasan Borussia Dortmund Roman Weidenfeller, ya ce kyaftin ɗin Ingila Harry Kane ya tabbatarwa da Bayern Munich ba ta da matsalar cin kwallo.

Bayern Munich za ta ziyarci Dortmund a Der Klassiker a ranar Asabar, yayin da Keane ya ci kwallo 14 a wasa 11 a wannan kakar.

Da wannan ya ci kwallo 64 a wasa 63 da ya yi tun bayan komarsa Bayern Munich - ciki har da kwallo uku da ya ci Dortmund a watan Nuwambar 2023.

Za ta je wasanne a matsayinta na wadda ke saman teburin Bundesliga - kuma maki 10 tsakaninta da mai masaukin baƙin.

An tambayi Weidenfeller mene ne banbanci tsakanin Bayern and Dortmund, sai ya shaida wa BBC cewa. "Daya daga ciki abubuwa masu muhimmanci da Bayern take da shi, shi ne ƙoƙarin da Kane ke yi - Kwallo 14 ya ci abin mamaki.

"Babban ɗan kwallo ne kuma ya bai wa Bayern tabbacin cin kwallaye."

Duk da kwallayen da yake ci Kane mai shekara 31, har yanzu bai taba cin kofi ba.