Yadda Iran da Rasha suka riƙa safarar makamai ta cikin Syria - Bincike

Bindigar Kalashnikov da akwatunan ajiyar makamai na Rasha, mai dauke da rubutun Rasha
Bayanan hoto, An gano makamai da harsasai kirar kasar Iran, a Lbiya da Syria
    • Marubuci, Sergei Goryashko, Anastasia Lorareva
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Russian
  • Lokacin karatu: Minti 8

Hambarar da gwamnatin shugaban Syria Bashir Al-Asad a baya-bayan nan, da ke cikin kasashe da ke da mahimmanci ga Rasha, a yankin Gabas ta tsakiya.

Hakan kuma ya sake fito da irin yadda dangantaka mai karfi da ke tsakanin Moscow da Teheran, yayin da suke karkatar da safarar makamai a yankin.

BBC ta daga murfin da aka yi amfani da shi wajen yin harkallar makaman yayin mulkin Asad- da irin abubuwan da ka iya biyo baya bayan saukarsa.

Bargo Mai Tarwatsewa

Farfagandar kafar yada labarai ta Rasha RT ta watsa wani bidiyo a ranar 1 ga watan Octoban, 2024. Tsawon minti biyae ba tare da an yi magana ba, kyamarar daukar hoton ta dauko yadda aka ringa safarar makamai a filin jirigin sama na Syria da ke birnin Latakia.

Daya daga cikin kayan na dauke da sunan babban yayan Asad, BAsil, wanda har zuwa lokacin da aka hambarar da gwamantin dan uwansa, kuma tun 2015, ya zama sansanin sojojin Rasha da aka jibge a kasar.

Faifan bidiyon ya fara da nuna filin jirgin saman, kafin daga bisani ya nuna wani jirgin Boeing na daukar kaya, mai dauke da dagin kamfanin hukumar jirgin sama na Iran Qeshm Fars Air, yayin da ya ke sauka a filin jirgin. Haka kuma bidiyon ya nuna yadda aka ringa sauke kaya da cikinsa.

Hotunan yadda ake sauke kaya daga jirgin sama daga Iran, a filin Latakia da ke Syria, kamar yadda tashar RT ta watsa.

Asalin hoton, RT

Bayanan hoto, Yadda ake sauke kaya daga jirgin daukar kayan mallakin Iran, a filin jirgi na Latakia, a wani bidiyo da tashar ta RT ta wallafa

An dai sauke buhunhuna masu yawa daga jirgin, yayin da wasu mutum sanye da kayan sojoji da ke dauke da alamar yansandan sojojin Rasha, yayin da suma suke daukar faifan bidiyon. an dan bude buhunhunan da don kyamarar ta dauko abin d ake ciki, wanda kuma aka ga koren bargo. anan ne bidiyon ya kare.

Wani jami'i a yayin wata ganawa, ya ce Syria na farin ciki da kayan jinkai, da aka kawo ta jirgin ruwa daga Rasha don bayarwa ga "yan gudun hijira, da wadan da suka rasa mastugunensu".

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan kwanaki biyu, kafafen yada labarai na duniya sun rawaito harin da wani Isra'ila ta kai, kusa da dakin ajiyar kaya, da ke kusa da sansanin sojojin Rasha da ke Hmeimim. Bidiyon baya kai harin ya nuna iya wutar da ta tashi a wajen ba kadai, har da sauran fashewar wasu abubuwa, Inda wasu ke hasashen cewar tashar ta RT ta watsa na da alka da harin da Isra'ilan ta kai.

"Kowa ya san cewar bargunan ka iya tashi, su ma"a wani kalami mai kamar gatse wata majiyar BBC ta fada, kuma ta ke da msanaiyar abin da ya faru a Hmeimim. da muka tambaye shi ko Iran ce ta shigo da makaman ya jirgin ruwa ta hanyar amfani da hanyoyin Sojojin Rasha, da ke kula da bangaren rarra kayan jinkai, sai majiyar ta mu ta ce: "To da me kake son in ce? Wai wadan nan "Bargunan' da suka yi muguwar fashewa, da har suka kusa kawar da Hmeimim baki dayanta."

Hmeimim ba ita ce hanyar safara da Iran ke amfani da ita ba don kai kayan Lebanon, a cewar Nikita Smagin wani kwarare a yankin.

Ya ce "Iran na da kafafin shigar da kaya wadda Isra'ila ke kaiwa hari akai-akai. Amma mafi kasarin wadan suke wucewa ta su suna isa Syriya da Lebanin- ba wai ta sansanonin Rasha ba". Daga baya ya bayyana su da basu da wani mahimmanci, ga kai kaya ta jirgi ruwa, bayan da aka sami sauyin gwamanti a Syria, wanda kuma ka iya karuwa.

