Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Iran da Rasha suka riƙa safarar makamai ta cikin Syria - Bincike
- Marubuci, Sergei Goryashko, Anastasia Lorareva
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Russian
- Lokacin karatu: Minti 8
Hambarar da gwamnatin shugaban Syria Bashir Al-Asad a baya-bayan nan, da ke cikin kasashe da ke da mahimmanci ga Rasha, a yankin Gabas ta tsakiya.
Hakan kuma ya sake fito da irin yadda dangantaka mai karfi da ke tsakanin Moscow da Teheran, yayin da suke karkatar da safarar makamai a yankin.
BBC ta daga murfin da aka yi amfani da shi wajen yin harkallar makaman yayin mulkin Asad- da irin abubuwan da ka iya biyo baya bayan saukarsa.
Bargo Mai Tarwatsewa
Farfagandar kafar yada labarai ta Rasha RT ta watsa wani bidiyo a ranar 1 ga watan Octoban, 2024. Tsawon minti biyae ba tare da an yi magana ba, kyamarar daukar hoton ta dauko yadda aka ringa safarar makamai a filin jirigin sama na Syria da ke birnin Latakia.
Daya daga cikin kayan na dauke da sunan babban yayan Asad, BAsil, wanda har zuwa lokacin da aka hambarar da gwamantin dan uwansa, kuma tun 2015, ya zama sansanin sojojin Rasha da aka jibge a kasar.
Faifan bidiyon ya fara da nuna filin jirgin saman, kafin daga bisani ya nuna wani jirgin Boeing na daukar kaya, mai dauke da dagin kamfanin hukumar jirgin sama na Iran Qeshm Fars Air, yayin da ya ke sauka a filin jirgin. Haka kuma bidiyon ya nuna yadda aka ringa sauke kaya da cikinsa.
An dai sauke buhunhuna masu yawa daga jirgin, yayin da wasu mutum sanye da kayan sojoji da ke dauke da alamar yansandan sojojin Rasha, yayin da suma suke daukar faifan bidiyon. an dan bude buhunhunan da don kyamarar ta dauko abin d ake ciki, wanda kuma aka ga koren bargo. anan ne bidiyon ya kare.
Wani jami'i a yayin wata ganawa, ya ce Syria na farin ciki da kayan jinkai, da aka kawo ta jirgin ruwa daga Rasha don bayarwa ga "yan gudun hijira, da wadan da suka rasa mastugunensu".
Bayan kwanaki biyu, kafafen yada labarai na duniya sun rawaito harin da wani Isra'ila ta kai, kusa da dakin ajiyar kaya, da ke kusa da sansanin sojojin Rasha da ke Hmeimim. Bidiyon baya kai harin ya nuna iya wutar da ta tashi a wajen ba kadai, har da sauran fashewar wasu abubuwa, Inda wasu ke hasashen cewar tashar ta RT ta watsa na da alka da harin da Isra'ilan ta kai.
"Kowa ya san cewar bargunan ka iya tashi, su ma"a wani kalami mai kamar gatse wata majiyar BBC ta fada, kuma ta ke da msanaiyar abin da ya faru a Hmeimim. da muka tambaye shi ko Iran ce ta shigo da makaman ya jirgin ruwa ta hanyar amfani da hanyoyin Sojojin Rasha, da ke kula da bangaren rarra kayan jinkai, sai majiyar ta mu ta ce: "To da me kake son in ce? Wai wadan nan "Bargunan' da suka yi muguwar fashewa, da har suka kusa kawar da Hmeimim baki dayanta."
Hmeimim ba ita ce hanyar safara da Iran ke amfani da ita ba don kai kayan Lebanon, a cewar Nikita Smagin wani kwarare a yankin.
Ya ce "Iran na da kafafin shigar da kaya wadda Isra'ila ke kaiwa hari akai-akai. Amma mafi kasarin wadan suke wucewa ta su suna isa Syriya da Lebanin- ba wai ta sansanonin Rasha ba". Daga baya ya bayyana su da basu da wani mahimmanci, ga kai kaya ta jirgi ruwa, bayan da aka sami sauyin gwamanti a Syria, wanda kuma ka iya karuwa.
"Iran ta rasa kusan komai a Syriya, saboda kasar ta bar karkashin ikonta, yana iya yiwuwa har yanzu zaa iya kai irin wadan nan kaya ta Hmeimim," a cewar Smagin. "Amma saiidan Rasha ta amince da hakan, zai yi mutukar rage damar cimma wata yarjejeniya da sabbin hukumomin gwamantin Syriya.
Yadda Rasha ke amfani da Rasha ke amfani da 'fararen hula waje yin shinge'
Sarit Zehavi wata leftanal kanal ce mai ritaya, a hukumar tsaro ta Isra'ila, da ta kware wajen tattara bayan sirri a banagren soji.
Itace shugabar Cibiyar bincike da bayar da horon harkokin ilimi a Isra'ila, "da farkon mun gano yadda wasu jiragen Iran, da aka san su, da safarar makamai a yankin, sannan su sauke su a karshen filin saukar jirgi na Hmeimin, a farkon 2023", a cewar ta.
"Isra'ila ta kai hari kan filin jirige a Syriya, da ke Damascus da Alleppo, kuma Iran ba sa iya sauka a nan. Dole suka nemi mafita," a cewar Zehavi.
Ta ce cibiyar bincken ta, ta taba yin wani gargadi na cewar, jirgin farko mallakin Iran da zai sauka a Hmeimin, ka iya zama sansanin sauke makamai - yayin da Rasha ke amfani da mutane a matsayin garkuwa, a lokutan da Isra'ila suka kai hari.
