Wace ƙungiya ce a Premier League za ta fi rasa ƴanƙwallo saboda gasar cin kofin Afirka?

Lokacin karatu: Minti 4

Gasar cin kofin Afirka ta ƙarato, gasar da ake ganin za ta shafi ƙungiyoyi guda 17 na gasar Premier ta Ingila saboda yadda ƴanƙwallon ƙungiyoyi da dama za su tafi gasar, wadda za a fafata a ƙasar Moroco.

Za a buga gasar ne daga ranar 21 ga watan Disamba zuwa ranar 18 ga watan Janairun 2026.

Zuwa yanzu dai babu sanarwa a hukumance kan ranar da ƙungiyoyin za su saki ƴanwasansu su tafi, sannan dole za a samu bambancin ranakun tafiyar ƴanwasan.

Ƴanwasan za su rasa wasanni shida zuwa bakwai a gasar premier, sannan ga kuma wasannin gasannin FC da Carabao idan sun kai wasan ƙarshe.

Za a kammala wasannin rukuni ne a ranar 31 ga watan Disamba, don haka ƴanwasan ƙasashen da aka cire a wasannin rukuni za su iya komawa da sauri su ci gaba da taka leda a ƙungiyoyinsu.

Ƙungiyoyin Arsenal da Chelsea da Leeds ba su da ƴanwasan da za su fafata a gasar ta Afirka, sannan Sunderland da Wolves ne gasar za ta fi kwashe wa ƴanƙwallo.

Wannan ya sa BBC ta yi nazarin kowace ƙungiya da ƴanwasan da za ta rasa domin gasar.

Aston Villa (1)

Ɗanƙwallo ɗaya ne ƙungiyar Aston Villa za ta rasa, wato ɗanwasan gabanta ɗan ƙasar Ivory Coast Evann Guessand.

Sai dai ɗanwasan mai shekara 24 wasa biyar kawai ya fara a gasar Premier ta bana, don haka ƙungiyar Villa ba za ta jijjiga ba saboda rashinsa.

Bournemouth (1)

Kamar Villa, ita ma ƙungiyar Bournemouth ba ta fuskantar barazana babba domin gasar ta Afcon.

Ɗanwasanta Amine Adli ɗan ƙasar Morocco ne, amma ɗan wasan mai shekara 25 wasa ɗaya kacal ya fara a gasar Premier ta bana tun bayan zuwansa ƙungiyar a wannan kakar.

Babban abin farin cikin kocin ƙungiyar shi ne babban ɗanwasan gabanta, Antoine Semenyo ba zai je gasar ba saboda ƙasar Ghana ba ta samu gurbi ba a gasar.

Brentford (2)

Ƴanwasan ƙungiyar Brentford biyu ne za su tafi gasar cin kofin Afirka, ciki har da daya daga cikin zaratan ƴanwasan ƙungiyar masu tashe.

Ɗanwasan ƙungiyar mafi tsada, Dango Ouattara zai taka wa Burkina Faso leda a gasar.

Ɗanwasan wanda ƙungiyar ta ɗauko a kan fam miliyan 42.5 ya zura ƙwallo biyu a kakar bana.

Haka kuma akwai ɗanwasan Najeriya Frank Onyeka, duk da cewa minti 88 kacal ya buga wa ƙungiyar a wasannin Premier.

Brighton (1)

Ƙungiyar Brighton za ta yi rashin ɗanwasan Kamaru Carlos Baleba, wanda zuwa yanzu ya buga duk wasannin ƙungiyar na kakar bana.

Amma ƙasar Gambia ba ta samu shiga gasar ba, don haka ɗanwasan ƙungiyar Yankuba Minteh ba zai tafi ba.

Burnley (3)

Ita kuma Burnley ƴanwasanta uku ne za su tafi gasar ta cin kofin Afirka.

Akwai Axel Tuanzebe wanda zai wakilci ƙasar DR Congo.

Akwai kuma ɗanwasan gaban Afirka ta Kudu Lyle Foster sai kuma ɗanwasan ƙasar Tunisia Hannibal Mejbri.

Crystal Palace (1-4)

Babban ƙalubalen da Crystal Palace ke fuskanta shi ne tafiyar ɗanwasan Senegal Ismaila Sarr, wanda zuwa yanzu ya zura wa ƙungiyar ƙwallo takwas.

Sannan kuma akwai yiwuwar wasu ƴanwasan ƙungiyar guda uku za su tafi gasar, wato ɗan Najeriya Christantus Uche da ɗanwasan Morocco Chadi Riad da na Mali Cheick Doucoure duk da cewa sun sha fama da jinya.

