Ƴan Najeriya takwas da aka kama a ƙasashen waje bisa zargin aikata manyan laifuka

Asalin hoton, AFP/Getty/ Others
A wannan makon ne hukumomin ƙasar Finland suka kama jagoran ƙungiyar ƴan awaren Biafra ta IPOB, Simon Ekpa, inda suka samu izinin ci gaba da tsare shi har lokacin da za a yi masa shari'a.
Hukumomin sun kama shi ne bisa zargin tunzura mutane su aikata ayyukan ta'addanci.
Hukumomin Najeriya sun ji dadin hakan tare da nuna sha'awar ganin an miƙa masu shi domin ya fuskanci shari'a a Najeriyar.
Ba wannan ne karo na farko ba da aka taɓa kama wani ɗan Najeriya a ƙetare bisa zargin hannu ko alaƙa a aikata manyan laifuka ba.
Ga wasu mashahuran ƴan Najeriya takwas da aka taɓa kamawa a wata ƙasa, waɗanda kamen nasu ya sanya sunan Najeriya a kanun labarai:
Simon Ekpa

Asalin hoton, Simon Ekpa/Twitter
Hukumomin ƙasar Finland sun kama shi ne a wannan mako, duk da dai ba su faɗi takamaiman ranar ba.
An kama shi ne tare da wasu ƴan Najeriya huɗu, waɗanda dukkanin su ake zargi da laifin tunzura al'umma.
Simon Ekpa ya daɗe yana iƙirarin cewa shi shugaban wani ɓangare ne na ƙungiyar IPOB, mai neman ɓallewar yankin Biyafara daga Najeriya.
Ya riƙa watsa shirye-shirye da manufofinsa ta shafukan sada zumunta, wani abu da ya sanya hukumomin Najeriya ke neman shi ruwa-a-jallo.
A cikin watan Yunin 2024, lokacin ganawa da manema labaru, babban hafsan sojin Najeriya, Janar Chriostopher Musa ya ce "mun faɗa ƙarara cewa dole ne a kama shi kuma dole a gurfanar da shi."
A lokacin, Janar Musa ya zargi hukumomin Finland da bai wa Simon Ekpa kariya.
Nnamdi Kanu

Asalin hoton, Getty Images
A watan Yunin 2021 ne hukumomin Najeriya suka bayyana cewa an kama shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu a wata ƙasar waje.
Yayin bayyana labarin kamen, ministan shari'ar ƙasar na wancan lokacin, Abubakar Malami bai bayyana haƙiƙanin ƙasar da aka kama mista Kanu ba.
Sai dai daga baya, bayanai sun nuna cewa jami'an tsaron sun kama shi ne a ƙasar Kenya, inda ba tare da ɓata dogon lokaci ba aka mayar da shi Najeriya.
Tun daga wancan lokaci ne kuma aka sake gurfanar da shi a gaban kotu bisa tuhume-tuhume da dama.
Tun da farko Mista Kanu ya arce daga Najeriya ne bayan shari'ar da ake yi masa kan tuhume-tuhume 11 ciki har da haɗa ƙungiyoyin tayar da zaune-tsaye da mallakar makamai ba bisa ƙa'ida ba da kuma shigar da haramtattun kaya Najeriya.
Tukur Mamu

Asalin hoton, Tukur Mamu
A cikin watan Satumban 2022 ne hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, DSS, ta tabbatar da kama Tukur Mamu, wanda ya shiga tsakani don kuɓutar da fasinjojin jirgin ƙasa da ‘yan bindiga suka sace a dajin da ke tsakanin biranen Abuja da Kaduna.
Cikin sanarwar kama shin da kakakin DSS, Peter Afunanya ya fitar, ya ce ‘ya sandan ƙasa da ƙasa ne suka kama shi a filin jirgin saman birnin Alƙahira da ke ƙasar Masar a ranar 6 ga watan Satumban 2022, lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa Saudiyya.
An mayar da Tukur Mamu Najeriya, inda hukumar DSS ta ci gaba da bincike a kansa.
Hukumomin Najeriya dai sun buƙaci a kama Mamu domin amsa wasu tambayoyi masu alaƙa da batutuwan tsaro da ƙasar ke fama da su.
Umar Farouk Abdulmutallab