"Iran ta rasa kusan komai a Syriya, saboda kasar ta bar karkashin ikonta, yana iya yiwuwa har yanzu zaa iya kai irin wadan nan kaya ta Hmeimim," a cewar Smagin. "Amma saiidan Rasha ta amince da hakan, zai yi mutukar rage damar cimma wata yarjejeniya da sabbin hukumomin gwamantin Syriya.

Taswira

Yadda Rasha ke amfani da Rasha ke amfani da 'fararen hula waje yin shinge'

Sarit Zehavi wata leftanal kanal ce mai ritaya, a hukumar tsaro ta Isra'ila, da ta kware wajen tattara bayan sirri a banagren soji.

Itace shugabar Cibiyar bincike da bayar da horon harkokin ilimi a Isra'ila, "da farkon mun gano yadda wasu jiragen Iran, da aka san su, da safarar makamai a yankin, sannan su sauke su a karshen filin saukar jirgi na Hmeimin, a farkon 2023", a cewar ta.

"Isra'ila ta kai hari kan filin jirige a Syriya, da ke Damascus da Alleppo, kuma Iran ba sa iya sauka a nan. Dole suka nemi mafita," a cewar Zehavi.

Ta ce cibiyar bincken ta, ta taba yin wani gargadi na cewar, jirgin farko mallakin Iran da zai sauka a Hmeimin, ka iya zama sansanin sauke makamai - yayin da Rasha ke amfani da mutane a matsayin garkuwa, a lokutan da Isra'ila suka kai hari.

Jirgi mara matuku na 'Shahed'

Asalin hoton, Morteza Nikoubazl_NurPhoto via Getty Images

Bayanan hoto, Rasha na baiwa Iran makamai ciki har da jirgin mara matuki mai lakabin 'Shahed', kuma Washington ta ce an kuma ga wasu makamai na roka.

Kornets in the playroom

A cikin watan Nuwamba, dakarun IDF sun wallafa wani bidiyo, da aka nade shi a kudancin Lebanon. a cikinsa, a wani daki, ana iya ganin buhunhuna, da akwatuna, da kayan wasa - kamar mai su ya bar wajen cikin hanzari. Akwain wani soja a tsaye a ciki bidiyon. Da kyamarar ta juya, a chan kusurwar dakin. akwai wani bangare da ya fashe.

"Mun shiga dakin yara, wanda ke da wani bango da fasa, "wani da ke cikin wadan suka kai sumame dakin, ya ke shidawa BBC. "Mun rushe bangon, anan ne muka gano abubuwa masu yawa.

Akwai makai masu yawa a dakin da ke ciki da kayan wasan yara.

Asalin hoton, IDF

Bayanan hoto, Bidiyon dakarun IDF ya nuna dakin da ake ajiye makamai, a wani gida da ke Lebanon tare da kayan wasan yara.

Karamin akwati ne da aka kera shi don makaman Rasha, kuma dakarun IDF ba wai iya bindigar Kalashnikov suka gano ba, har da manyan makaman yaki, na kariya harin tankar yaki. Sun kuma gano makamancin hakan a wasu gidajen da ke yankin.

Оружие и боеприпасы, найденные ЦАХАЛ в одном из домов на юге Ливана
Bayanan hoto, Makamai da harsasai da dakarun IDF suka gano a wani gida da ke kudancin Lebanon

"Irin wannan makamai, ana amfani da su ne, wajen kai hare-hare a birin, ba wai na gwabzawa da dakarun IDF ba" a cewar sojan. "A kiyasi, kowane gida na iya mallakar makamin da zai wadatar da mutum biya ko shida su yi fada.

"Sojojin da ke janyewa sun dauki na'urar harba babbn makamin sai dai sun bar akwatin da aka shigo da ita. Ana iya ganin hakan a wasu hotuna da BBC ta gani.

Ana iya ganin wani bangare na na'urar harin ta Kornet, da aka nunasu a hotuna. Sun yi amfani da mamakamai na musamman da ke iya huda sulke sannan yana tashi a karo na biyu, a cikin abin hawa. Dayan kuma, akwai manyan makamai masu fashewa ciki har da makaman kare dangi.

Akwatin makamin na 'Kornet'
Bayanan hoto, An ajiye sulken tanka na Kornet a daya daga cikin tashohin da aka yin kwalaye.

Ya yi hasashen cewar makamin kare dangin da aka bari, an barsu ne saboda ana shan wahala wajen fitar da su cikin sirri. An shigo da shi daga kudancin Lebanon daga Syriya ta titi. Titunan da ake jefa ayar tambaya akai, na cikin idan Isra'ila ta yi fakon kai hari a lokacin Bazara, ta hanyar kai hare hare ta sama.