Everton (2-3)

Ƴanwasan Everton guda biyu da suke cikin zaratan ƴanwasan ƙungiyar ne za su tafi gasar cin kofin Afirka.

Akwai ɗanwasan gaban Arsenal Iliman Ndiaye da ɗanwasan tsakiyan ƙasar Idrissa Gueye.

Matashin ɗanwasan Morocco Adam Aznou bai samu shiga tawagar ƙasar ba tun bayan komawarsa Bayern Munich.

Akwai kuma Beto wanda ƙasarsa ta Guinea-Bissau ba ta samu gurbi ba a gasar.

Fulham (3)

Ƙungiyar Fulham za ta rasa ƴanwasa guda uku, waɗanda dukansu za su wakilci ƙasar Najeriya a gasar.

Akwai ɗanwasan tsakiya Alex Iwobi da Calvin Bassey waɗanda zuwa yanzu sun buga dukkan wasannin ƙungiyar a kakar bana, sai kuma Samuel Chukwueze.

Liverpool (1)

Ita kuma ƙungiyar Liverpool ɗanwasanta ɗaya ne kawai zai tafi buga gasar ta bana.

Mohamed Salah, wanda zuwa yanzu ya zura ƙwallo biyar zai wakilci tawagar Masar a gasar ta cin kofin Afirka.

Manchester City (2)

Ita ma ƙungiyar Manchester City za ta yi rashin ƴanwasanta guda biyu ne da za su tafi gasar cin kofin na Afirka, amma dukansu sun yi fama da rauni a kakar bana.

Ɗanwasan gaban Masar Omar Marmoush wasa biyu kacal aka fara da shi, sai kuma ɗanwasan Algeria Rayan Ait-Nouri.

Manchester United (3)

Ita kuma ƙungiyar Manchester United ƴanwasanta guda uku ne za su tafi gasar ta Afirka.

Akwai ɗanwasan Kamaru Bryan Mbeumo da ɗanwasan Ivory Coast Amad Diallo sai kuma ɗanwasan Morocco Noussair Mazraoui.

Newcastle (0-1)

Ɗanwasan DR Congo Yoane Wissa, ne kaɗai wanda ƙungiyar Newscastle za ta rasa.

Sai dai ɗanwasan ya sha fama da rauni a kakar bana, wanda hakan ya sa ake tunanin da wahala ƙasar ta gayyace shi.

Nottingham Forest (1-4)

A ƙungiyar Nottingham Forest akwai yiwuwar aƙalla ƴanwasa huɗu ne za su tafi gasar Afcon ta bana.

Ibrahim Sangare da Willy Boly za su wakilci Ivory Coast, sai ba su cika samun wasa ba.

Akwai kuma ƴanwasan Najeriya Ola Aina da Taiwo Awoniyi.

Sunderland (7)

Ƙungiyar Sunderland ce za ta shiga tasku saboda gasar ta Afcon ta bana, inda ake hasashen ƴanwasanta bakwai za su tafi.

Akwai Chemsdine Talbi na Morocco, da ɗanwasan Senegal Habib Diarra, da na Mozambique Reinildo, da Simon Adingra naIvory Coast da ɗan wasan Burkina Faso Bertrand Traore sai Arthur Masuaku da Noah Sadiki na DR Congo.

Yawancinsu ƴanwasa ne da suke matuƙar taka rawar gani a kakar bana a ƙungiyar.

Tottenham Hotspur (1-2)

Ita ma ƙungiyar Tottenham za ta rasa ƴanwasanta guda biyu ne da Pape Matar Sarr da na Mali Yves Bissouma.

Mohammed Kudus ba zai tafi ba saboda ƙasars Ghana ba ta samu gurbi ba a gasar.

West Ham (2)

Ita kuma ƙungiyar West Ham za ta rasa ƴanwasanta biyu da suke taka rawa a bana.

Akwai Aaron Wan-Bissaka na DR Congo, da kuma El Hadji Malick Diouf na Senegal.

Wolves (5)

Ƙungiyar Wolves ita ma za ta rasa ƴanwasanta biyar domin gasar ta Afcon ta bana.

Akwai ƴanwasan Zimbabwe Marshall Munetsi da Tawanda Chirewa, sai Emmanuel Agbadou na Ivory Coast da ɗanwasan Najeriya Tolu ArokodareJackson Tchatchoua na Kamaru.