'Abin da ya sa muka bijirewa dokar yin lulluɓi' - Mata a Iran

Asalin hoton, Sent to BBC
- Marubuci, Faranak Amidi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Global Women
- Lokacin karatu: Minti 4
"Gudu a tsibirin Kish abu ne da na saka kaina, tsallake layin ƙarshe tamkar nasara ce a gare ni bayan kasa yin haka na tsawon shekaru," in ji Sara, wadda ba sunanta na asali bane, kamar yadda ta faɗa wa shirin mata na BBC Global Women.
Tana ɗaya daga cikin mata 2,000, waɗanda yawanci ba su saka lulluɓi ba da aka ce wajibi ne, lokacin da suka shiga wasan tsere a wani a tsibirin Kish a farkon watan nan.
Hotuna da bidiyon wasan sun karaɗe shafukan sada zumunta, inda aka nuna suna sanye da riguna da wanduna suna ɗaure da gashin kansu, sannan suna gudu ga kuma kiɗa da waƙa na tashi, dandazon mutane kuma na kallo.
Shekaru kaɗan da suka wuce, zai yi wuya a yi tunanin cewa mata za su shiga wasan ba tare da lulluɓi ba a ƙasar. Ƙasar ta tilasta rufe kai a bainar jama'a tun shekara ta 1979, inda a wasu lokuta ake amfani da ƙarfi.
Mata da yawa sun yi ta ƙalubalantar wannan doka sama da shekara 40, sai dai lamarin ya ƙara ƙarfi da samun goyo baya a Satumban 2022 lokacin da aka kama Jina Mahsa Amini a Tehran saboda zargin rashin saka hijabi yadda ya kamata.
Ƴar shekara 22 ɗin ta mutu a hannun jami'an tsaro kwanaki kaɗan da kama ta. Daga lokacin zanga-zanga ta ɓarke a faɗin ƙasar, inda mata suke sahun gaba, suna ƙona lulluɓinsu da kuma ihu suna cewa, "Mata, Rayuwa, Ƴanci."
Zanga-zangar ta janyo kama ɗaruruwan mutane, tun wannan lokaci, wasu mata a Iran suka ci gaba da bijirewa dokokin.

Asalin hoton, Getty Images
Artemis, ba sunanta na asali ba, ta ce ta ga matan da ke bijirewa dokar saka hijabi tun tana yarinya, sai dai ta yi imanin cewa shekara ta 2022 lokacin sauyi na mata da suka nuna turjiya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Mun fara zubar da lulluɓin kai a wancan lokaci a matsayin ɓangare na zanga-zanga zuwa saka ƙananan riguna da wanduna a kan tituna a shekara da ta biyo," in ji ta.
Lokaci zuwa lokaci ana wallafa hotunan bidiyo na mata suna gudu a wuraren shaƙatawa, motsa jiki ta hanyar ɗaga kafafu sama yayin da ake ƙarfafa musu ko kuma raye-raye a cikin kantuna. Yawan hotunan bidiyo na abubuwan nan ya saka yana da wahala hukumomi su ɗauki mataki.
Ana yin kame a wasu lokuta, ana cin tarar matan sannan hukumomi na rufe shafukan sada zumuna, sai dai hakan bai sa matan sun daina ba.
Batun saka hijabi na ci gaba da janyo muhawara kan inda Iran ta dosa.
Matakin da gwamnati ke ɗauka kan mata a bainar jama'a waɗanda ba su saka lulluɓin kai ba ya bambanta - a wasu lokuta ana sassauta dokokin, a wasu kuma ana tsaurara mataki kan duk wanda ya take doka.
Suna amfani da fasahar gane fuska ta hanyar aikawa mata sakonnin gargaɗi. Mata sun ce na'urorin ɗaukar hoto na naɗar lambobin motocinsu, kuma hukumomi sun yi barazanar ƙwace motocin.

Asalin hoton, Getty Images
Kwanaki biyu kafin wasan tseren a tsibirin Kish, da ke kudancin tekun Iran, jagoran addini na ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei ya gargaɗi kafofin yaɗa labaran ƙasar cewa "kada su yaɗa ɗabi'un ƙasashen yamma dangane da mata da hijabi."
Shugaban alƙalan ƙasar, Gholam-Hossein Mohseni-Ejeie, ya ƙara da cewa "batun hijabi haƙƙin kowa ne kuma akwai buƙatar ƙara ƙaimi a ɓangaren saka hijabi da kuma yin shigar kamala a bainar jama'a".
Wasu hukumomi da ƴan majalisar ƙasar Iran sun nuna fushinsu kan batun rashin saka hijabi a baya-bayan nan - da kuma ci gaba da bijirewa da mata ke yi - sun yi gargaɗin cewa ya kamata a ɗauki mataki mai tsanani.
Daf da kafin fara wasan, an gudanar da maci don nuna goyon baya kan batun saka hijabi a Tehran. Mata cikin lulluɓi, sanye da baƙaƙen gyale masu tsawo, wanda shi aka fi aminta a Iran - su ma sun fito riƙe da alluna tare da kiran a ɗauki tsauraran matakai ga matan da suka ki saka hijabi.
Sai dai duk da wannan, matan da suka shiga wasan ba su sare ba. Ga yawancinsu, wasan ya zarce a ce gasa ne kaɗai.
"Tamkar mafarki ne da ya tabbata a gare ni, ko a shekara da ta gabata ban taɓa tsammanin zan shiga cikin gudun ba," in ji Sara.
Ta shiga yanayin jimami lokacin da ta tuna da ranar. "Ina son na yi kuka bayan tuna ranar, gani kusa da waɗannan mata duka, mun ji tamkar mun kuɓuta," a cewarta.
Artemis ta ce tana jin alfahari da kuma farin ciki na gudun da suka yi.
"Akwai lokacin da nake son tsayawa na yi kuka a lokacin da ake tseren saboda ina ganin komai tamkar mafarki, mutane na yi mana tafi, akwai waƙa na tashi... ina tunanin yadda Iran ɗin za ta kasance," in ji ta.
Mata da dama sun faɗa mana cewa gasar ta kasance kamar jimami, sun ce suna ji kamar sun yi nasara. Ga hukumomin Iran kuwa, wata alama ce da ke nuna cewa za a ci gaba da ɗaukar matakan ba sani ba sabo.