Kornets in the playroom
A cikin watan Nuwamba, dakarun IDF sun wallafa wani bidiyo, da aka nade shi a kudancin Lebanon. a cikinsa, a wani daki, ana iya ganin buhunhuna, da akwatuna, da kayan wasa - kamar mai su ya bar wajen cikin hanzari. Akwain wani soja a tsaye a ciki bidiyon. Da kyamarar ta juya, a chan kusurwar dakin. akwai wani bangare da ya fashe.
"Mun shiga dakin yara, wanda ke da wani bango da fasa, "wani da ke cikin wadan suka kai sumame dakin, ya ke shidawa BBC. "Mun rushe bangon, anan ne muka gano abubuwa masu yawa.
Karamin akwati ne da aka kera shi don makaman Rasha, kuma dakarun IDF ba wai iya bindigar Kalashnikov suka gano ba, har da manyan makaman yaki, na kariya harin tankar yaki. Sun kuma gano makamancin hakan a wasu gidajen da ke yankin.
"Irin wannan makamai, ana amfani da su ne, wajen kai hare-hare a birin, ba wai na gwabzawa da dakarun IDF ba" a cewar sojan. "A kiyasi, kowane gida na iya mallakar makamin da zai wadatar da mutum biya ko shida su yi fada.
"Sojojin da ke janyewa sun dauki na'urar harba babbn makamin sai dai sun bar akwatin da aka shigo da ita. Ana iya ganin hakan a wasu hotuna da BBC ta gani.
Ana iya ganin wani bangare na na'urar harin ta Kornet, da aka nunasu a hotuna. Sun yi amfani da mamakamai na musamman da ke iya huda sulke sannan yana tashi a karo na biyu, a cikin abin hawa. Dayan kuma, akwai manyan makamai masu fashewa ciki har da makaman kare dangi.
Ya yi hasashen cewar makamin kare dangin da aka bari, an barsu ne saboda ana shan wahala wajen fitar da su cikin sirri. An shigo da shi daga kudancin Lebanon daga Syriya ta titi. Titunan da ake jefa ayar tambaya akai, na cikin idan Isra'ila ta yi fakon kai hari a lokacin Bazara, ta hanyar kai hare hare ta sama.
Hanyoyin da ake shigar da makamin Kornets
Sojan da muka yi magana da shi ya ce makaman sun iso Lebanon daga Syriya.
Sojojin IDF sun sun gano kudaden Syriya a gidajen, wanda hakan ke tabbatar da zargin kalaman nasa.
Amma sai dai stamfin da aka samu a jikin makaman, daga hukumar fitar da kaya ta Rasha, na nuni da cewar an siyarwa wani jami'ain wata kungiya, a cewar wata majiya da BBC ta yi magana da ita.
"Kungiyar farko da ta fara zuwa rai na, a wannan hali da ake ciki itace ta Gwamantin Syriya, sojojin Assad. Kamar yadda muka sani, tana da kwance mai karfi da Syriya da Hezbolla, wanda kuma ta ke kawance da Hezbollah ta Lebanon," a cewar sa.
Wata majiya ta tattara bayan sirri na kasashen Yamma, da ya yi magana da BBC, ya tabbatar da cewar mafi akasarin makaman Rasha da dakarun IDF suka gano a Lebanon sun futo ne daga sojojin gwamantin Syriya.
A wani rahoto da jaridar Walla Street journal ta wallafa, ta ambato wata majiya da bata bayyana ba, na cewar wasu daga cikin makamai masu linzamina Kornet an gano su ne a kudancin Lebanon, an kuma kera su tun a 2020, kuma an yi ta shigo da su daga Rasha da yawansu zuwa Syriya.
Gabinin a gano su, tunanin shugabancin sojin Isra'ila ya karkata kan cewar Hezbollah iya wani tsohon makamin Soviet ta ke da su.
Smagin ya ce gwamantin Assad ta na bayar da makaman Rasha ga dakarun Hezbollah; wanda daga nan sai a kai su Rasha. Amma Rasha ta shafawa idon ta toka.
"Ba su iya gani cewar an sami futar bayanai ba da ke cewar akwai kaya da aka shigo da su, Amma sai dai ko dai babu wani mataki da suka dauka, ko kuma sun sani suka yi burus, a cewar Smagin.
Har zauwa 2022, ta fi darajanta alakarta da Isra'ila, wanda hakan yasa taki bayyana barin a baiwa Hezbollah makamai, a cewar bayanin Smagin.
"Halin da ake ciki ya sauya, kuma ba a baiwa ra'ayin Isra'ila wani goyan baya ba. Duk da haka dai babu wani tabbaci daga Rasha na ko kai tsaye ta ringa baiwa Hezbolla makamai" a cewar Smagin.
Hezbollah babbar kawace ga dakarun Syriya, tana kuma yin aiki da dakarun Rasha da da ke Syriya. Sai dai an kashe musu sojoji masu yawa, a hare-haren da Isra'ila ta kai, wanda kuma haka ya raunatsu. a hannu guda hakan ya zama wani dalili da ya kai ga hambarar da gwamantin Asad shi kansa.
Bayan nan, dakarun sojin saman Isra'ila, sun yi aiki tukuru wajen kai hari kan tashohin makamai da ke Syriya. kusan kashi 80 cikin dari, na makaman Syriya an ce sun zama shara. Kadan din da suka rage sabuwar gwamantin kasar ka iya mayarwa da Hezbollah su, idan suka ga dama.
Haka kuma, An mayar da ikon mulki zuwa ga sojoji a Syriya da ke adawa da Iran. Ko me zai zama makomar sansanonin Rasha da na Theran, da sauran hanyoyin raraba makamai a Syriya wanda hakan babban abu ne.