Bidiyon matan da aka yi wa tsirara a Indiya na neman tayar da hargitsi

Tun a watan Mayu ne rikicin ƙabilanci ya mamaye yankin Manipur

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tun a watan Mayu ne rikicin ƙabilanci ya mamaye yankin Manipur

Wani bidiyo da ya nuna wasu matasa sun tasa wasu mata tsirara a gaba suna dukan su a yankin arewa maso gabashin Manipur da ke Indiya, na neman haifar da rikici a faɗin ƙasar.

Yan sanda sun ce sun gurfanar da ɗaya daga cikin waɗanda aka gani a bidiyon, sun ce kuma suna fatan damƙe sauran matasan nan bada jimawa ba.

A ranar Alhamis, majalisar ƙasar ta nemi a yi muhawara a kan batun, sai dai ƙudurin ya gamu da cikas.

Firaministan Indiya, Narendra Modi, ya ce lamarin ya kunyata Indiya a idon duniya, kuma in ji shi, ba za a sassautawa duk waɗanda ke da hannu a lamarin ba.

"Ina mai tabbatarwa yan ƙasa cewa doka za ta yi aikinta, kuma abin da ya faru da matan Manipur ba abu ne da za a taɓa mantawa da shi ba." in ji shi, daga bisani dai ya kawo ƙarshen shirun da ake zargin ya yi a kan lamarin, bayan kwashe tsawon wata biyu da faruwar lamarin a Manipur.

Alƙalin alƙalan India DY Chandrachud shi ma ya nuna damuwarsa a kan cin zarafin, ya kuma ce "kotun ƙoli ta kaɗu da ganin bidiyon".

Ya ce "idan gwamnati ba ta ɗauki mataki ba, mu za mu ɗauka."

Gargaɗi: Wannan labarin na ƙunshe da bayanai waɗanda za su iya tayar da hankali.

Ƴan sanda sun ce an ci zarafin matan ne tun ranar 4 ga watan Mayu, amman sai ranar Alhamis ɗin da ta wuce ne lamarin ya bayyana saboda bidiyon da ya yi ta yaow a shafukan sada zumunta.

Gwamnatin Indiya ta umarci kamfanonin sada zumunta su goge bidiyon daga shafukansu.

Aƙalla mutum 130 ne suka rasu, wasu 60,000 suka rasa muhallansu saboda rikicin ƙabilanci da aka fara a watan Mayu tsakanin ƴan ƙabilar Meitei da Kuku a Manipur.

Bidiyon mai cike da tashin hankali wanda ya nuna wasu mata biyu tsirara, ana cin zarafin su, ya karaɗe shafukan sada zumunta a ranar Laraba.

Bidiyon mai tayar da hankali na matan biyu, an baza shi sosai a shafukan sada zumunta ranar Laraba. Ya nuna lokacin da cincirindon 'yan ta-more ya riƙa jan su tare da tura su wani fili sannan ana ta tattaɓawa da shasshafa su.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar shugabannin ƙabilar yankin ta ce an yi ta'asar ne a wani ƙauye da ke gundumar Kangpokpi, kuma an aikata hakan ne ga matan ƙabilar Kuki-Zo, har ma ta yi zargin cewa an yi musu fyaɗen gungu.

Jikin mata fage ne da ake yaƙi kansa a Indiya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sharhin Geeta Pandey, daga BBC Delhi

Sanannen abu ne cewa a duk lokacin wani rikici ko tarzoma ta faru, sau da yawa jikin mata ne fagen yaƙi, inda ake amfani da fyaɗe da cin zarafin lalata a matsayin makaman tashin hankali don a hukunta su.

Cin zarafin da ya auku ga matan Kuki a Manipur shi ne wani misali na baya-bayan nan. Bidiyon da ke nuna matan suna kuka kashirɓan, suna yamutsa fuskoki cikin azaba tare da roƙon masu auka musu da cewa su yi musu afuwa, yana da tayar da hankalin mai kallo.

Sanin gaskiyar cewa sai yanzu ne aka kama mutane a karon farko, bayan fiye da tsawon wata biyu, da kai rahoto ga 'yan sanda, abu ne mai sanyaya gwiwa ga hukumomi - musamman ma tun da yake da yawan mazan ana iya shaida su ƙarara a cikin bidiyon.

Sai dai fushin da ya zo bayan bayyanar bidiyon a Indiya ya haskaka filita a kan irin wannan laifi na tashin hankali. Lamarin kuma ya bijiro da tambayoyi a kan gazawar hukumomi wajen sanyaya zukata waɗanda aka cutar - kuma daga bisani Firaminista Modi ya yi jawabi game da rikicin ƙabilancin da ke ɗaiɗaita jihar Manipur.

Matuƙar ana son dawo da ƙwarin gwiwa a Manipur, musamman a tsakanin al'ummar Kuki tsiraru, hukumomi a yanzu na cikin matsin lamba na su tashi cikin gaggawa su ɗauki mataki a kan waɗanda suka aikata wannan lamari, kuma su tabbatar an yi wa matan adalci. Mutane a faɗin ƙasar na jin cewa irin wannan bai kamata a ce tana faruwa a sabuwar Indiya ba.

"Fyaɗen gungun ya faru ne bayan an ƙona ƙauyen mata kuma cincirindon mutanen sun lakaɗa wa wasu maza guda biyu dukan kawo wuƙa," cewar ƙungiyar shugabannin ƙabilu 'yan asalin yankin. Sai dai ƙorafin da wani dangin ɗaya daga cikin matan da aka ci wa zarafi suka kai wa 'yan sanda, ya ce ɗaya a cikinsu ce kawai aka yi wa fyaɗen gungu. Ya ƙara da cewa akwai ma wata mace ta uku da aka tilasta mata yin tsirara amma ita ba a gan ta a bidiyon ba.

'Yan sanda sun ce lamarin ya faru ne ranar 4 ga watan Mayu kuma an kai musu rahoton satar mutane da aikata fyaɗen gungu da kisan gilla a lardin Thoubal.

'Yan siyasa daga ɓangarori daban-daban sun yi Allah-wadai da lamarin.

Wata ministar gwamnatin tarayya, Smriti Irani ta bayyana lamarin da "tsantsar wulaƙanta ɗan'adam".

Shugabannin adawa da yawa kuma sun soki lamirin gwamnatin jam'iyyar BJP saboda rashin tashi tsaye wajen kwantar da rikicin da ya ɓarke a jihar.

Jagorar jam'iyyar Congress Priyanka Gandhi Vadhra ta ce "hotunan cin zarafin da aka aikata wa mata a Manipur suna da dugunzuma ran mutum".

Babban ministan Delhi Arvind Kejriwal shi ma ya nanata cewa "Irin wannan ƙazamin aiki bai kamata a lamunce shi ba a tsakanin al'ummar Indiya".