Asalin hoton, AFP
A watan Fabrairun 2012 ne wata kotu a Amurka ta yanke wa dan Najeriyar hukuncin ɗaurin rai-da-rai, bayan da aka same shi da ƙoƙarin tayar da bam a wani jirgin saman Amurka.
Umar Farouk Abdulmutallab, ya amsa laifin yunƙurin tarwatsa wani jirgin saman kasuwanci na Amurka, a wani lamari da ake ganin yunƙurin ƙunar baƙin wake ne.
Akalla mutum 300 ne a cikin jirgin wanda ya tashi daga Amsterdam na ƙasar Holland zuwa birnin Detroit na Amurka a ranar bikin Kirsimetin 2009.
Sunday Igboho

Asalin hoton, SUNDAY IGBOHO
A watan Yulin 2021 ne hukumomin Jamhuriyar Benin da ke yammacin Afirka suka kama fitaccen mai fafutikar kare muradun Yarabawa, Sunday Igboho a filin jirgin saman ƙasar.
Kamen nasa ya zo ne bayan jami’an hukumar DSS na Najeriya sun kai samame gidansa da ke birnin Ibadan bisa zargin shi da yaɗa aƙidar ƴan aware.
To sai dai Igboho ya ci gaba da zama a hannun hukumomin Benin har bayan shekara biyu, kafin daga bisani a sake shi.
Lawal Babafemi

Asalin hoton, Lawal Babafemi
A watan Agustan 2015 ne wata kotu a birnin New York na Amurka ta yanke wa Lawal Olaniyi Babafemi, wanda a lokacin yake da shekara 35 a duniya, hukuncin ɗaurin shekara 22 bayan samun sa da laifin haɗa baki don goyon bayan ƙungiyar al-Qaeda a yankin ƙasashen Larabawa.
Babafemi ya amsa laifin da aka tuhume shi da aikatawa tsakanin 2010 zuwa 2011, inda ya amsa cewa ya yi bulaguro daga Najeriya zuwa kasar Yemen domin ganawa da kuma samun horo daga shugabannin al-Qaeda reshen ƙasar Yemen, sannan kuma yana da hannu a shirya wasu hare-hare kan Amurka na tsawon shekara 10.
Shugabannin al-Qaeda sun horas da Babafemi kan amfani da bindiga ciki har da ƙirar AK-47 tare da koya masa dabarun amfani da harshen Ingilishi wajen yaɗa manufofin ƙungiyar a ƙasashen ƙetare.
Ramon Abbas - Hushpuppi

Asalin hoton, Hushpupi Instagram
An kama Hushpuppi ne kan zarge-zargen aikata zamba ta intanet.
A watan Yunin 2020 ne aka kama Ramon Abbas da aka fi sani da Hushpuppi a ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, bisa zargin zambar kuɗaɗe.
Daga baya aka miƙa shi ga Amurka inda aka tuhume shi da hannu a wani shirin zambar miliyoyin dolili.
Ƴan sandan sun kuma cafke wasu mutum 11 a samamen da suka kira Fox Hunt 2 a samame 6 da suka kai a kasar.
Kusan mutane miliyan biyu akai amanna sun fada komar dan damfarar ƙungiyar su Hushpuppi.
A ƙarshe an yanke wa Abbas hukuncin ɗauri na sama da shekara 11 a Amurka bayan kama shi da laifi.
Haka nan an buƙace shi da ya biya kuɗi dala 1,732,841 ga wasu mutum biyu da ya zambata.
Ike Ekweremadu da matarsa

Asalin hoton, MET POLICE
An kama babban ɗan siyasarna Najeriya ne a Birtaniya kan laifin safarar gaɓoɓin ɗan'adam.
Kama shi ya haifar da muhawara a ciki da wajen Najeriya, wani abu da ya kai ga cewa an samu sanya bakin manyan ƴan siyasa, musamman sanatoci.
An kwashe tsawon lokaci ana tafka shari'a, yayin da hukumomin ke tsare da Ekweremadu a birnin Landan.
A watan Mayun 2023 ne wata kotu a Birtaniya ta yanke wa hamshaƙin tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan na Najeriya, Ike Ekweremadu, da mai ɗakinsa, hukuncin ɗaurin shekara tara a gidan yari bayan samun sa da laifin yunƙurin safarar sassan jikin ɗan'adam.
An kama shi ne a watan Yunin 2022 tare da mai ɗakin nasa a filin jirgin saman Heathrow da ke Landan, bisa zargin safarar sassan jikin bil-adama.
Kotun ta samu tsohon Mista Ekweremadu da mai ɗakin tasa da laifin haɗa baki wajen shirya safarar wani matashi domin a cire ƙodarsa a saka wa 'yarsu maras lafiya.











