Muna sake nazari kan jaddawalin zaɓen 2027 - INEC

Asalin hoton, INEC
Hukuma zaɓe ta Najeriya, INEC ta ce ta fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin samun maita ga ƙorafin da wasu ke yi game da jaddawalin zaɓen 2027 da ta fitar, wanda ya nuna za a yi zaɓen a cikin azumi.
INEC ta bai wa ƴan Najeriya tabbacin cewa a tsaye take domin ganin ta yi la'akari da buƙatun kowanne ɓangare na al'umma wajen tsara ayyukan ta.
Hukumar zaɓen ta sanar da cewa za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokokin tarayya a ranar 20 ga watan Faburairun 2027, yayin da na gwamnoni da ƴan majalisar dokokin jihohi zai gudana a ranar 6 ga watan Faburairun 2027.
Sai dai sanarwar hukumar zaɓen ta bar baya da ƙura, inda wasu ƴan Najeriya musamman musulmai suka bayyana damuwa kan yadda jadawalin na INEC ke nuna cewa zaɓen zai gudana ne a lokacin azumin watan Ramadan.
Masu wannan damuwa na ganin cewa hakan zai shafi musulmai ta la'akari da yadda wasu za su gaza jure fita kaɗa ƙuri'a cikin yanayi na azumi, da kuma yadda yanayin zai iya shafar ƙwazon ma'aikatan INEC da za su kasance cikin azumin lokacin.
Daga cikin waɗanda suka yi ƙorafin kan jddawalin zaɓen na INEC harda tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, wanda a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce ranar 20 ga Faburairu ta faɗo "a tsakiyar watan Ramadan," yana mai bayyana lokacin a matsayin na gudanar da azumi da ibada ga miliyoyin Musulmin Najeriya.
"Sanya lokacin gudanar da wannan muhimmin al'amari na jama'a a tsakiyar lokacin ibada yana nuna rashin fahimta da rashin kulawa ga al'amuran zamantakewa da addini na ƙasar," in ji sanarwar.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa yana da mauƙar muhimmanci a yi la'akari da yadda Najeriya ta ƙushi al'ummomi daban-daban kafin a yanke shawarar da za ta shafi rayuwar ƴan ƙasar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Amma a martanin da ta bayar bayan ƙorafe-ƙorafe da ta samu daga al'umma da dama, INEC ta ce ta zaɓi ranakun gudanar da zaɓen ne bisa la'akari da tanade-tanaden kundin tsarin mulki na 1999, da kuma dokar zaɓe ta 2022 wadda ta ƙayyade lokacin da za a kammal zaɓe a ƙasar.
Hajiya Zainab Aminu Abubakar, jami'ar hukumar zaben ta INEC ta shaidawa BBC cewa hukumar ta karbi koken masu ruwa da tsaki kan yadda ranakun zaɓen na 202 suka cikin watan Ramadan kuma tana tabbatar masu cewa tana mutumta duk wasu kiraye-kirayen da ba su saɓa wa doka ba, musamman waɗanda idan aka gyara za su sa mutane su shiga harkokin zaɓen yadd ya kamata.
Dangane da matakin da hukumar za ta ɗauka a game da ƙorafin da aka shigar mata kuwa, sai Hajiya Zainab Aminu ta ce ''Tuni hukumar zaɓen ta fara tuntuɓar masu ruwa da tsaki tare da yiyuwar neman shawarar majalisar dokoki domin ganin ta yi wani abu da bai saɓawa kundin tsarin mulkin ƙasa ba.''
Ta ce hukumar za ta yi aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki domin ganin an yi abin da duk jama'ar ƙasa za su ji daɗin bayar da gudunmuwar su a zaɓen 2027.
Ta jaddada cewa bayan tattaunawa da waɗanda ya kamata, musamman majalisar dokoki, hukumar zaɓen za ta sanar da matsayar da suka cimmawa domin jama'a su san halin da ake ciki.
Majalisa wakilan Najeriya ta kira zaman gaggawa kan jaddawalin zaɓen 2027

Asalin hoton, House of Reps
Majalisar Wakilan Najeriya ta sanar da cewa za ta yi zaman gaggawa a ranar Talata 17 ga watan Fabrairu, 2026, domin duba batutuwan da suka taso dangane da fitar da jadawalin zaɓen 2027 da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta yi.
Sanarwar da mai magana da yawun majalisar, Hon. Akin Rotimi ya fitar ta bayyana cewa an sanar da mambobin ne ta wata takarda ta cikin gida da ofishin shugaban majalisar ya fitar a yammacin ranar Juma'a.
Sanarwar ta jaddada cewa zaman gaggawar ya nuna ƙudurin majalisar na ɗaukar matakin daidaita al'amuran da ke da matuƙar tasiri ga tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya.
Ana sa ran tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi sanarwar INEC, daidai da ayyukan majalisa kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.