An harba makamin mai linzami na 'Kornet'

Asalin hoton, Laurent Van der Stockt for Le Monde/Getty Images

Bayanan hoto, Zangon makamkin na Kornet na iya kaiwa Isra'ila ta iyakar dake kudancin Lebanon

Hanyoyin da ake shigar da makamin Kornets

Sojan da muka yi magana da shi ya ce makaman sun iso Lebanon daga Syriya.

Sojojin IDF sun sun gano kudaden Syriya a gidajen, wanda hakan ke tabbatar da zargin kalaman nasa.

Amma sai dai stamfin da aka samu a jikin makaman, daga hukumar fitar da kaya ta Rasha, na nuni da cewar an siyarwa wani jami'ain wata kungiya, a cewar wata majiya da BBC ta yi magana da ita.

"Kungiyar farko da ta fara zuwa rai na, a wannan hali da ake ciki itace ta Gwamantin Syriya, sojojin Assad. Kamar yadda muka sani, tana da kwance mai karfi da Syriya da Hezbolla, wanda kuma ta ke kawance da Hezbollah ta Lebanon," a cewar sa.

Wani akwatin katako dauke da lambobin da ke nuni da na rasha ne
Bayanan hoto, Wani akwatin ajiye makamai da ke dauke da alamun Rasha da dakarun Isra'ila na IDF suka gano

Wata majiya ta tattara bayan sirri na kasashen Yamma, da ya yi magana da BBC, ya tabbatar da cewar mafi akasarin makaman Rasha da dakarun IDF suka gano a Lebanon sun futo ne daga sojojin gwamantin Syriya.

A wani rahoto da jaridar Walla Street journal ta wallafa, ta ambato wata majiya da bata bayyana ba, na cewar wasu daga cikin makamai masu linzamina Kornet an gano su ne a kudancin Lebanon, an kuma kera su tun a 2020, kuma an yi ta shigo da su daga Rasha da yawansu zuwa Syriya.

Gabinin a gano su, tunanin shugabancin sojin Isra'ila ya karkata kan cewar Hezbollah iya wani tsohon makamin Soviet ta ke da su.

Akwatunan makamai masu linzami da aka bude
Bayanan hoto, Dakarun Isra'ila sun gano sabbin makami mai linzami na Korent da suka gano a lokacin da suka kai sumame a kudancin Lebanon.

Smagin ya ce gwamantin Assad ta na bayar da makaman Rasha ga dakarun Hezbollah; wanda daga nan sai a kai su Rasha. Amma Rasha ta shafawa idon ta toka.

"Ba su iya gani cewar an sami futar bayanai ba da ke cewar akwai kaya da aka shigo da su, Amma sai dai ko dai babu wani mataki da suka dauka, ko kuma sun sani suka yi burus, a cewar Smagin.

Har zauwa 2022, ta fi darajanta alakarta da Isra'ila, wanda hakan yasa taki bayyana barin a baiwa Hezbollah makamai, a cewar bayanin Smagin.

"Halin da ake ciki ya sauya, kuma ba a baiwa ra'ayin Isra'ila wani goyan baya ba. Duk da haka dai babu wani tabbaci daga Rasha na ko kai tsaye ta ringa baiwa Hezbolla makamai" a cewar Smagin.

Kwanson sabon gurneti da aka lulube shi a cikin wata leda
Bayanan hoto, Sabon makamin roka, daga Rasha da shi ma aka gano a kamdanin samar da kwalayen

Hezbollah babbar kawace ga dakarun Syriya, tana kuma yin aiki da dakarun Rasha da da ke Syriya. Sai dai an kashe musu sojoji masu yawa, a hare-haren da Isra'ila ta kai, wanda kuma haka ya raunatsu. a hannu guda hakan ya zama wani dalili da ya kai ga hambarar da gwamantin Asad shi kansa.

Bayan nan, dakarun sojin saman Isra'ila, sun yi aiki tukuru wajen kai hari kan tashohin makamai da ke Syriya. kusan kashi 80 cikin dari, na makaman Syriya an ce sun zama shara. Kadan din da suka rage sabuwar gwamantin kasar ka iya mayarwa da Hezbollah su, idan suka ga dama.

Haka kuma, An mayar da ikon mulki zuwa ga sojoji a Syriya da ke adawa da Iran. Ko me zai zama makomar sansanonin Rasha da na Theran, da sauran hanyoyin raraba makamai a Syriya wanda hakan babban abu ne.