Yadda ƴanbindiga ke tarewa a yankin Bakori da Faskari

Lokacin karatu: Minti 3

Rahotanni daga jihar Katsina da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya sun ce ƴan bindiga sun kafa wani sabon sansani a yankin ƙaramar hukumar Bakori, inda daga nan ne suke fita suna kai hare-hare, yayin da wasu kuma ke ƙoƙarin kafa wani sansanin a wani daji da ke gefen garin Tafoki na yankin ƙaramar hukumar Faskari.

Hakan dai ya tilasta wa jama'ar garuruwa da dama watsewa, suna yin gudun hijira zuwa wasu wurare.

Waɗannan bayanai na fitowa ne dai duk kuwa iƙirarin da hukumomin tsaro da gwamnatin jihar ta Katsina ke yi cewa suna yin iya bakin ƙoƙari a yaƙin da suke yi da ƴan bindiga, kuma ana samun nasara.

Yanzu haka dai jama'ar garuruwa aƙalla shida na yankin ƙaramar hukumar Bakori suna can cikin tashin hankali mai tsanani, a cewar wani mutumin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa:

''Ɓarayin nan dai kullum fitowa suke yi , kwashe mana dukiya suke yi, sun hana mu sakat. Yanzu tsakanin Kakumi, ungwar Lamido, Doma, mun shiga wani iftila'i wanda kullum ne ɓarayin nan sai an ce muna ga su nan suna fitowa''

''Tun suna fitowa da daddare, yanzu sun fara fitowa da rana, yanzu haka wasu gudu suke, wasu ma basu da kuɗin mota da za su tafi, a ƙasa suke tafiya da iyalinsu'' in ji shi.

Mazaunin yankin ya ce yanzu haka ƴan bindigar sun kafa sansani a Mununu inda daga nan ne suka kai mu su hari.

Ya ce ƴan bindigar sun zafafa hare harensu tun watan jiya zuwa watan da mu ke ciki.

'' Kullum kiranye mu ke yi, mu na da wata ƙungiyar da ake kira KBK, sun yi mota sun tafi har ofishin gwamna, sun je sun kai kukansu, har yanzu Allah bai sa mun cimma nasara ba''

Shi ma Moustapha Musa Kakumi ya shaidawa BBC cewa ƴan ta'adan sun sa su a gaba

''Kullun sai sun shiga cikin gari da ƙauyukan garinmu, su ɗebi mutane, su kora mutane daji, su kashe na kashewa sannan su kwashi dabobbi'', in ji shi

Su ma jama'ar shiyyar Tafoki na yankin ƙaramar hukumar Faskari na can cikin irin wannan damuwa, sakamakon yadda ƴan bindigan ke ƙoƙarin kafa sabon sansani, a cewar wani mutumnin wajen:

'' Ƴan bindigar nan suna kawo farmaki ba bu dare ba bu rana, kashe mana jama'a suke yi ba bu yaro babu babba, za su zo su ƙona gidaje su ƙona shaguna, su kwashi mata da maza a kai su daji , sai an biya kuɗin fansa''

''Yanzu ma haka suna ƙoƙarin kafa sansani a wani daji da ke nan bayan Tafoki, tun lokacin da aka gansu suna taruwa a wannan wuri da makamansu da mashinansu kuma wani da ya kuɓuta daga hannunsu ya tabbatar muna da cewa suna so ne su kafa sansaninsu a nan domin su mamaye Funtua da Danja da Bakori da Faskari baki ɗaya'', in ji shi.

Mazaunin ya ce garuruwa da suka tashi a yankin sun kai takwas zuwa goma.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Katsina, Dokta Nasiru Mu'azu, ya ce suna bibiyar waɗannan matsaloli:

'' Kullum cikin faɗa mu ke da su ta hanyar jirgin sama ta hanyar sojojin ƙasa da kuma ta hanyar ƴan banga da ƴan sanda da kuma sibil defence''

''A don haka ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajan al'ammarmu domin yana daga cikin alƙawarin da mu ka yi na cewa za mu kare alummarmu da dukiyoyinsu''

Kwamishinan dai ya ce ya takaita bayanin nasa, don kauce wa abin da ya kira 'nuna wa kurciya baka'.