An yanke wa 'yan Najeriya hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan alaƙa da Boko Haram a Dubai

Boko Haram

Asalin hoton, Getty Images

Rahotanni na cewa wata kotu a birnin Abu Dhabi na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta yanke wa wasu 'yan Najeriya shida hukunci kan alaƙarsu da ƙungiyar Boko Haram.

An zarge su ne da ɗaukar nauyin ƙungiyar ta Boko Haram ta hanyar ba su kuɗaɗe.

Kotun daukaka karar da ke zama a Abu Dhabi ta kama mutum shidan ne da laifin taimaka wa kungiyar Boko Haram da kudi, ta hanyar tattara mata kudi daga kasashen waje, tana hada baki da wasu masu sana'ar canjin kudi a Najeriya.

Kotun ta raba mutunen ne gida biyu, kashi na farko na mutum biyu da ta yi musu hukunci ma fi tsanani, bayan ta dogara da binciken da ta yi, wanda ya kawar mata da dukkan shakku cewa ƴan Boko Haram ne.

Yayin da kashi na biyu kuma mai mutum hudu, ta yi musu hukunci mai sassauci - na ɗaurin shekara 10, saboda fahintar ba su shiga ƙungiyar har wuya ba.

Tun a shekarar da ta wuce ne aka yi wannan shara`ar, amma labarin ne bai fito ba sai a dan tsakanin. Kuma shara`ar ma an ta dan ja lokaci gabannin yanke hukunci.

BBC ta yi ƙoƙarin tuntuɓar Ministan Shari'ar Najeriya, Abubakar Malami, don jin matsayin gwamnatin ƙasar a kan wannan hukuncin, amma ba a same shi ba.

Ko da yake wasu kafofin yaɗa labarai sun ambato shi yana cewa sun samu labari, har ma sun nemi mahukunta a Hadaddiyar Daular Larabawa da su ba su cikakken bayani a kan hukuncin, amma shiru kake ji.

Takardun shari'ar da jaridar Daily Trust ta samu sun nuna cewa an yanke musu hukuncin ne a shekarar 2019.

Waɗanda aka ɗaure ɗin na da hannu wurin tura wa Boko Haram kuɗi kusan dala 782,000 tsakanin shekarar 2015 zuwa 2016, a cewar takardun shari'ar.

Wani jami'in gwamnatin Najeriya ya faɗa wa jaridar cewa suna sane da shari'ar.

Sai dai iyalai da kuma abokan mutanen sun ce "sharri aka yi musu" saboda sun daɗe suna yin harkar canjin kuɗin ƙasashen waje.

Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 36,000, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).

Wani bincike da hukumomi suka yi ya ce mutum fiye da miliyan ɗaya ne ke gudun hijira a cikin Jihar Borno kaɗai saboda rikicin, yayin da aka rusa kashi 30 cikin 100 na yawan gidajen da ke jihar.